NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 38 of 136

i matsa Mata na lallai sai yaji ra'ayinta a sannan ba shima bai jima ba ya tafi, bayan ta shigo ne Mai gadi yayi knocking a kofar falon shema'u ta bude manyan ledoji ne ya Mika Mata guda biyu yace a bawa Zahara'u inji bakonta. Tun daga lokacin Koda yaushe Muneeb yana hanyar gurin Zahra,r tun tana dari dari dashi har ta sake, shi mutum ne Mai saurin shiga Rai Yana da wasu Qualities da zasusa asoshi. Kafin su rufe wata biyu sunyi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a family din Mubeen yasan da zaman Zahra haka itama nata sun San Muneeb Dan har Azare yaje ya gaishe su da ashirin bama sha tarabta Arziki ba,har Saida Abban su yayi Masa fada sosai akan kada ya Kara musu haka in dai Yana son su Shirya. Sun daf da Gama diploma dinsu Iyayen Muneeb sukayi maganar aure, ba Bata lokaci aka saka Rana ba'a wani ja lokaci ba Mai tsawo ba, abu kama-kama shima Kamar na baya abun ya shashence ba wani cikakken dalili haka Nan Rana tsaka Muneeb yace ya fasa akayi juyin duniyar Nan yace shifa aure ba dai da Zahra ba komai za'ayi, dole aka hakura Dan shi cewa yayi har kayan ya bar Mata saidai abinda iyayenta Basu amince ba kenan. Fadin halin da zahra da su Ammah suka shiga bazai misaltu ba, Dan hankalinsu yanzu yafi tashi fiye da wancan lokacin. Ammah taso kwarai zahrar ta koma Azare Amman Maman Ya Aliyu ta roki Alfarmar zata Kai zahra gurin masu Islamic chemist a gani ko namijin Aljani ne ya aureta. Ammah ba tayi musu ba sai godiya tayi sosai, sunje harda Aunty Hasana anyiwa Zahra tambayoyi ba alamar Aljani a jikinta sai dai sun fada musu da alamar sihiri a tare da ita Amma ba sosai ba, Nan suka bada magunguna Hajiyar ta biya suka dawo gida. Jannifer ma tayi bakin cikin abinda ya faru taso Zahra ta Bata dama taje garinsu ayi mata wani Abu akan idan ma wani ne yake lalata lamarin auren zega abinda ze same shi. Nunawa tayi Bata so ita haka Allah ya tsara Mata wannan qaddarorin Kuma ba makawa sai sun sameta. A haka har suka Gama diploma dinsu kafin Aunty Hasana ta mayar da Zahra Azare. Haha rayuwa taci gaba da gudana, duk wani buri akan aure Zahra ta cire shi Bata kula kowa duk iya nacin mutum Bai isheta kallo ba, wani lokacin har fada suke da Hameeda akan rashin kula samari sai dai sau da yawa tana Mata uzuri akan irin yanda fasuwar aure take walagigi da ita. Zama ya Mika lokacin har anyi wurin wata Tara da fasa aurenta da Muneeb. Wani yammaci suna zaune a bayan part din Ammah ita da Hameeda da Mujiba data shigo musu yawan yamma suna hira Kiran ya Abdul Hakeem ya shigo wayar Hameeda Yana tambayar suna ina ne ya shigo Bai gansu ba. Inda suke ta fada Masa suna niyyar tashi ya zagayo bayan, a tare suka gaishe dashi ya amsa Yana gaisuwar tasu yana fadin "Congratulations" "For what Yaya?" cewar Zahra. Irin Brown din envelope din Nan babba ya Mika Mata Admissions letters ne guda biyu a ciki na Salma da Hameeda duk sun Sami gurbin karata a federal University Dutse jigawa state (F.U.D). Cikin murna ta rungume Hameeda tana fadin "congratulations sister". Kafin ta sake ta tana Mika Mata takardun, ai tana arba da wannan abin Arziki ta Diba a guje tana fadin"thank you Yaya Allah ya saka maka da Alkhairi". Bayan ta wuce ne zahra ma ta Kara Masa godiya sosai. Kujerar da Hameeda ta tashi ya janyo ya zauna alamun dake nuna magana Mai mahimmanci zeyi da ita. Ganin haka yasa Mujiba tashi tana fadin "Yaya sai anjima". "Dawo ki zauna ba Zama zanyi ba.magana zan fada Mata kawai" A takure ta koma ta zauna. Kan Zahra ya maida kallonsa "kina jina?" Kai ta gyada Masa alamar eh. "Good" ya fada. "Ina ga Nan da one month ko three weeks kema Zaki wuce Zuwa Turkey daga can Kuma idan komai ya daidaita Zaki wuce syprus inda Zaki hada a degree dinki, idan kin tuna Kamar two months da suka wuce ai na karbi komai naki to Mama Hanifa ce ta bukata a tura Mata a she makarantar zata nemar Miki taso a Samu a Nan turkey din to ba'a samu ba, ita kuma Bata son a Kara Bata lokaci, shine ta yiwa danta magana tunda a can yake aiki da ofishin jakadancin turkiyya na kasar Kuma ma Nan ne kawai Mama Hanifar ke ganin yafi kusa da istanbul din". Ba Zahra kawai ba hatta Mujiba tayi murna kwarai da gaske gatan da za'a yiwa Zahra kenan a irin wannan lokacin na a rabata da kasar gaba daya Kota Samu peace of mind. Godiya ta ringa yiwa ya Abdul Hakeem din harda 'yan hawayenta na Dadi. Gashi Ammah Bata Nan taje Jimeta gurin biki, taso tana Nan ta kwanta a jikinta suyi sharing din farin cikin. Har ya Abdul Hakeem din ya kai kwanar da ze fita ya juyo Yana fadin "don't talk to anyone, keep silent pls, nasan Mujiba Bata da problem shi yasa na fada a gabanta". Yasa Kai ya wuce. Kallon junan su sukayi suna son banbance maganar Ya Abdul Hakeem. 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ MAMAN FATIMAH PAGE TWELVE (12) __________A cikin qanqanin lokaci aka Gama yiwa su Hameeda shirye - shiryen tafiya makaranta Dan sau biyu suna Zuwa jigawar akan registration din. Sai wannan ciccira kai salma keyi tana sakin maganganu
🏠