hrar taje Amma Alhaji Jafar yayi uwa yayi makarb'iya akan suzuzo idan hankali ya kwanta, da haka suka bar zancen.
A Dan tsakanain ne Aunty Hasana tazo, sun Sha jajantawa sosai da Ammah itama sai da ta tsare zahra da tambayoyi kala kala, daga karshe ta Kare da nasiha Mai tsoratarwa sosai.
Lokacin da zata koma Jos ta nemi zata tafi da Zahra Abban bai Hana ba Yana ganin idan tayi nisa da garin zatafi Samun kwanciyar hankali.
Zamanta a Jos Mai Dadi ne Dan daga baya ma fafutukar nemar Mata admission mijin Aunty Hasanar ya Fara ba'a samu wadda ake so ba, sai diploma ya nemar Mata a wata private school ta Fara computer science.
Hankalinta ya kwanta sosai ta cire soyayya daga zuciyar ta Sam taqi ba kowa fuska akan soyayya duk da yanda ake kawo Mata Rida.
Ranar wata litinin sun Gama lectures dinsu na safe suna zaune da wata course mate dinta 'yar kabilar Tiv suna wani Assignment jininsu ya hadu da jannifer sosai Dan har gidan Aunty Hasana tana zuwa idan zasuyi wani aikin.
Bayan sun Gama ne suka nufe caf'e na cikin makarantar a cire musu hard copy din aikin suka tarar da cinkoson mutane dole tasa suka fito waje ayi musu.
Har sun Gama sun fito suna niyyar tsallaka titi ne wata mota Mai azabar kyau ta tsaya dai dai inda suke tsaye. A hankali na ciki ya sauke tinted glass din motar, wani guy ne da gani hutu ya ratsa shi sosai, murmushi yayi musu idonsa na kan zahra
Yana fadin "sannunki"
Jannifer ce to amsa masa Dan tana Jin hausa Kamar jakar kano.
"Yauwa sannunka" ta fada.
Kofar ya bude ya fito Yana sanye da kananun Kaya,fari tas dashi kamar irin ruwa biyu din Nan half cast Dan sumarsa a nannade take kamar irin ta buzaye din Nan.
Cikin kwarewa da yadda da Kai kalli jannifer Yana fadar "Naga kawarki ne inso da fatan zakiyi min campaign".
Dariya tayi tana kallon Zahra wadda tayi kicin kicin da fuska Kamar zatace wayyo Allah.
"Gaskiya na tafi tunda Baki da aikin Yi ke saiki zauna".
Zahra ta fada tana nufar titi ganin an Sami space din tsallawa.
Jannifer da Dan jima dashi kafin ta shigo cikin makarantar, Koda ta shigo Bata yi Mata maganar komai ba har suka Gama lacture dinsu suka tashi. Direban su Aunty Hasana ya dauke su ya ajiye jannifer a hanya kasancewar su zahra sun gaba dasu Amma hanyarsu daya sau da Daman sukan tafi tare ranar da jannifer Bata zuwa shagonsu.
Ranar Saturday misalin hudu da rabi haka su zahra da yaran Aunty suna compound din gidan tana Dora Yara kan lilo marry go round suna Wasa kusan duk weekend a Nan suke hutawa da yamma tunda islamiyyar safe suke zuwa a weekend.
Mai gadi ne ya nufo gurin da suke Yana fadin Zahara'u ki fadawa yallabai Yana da bako a waje".
Auntyn ta fadawa Abban su Faruq Yana da bako inji Mai gadi.
Lokacin daya fito yayi mamakin da baiga bakon ba ya nufi gate Yana tambayar Mai gadi, shine yace "ni ne na hana ya shigo tunda yace bakasan da zuwansa ba bilhasal ma yace baka sanshi ba"
Kofar Mai gadin ya bude masa ya nufi gurin da motar take yayin da shi kuma na cikin ya fito. Da gaske baisan yaron ba, hannu ya bashi sukayi musahiha sai Kuma sukayi shiru Ya Aliyun ne mijin Aunty Hasanar yace Masa "ko kaine maisallama Dani?".
"Eh nine"sai Kuma ya danyi shiru.
Ya Aliyun ne yace "my friend pls talk feel free with me".
Nan yayi Masa bayanin yaga Zahra ne Yana sonta shine ya biyota gida, ya fada masa sunansa MUNEEB mahaifansa Kuma Alhaji Salman Mai fata. Kallonsa ya Aliyu ya karayi yayi mamakin yanda d'a Kamar na Alhaji Salman Mai fata yake da irin wannan tarbiyya ganin yanda mahaifansa yake da mahaukanta kudi Kuma yasan 'ya'yansa sosai Amma da yawansu gata yasa sun lalace basa ganin kan mutane da gashi.
Ya Aliyun yaji dadi sosai ya Kuma bashi damar zuwa gurin Zahrar sannan ya Dan fada Masa wacece Zahrar a gurinsa.
Lokacin da ya Aliyun ya koma bayani ya yiwa Aunty Hasana na abinda ya faru itama ta bada goyon baya tasan ko yanzu Zahra tayi gaba Allah ya Bata Wanda yafi Sahal Dan ba karya ba hadi a tafiyar.
Da dare Aunty ta Samu zahra da maganar da farko tuburewa tayi akan ita Bata so saida Aunty ta fito Mata ta bayan gida sannan ta fashimci abinda Auntyn take son ta Gane.
Washe gari Aunty har da ita aka hadawa MUNEEB abin tarba, Zahra ta Dade tana mamakin yanda akayi yasan gidan su Amma data Zama very curious sai ta gano duk yanda akayi jannifer ce ta bashi address dinta. Yau ma da yamma yazo, falon Ya Aliyu aka bude Masa yayin da Mai aikin Aunty shema'u ta Kai Masa abin tarba.
Wata straight gown ta saka ta atamfa glitter Mai ruwan peach colour sai madaidaici gyale kalar lemon green irin touching din jikin atamfar sai takalmi shima lemon green din plat Mai kyau. Bata daura dankwalin kayan ba. Ta fesa turenta Amber oud gold, tun kafin ta karaso kamshin ta ya fada Masa zuwanta, kofar ya zubawa idanu ai lokacin data shigo da sallama Saida ya Dan samu shock na wucin gadi Ashe ranar ba inishin Zahrar ya gani ba yanzu ne yaga zahirinta, a kasa ta zauna kan carpet tana gaishe shi kanta Yana kallon kasa. Nan ya gabatar Mata da kansa da abinda ya kawo na son aurenta, ba