NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 36 of 136

kon da tayi maganar ba tace "A"a Hajiya ba Zama mukazo ba munzo ne mu karbi kayan lefen da muka kawo na Sahal yace baya yi akai kasuwa". Lafazin da Ya yiwa Ammah sallama kenan lokacin data fito Zahra na biye da ita. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Abinda Ammah ta fada kenan a zuciyar ta Nan da Nan wani jibi ya taso Mata. Salatin Mama da Asabe ne ya fito da Alhajin daga part dinsa yayin da su Zilai sukayi cirko-cirko duk wuta ta dauke musu Dan maganar tasu ba karamin razani tasa a zukatansu ba. A hankali ya karaso kusa da Ammah Yana tambayar meke faruwa ne kafin tayi magana Mama tayi tsagal tana fadin "wane irin cin mutunci ne Alhaji ba laifi tsaye bana zaune zasuzo suce a Basu lefensu Wai auren amfasa". Ta karasa fada tana fashewa da kuka tana maganganu, ita kuwa Ammah ba abinda take sai ambaton Allah yayin da Zahra ta nemi gefen inda aka shuka filawoyi ya zauna Dan ji tayi Nan da Nan jiri Yana nema kayar da ita, itama bakinta ba abinda yake sai ambaton Allah. Kallo Daya Alhaji Jafar yayiwa Baki ya kawar da kansa Dan da alama da rashin mutunci suka shigo gidan. Gyaran murya yayi kafin yace "Masha Allah munji sakonku Amma Dan Allah ku koma kuce musu zuwa anjima inshallah Allahu za'a dawo da duk wani Abu daya kasance nasu ne har sadakin da suka kawo Allah yasa hakan yafi Alkhairi". Yana Gama fadar haka ya juya dakinsa ya barsu a Nan a teaye, Dan dukkansu ba karamin kwarjini yayi musu ba. Ammah part dinta ta nufa duk kwakwar mutum baze taba Gane Yanayin da take ciki ba.Dan Allah yayi Mata wata irin zuciya Mai iya danne bacin Rai da wuya ka Gane fushinta tana da hadiye fushi sosai, dakin suka bita suna Bata magana Mama sai sharbe take tana Dan Allah wannan wane irin cin zarafi ne da tazarce ace saida komai ya kankama sannan za'a bullo da wannan cin zatafin dan a wulakanta yarinya har a ringa yi Mata wani gani -gani aga Kamar wani Abu tayi yasa aka fasa". Sai lokacin Ammah tayi magana tana fadin "ba komai Mama Daman can haka Allah ya nufa ba mijinta bane Kuma maganar mutane su ringa ganin Kamar wani Abu marar kyau ne yasa aka fasa na barsu da Allah yayi Mani maganin komai, ba komai haka Allah ya nufa rubutaccen Al'amarine baya goguwa". Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta sun jima a falon suna tattaunawa kafin su koma dakin mamar su Zilai kuma suka nufi in da Zahra tace zaune suka dinga Bata magana duk da Bata want rude ba a nitsenta take. Duk wannan kwamacalar da akayi su Hameeda da Salma basa Nan sunje Aiken Mama. Tunda Alhaji Jafar ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye Bai taba zaton karamar magana daga gida irin Honorable ba Amma ya hanasu kayan ne Dan ya tabbatar da daga Ina maganar take shin da sanin uban yaron da waliyayansa ko Babu Dan yanda sukayi komai cikin girma da mutunci ya kamata ko baza'ayi auren ba to a rabu cikin mutunta juna. Su malam Bukar da Yayan Alhajin Wanda suke 'yan maza Alhajin ya Samu da maganar basuyi kasa a Gwiwa ba zuka nufi gurin waliyyan Sahal sai dai maganar haka take Dan sun tsame ma hannunsu daga lamarin tunda iyayensa Basu da lissafi, Wai yaron ne yace musu shi baze iya auren Zahrar ba yanzu ba wadda ya tsana kamarta duk duniya". Lokacin da suka dawowa da Alhajin wannan labarin ransa yayi matukar baci, a ranar aka maida duk wani Abu da yake mallakinsu ne. Sai dare Abban ya Samu kebewa da Ammah in da ya ringa tausarta da kalamai masu Dadi har ta Samu ta Samu nutsuwa Amma fa kasa kwana tayi a dakin nasa. Lokacin data dawo daki Zahra Bata tafi nasu bangaren ba tana dakin Amma a kan gadon tayi rigingine idanuta a rife hawaye na zurarowa daga gefen idon wani Abu yake Mata yukuki a zuciyar ta. Har Ammah ta bude kofa zahra Bata sani ba saida ta zauna a kiss da ita taji shashhshekar kukanta kasa -kasa. "Tashi zaune magana zamuyi". Daga sama taji maganar Sam bata San Ammar ta shigo ba. Ba musu ta tashi zaunen tana koge fuskarta da tayi wajir. "Meye dalilin da Sahal ya fasa Aurenki ko ya sanki 'ya mace ne". Cikin tashin hankali marar misaltuwa Zahra ta dago ta kalli Ammah kafin ta fasa kukan da take dannewa tana na zuci. Kai ta shiga girgizawa tana wani irin numfashi nKamar wadda zata shide. Kafin Allah ya batan ikon bude bakinta ta magantu. "Wallahi Ammah ban taba abinda kike tuhumata ba Koda wasa wallahi zan rantse Miki da Alur'an a bani zanyi Alwala in ratse, idan na taba Zina Ammah Allah ya haramtamin shiga Aljannarsa ranar Alkiyama" Ta fada tana wani irin kuka Mai taba zuciyar Mai sauraro. "Shitttt.....kada na Kara Jin wata magana makaranciyar wannan daga bakin ki. Ba zarginki nakeyi ba na kasa samun nutusawa ne tun lokacin da sabbin halayensa suka Fara fitowa, nake cikin zulumi da taraddadi saboda sanin yanda rayuwa ta Zama abinda ta zama, ba komai kansa yayiwa ke kuma Allah yayi Miki Albarka ya bakin Wanda yafi Sahal". Bata iya amsawa a fill ba sai a zuciyar ta. Tun bayan faruwar lamarin Zahra ke cikin damuwa Dan ma Haneeda tana tausarta da kalamai na kwantar da hankali. Ammah ta Kira su Ummee ta fada musu komai sun so kwarai za
🏠