NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 34 of 136

a Sulaiman. Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka dauko hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu. Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one. A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Mata "sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa". Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "ni sunana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?". Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C. Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar gasu Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah. Lokacin da akayi hutu Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman. Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsokana. Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha. Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga FGC AZAREN itama a ss1. A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida. Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai. Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin uba namiji ba itace komai nasa. Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'a, cikin ikon Allah sai komai ya daidaita. Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka dinki ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini. Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito. A kasa suka taka suna Hira har sulaje gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane. Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta fito. Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa. Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar. Gaishe shi sukayi su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa". Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da zafin Kasarmu". Ta fada tana dariya. Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?" Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Allah." Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi. Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu. Har kofar gida ya kawosu suna tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana". Dan murmushi tayi tana fadar. "Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi" Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya takura Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra. Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo ta wuce dakin su. Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu. Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka bijiro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira. Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izininsa duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma ne
🏠