makka kusan abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta.
A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye amfanin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida.
Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji.
Murna gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu.
Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi wata biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem.
Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta haifi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma Ammah.
WACECE FATIMAH ZAHRA?
'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya har Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can.
Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a can yayi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda.
A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga iyayensa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah.
Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar.
Zahra nada wata biyar wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono.
Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja.
Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi Kuma ya koma Abuja.
Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta.
Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar da har abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba.
Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Zahra ta hakura ta barwa Ammah Zahrar.
Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin Kamar nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta.
Wannan kenan.
Ranar da za'ayi jarabawar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta.
Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Zahra ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna".
Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside locker ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana".
Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu"
"To naji maza Allah ya bada sa'a"
A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan".
Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan.
Masha Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako.
A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha.
Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sannan ya fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru