NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 3 of 136

abinda za'a fad'a na yaba da nutsuwarsa idan kaga ba'ayi ba to shima Allah Bai nufi mijinta bane Amma na jima Ina yiwa 'ya'yana sha'awarsa". Kai kawai Malam yake jinjinawa shi lamarin duk yazo Masa a baibai ya jima Yana nazari akan lamarin Fadima kullum Abu daya yake gani mijinta ba Nan kusa take ba bil hasal ma wani lamari yake gani Mai girma dangane da mijin nata da wani irin Haske Amma koda Wasa Bai taba fadawa Alhajin ba sai dai Yana yawaita saka almajiransa gurin yi Mata addu'a. Sun jima suna kullawa da kwancewa a tsakaninsu daga karshe suka tsaya a malam ya tambayi ra'ayin yaron idan yana so la'ba'as. _______ A hankali take sakkowa daga stair din tamkar wani dawisu Tasha make-up da wata gawon Mai azabar kyau Sai karamar pos a hannunta daga bayanta 'yan Mata ne su biyu ko wacce Tasha nata gayun, tun kafin su karasa sakkowa kamshinta Mai saka nutsuwa ya gauraye ilahirin falon. Falon a Cike yake da jama'a kowa ka gani ta amsa sunanta sai tsirarun yara. Da sauri wata ta matso gurin su tana rangada buda, tana fadar "Masha Allah Amarya Allah ya kade hau da bala'i ya bada zaman lafiya Hajiya Zahra suga bayi farin banza jikar hardon fulanin Mubi jikar larabawan Jodan da larabawan madinatul munawwara kaga musu kyawun asali Amarya a gidan Mushahu alherin Allah yakai Miki". Wata daga cikin matan dake zaune ta tashi ta sunga zubawa marokiyar kudin ita Kuma tana Kara Koda Amarya Zahra. Aunty Hasana ce ta fito daga wani Dan korido ta karaso tana kallon kanwar ta ta, tana Kara tasbihi ga ubangiji daya halicci wannan kyakykyawar surar. Hannaun Zahra ta rike tana kallon Baba Tabawa Mai aikinta yanda ta zage tana jero kirari kamar wata marokiya. Dan murmushi tayi tana fadar "Masha Allah, Baba Tabawa yaushe Kika Zama marokiya bani da labari?" Dariya tayi tana fadar " ai ko ban iya ba na koya mu Abu namu bikin uwar dakina guda kinsan biki na d farar kaza balbela ba gayya ce ba, yakuwar kan kabari kenan baking cikin 'yan taushe, murucin kna dutse Baki fito ba sai da kika shirya" Dariya sukayi gaba daya, har gurin da zasuyi bridal shower din kawar Aunty Hasana da Baba Tabawa suka raka Zahra. Sun chashe, sunyi hotuna kamar ba gobe sai dai duk Wanda yasan Zahra yasa Bata cikin walwala haka nan take Jin wata irin faduwar gaba da rashin dadin zuciya Amma ita kanta Bata San taka maimai me yake damunta ba gashi tun jiya take neman wayar Mushahun ta kasa samun shi, haka ta abokinsa Deeni itama shiru a yanda sukayi dasu yau ne ranar da zasuzo Dan har hotel din da zsau zauna sun Kama mukullan ma suna hannun magaji. Dadin dadawa yau sukayi za'a kawo ya'yan yayar shi da wasu cussing dinsa. Sai gurin karfe Tara suka Gama shagalinsu, Zahra Bata koma saman ba inda akayi musu masauki Sai ta nufi bed room din Aunty Hasana na kasa dakin ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta yake tashi ga danyi AC ya gauraye dakin. Head din ta cire ta aje kan bed side locker kusa lamp, gadon ta hau ta kwanta lamo kamar ba mutum akai Dan ko kwakwkwarwn motsi Bata sonyi wata irin kasala ce ta sauko Mata. Ta jima a dakin kafin taji alamun bude kofar Bata daga Kai taga ko wanene ba kamshin da taji ne ya sanar da ita Auntyn ce. Kusa da ita ta zauna tana Kai hannu jikin.wuyanta tare da tambayar "me yake damunki? tun safe Ina Kula da mood dinki Sam bakya cikin nutsuwa". Ta fad'a tana kafe Zahrar da Ido. Yunkurawa tayi ta tashi zaune tare da fadar "Nima bansan me yake damuna ba wlh Aunty Sam bana Jin dadin zuciya ta sai zafi take min Kuma gabana sai faduwa yakeyi". Ta karasa fad'a tana shashhshekar kuka kasa -kasa. "Meye Kuma abin kuka? keda zakiyi farin cikin Allah ya kawo lokacin bikin ba kamar lokutan baya ba da aka dunga samun akasi". Kanta ta kifa a jiki Auntyn taci gaba da kukan ta marar sauti. Bata hanata sai tayi Mai isarta kafin ta Sami zarafin magana. "Aunty wlh Ina ji a jikina kamar wannan ma za'a Sami matsalar kinsan jiya saida nayi irin mafarkin da nakeyi idan za'a fasa aurena". Ta fad'a tana Kara goge kwallar data ciko Mata Ido. Kallon ta kawai Aunty Hasana take ita fa lamarin yarinyar Nan Yana Bata tsoro kada fa namijin Aljani ya aure ta suna zaune Basu Gane ba. Karo biyu ana saka bikinta abun Yana lalacewa toga wannan ma, itama fa kawai daurewa tajeyi tunda Zahra ta fad'a Mata Musbahun Bai kira ba Bai kumazo ba ba wani Kuma nasa da yazo alhalin ba haka aka tsara abunba, Amma sai tayi ta maza tace. "Haba Zahra ya Zaki ringa fadar irin wannan maganar kiyi addu'a ba abinda zai Sami aurenki wannan karon sai Alkhairi, Ina ga da abinda ya hanasu karasowar har yanzu ki jira zuwa gobe Mana maza kiyi sallah kici abinci a sakonki can ki dauko zuwa an jima sai kiyi amfani dashi. _________' GIDAN MLM BUKAR Bayan idar da sallar insha'i Malam da sauran manyan Almajiransa suna Zama ana karatun littatafan fiqihu da hadisan Manzon Allah s.a.w.w, a Nan cikin baban falonsa ake karatun an kwata shi sosai a zuba kujeru na alfarma, saida aka Gama karatun sannan sukaci abinci kamar yanda aka Saba kafin Kuma kowa ya
🏠