NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 136

n haihuwa. Yayin da abin ma ya Fara damun Nanna har ta gaji tayi Masa magana akan ko maganin hausa za'a fata nemawa Rabi'a ne. Amma sai ya nuna Mata ayi hakuri tunda tana ganin consultant na Gynicology a gani idan ba wani cigaba sai ayi na hausan. A Kuma ciki shekarar ne Alhaji Jafar ya koma Abuja da aiki inda arzikinsa ya Kara bunkasa gashi Allah yayi shi Mai sakakken hannu bashi da rowa ko kadan, in dai Yana gari to kofar gidansa Cike take da jama'a, sai Suma mutane suna tausaya Masa akan rashin haihuwa ga dukiyar dai Kama hankadota ake Amma ba magaji. Ana haka Allah ya kawo ibtila'in ambaliyar ruwa a Adamawa state yankin MUBI. Lokacin da gwamnati tarayya zata tura masu zuwa jaje sai sunan Alhaji Jafar ya shigo cikin tawagar vice president. Sun jajje guraren da b'arnar ta afku anyi rubuce rubuce sosai da Alkawarin ka na gwamnatin tarayya sanan an bada kayan agaji ga wadanda iftila'in ya shafa a hanyarsu ta komawa ne Alhaji Jafar suna tattaunawa da Ardon filanin Yana Karayi Masa bayanin abinda ya faru. Suka jiyo maganar mace daga bayansu lokacin ayarin sun danyi nisa dasu, da sauri Ardon ya juya Yama fadin "ho! 'yar nema Saida Kika biyoni Nan ko ma'u?" Dariya tayi tana kare fuskarta da wani littafin Mai Dan fadi dake hannunta cikin shiga take ta Kamala Riga da siket na lace brown sai takalman ta da jaka da mayafinta farare. Har kasa ta tsuguna tana gaishe da Baffan nata kafin ta Dan kalli gurin da Alhaji Jafar yake ta gaishe shi. Baffan nata ta mikawa littafin hannunta tana fadar "Baffa ga project din nawa komai ya kammala". Baki sake Alhaji Jafar ke kallonsu wannan 'yar yarinyar har ta Gama karatu ake nufi ko me" 💋❤ 💋❤️️ AUREN HUCE HAUSHIN 💋❤️ 💋❤️ 🔷PEGE TEN🔷 Story & Written By MAMAN FATIMAH ******Jujjuya littafin project din Ardo yayi, sai Kuma ya mikawa Alhaji Jafar Yana fadin "Duba ka gani Yallabai ni tunda ba ganewa zanyi ba,naji Dadi da Allah yasa aka Gama wannan karatun ba domin na saka auduga na toshe kunnuwa naba da ba'ayi karatun Nan ba, tunda Wanda yaso auren nata yace in dai zatayi karatun Nan shi ya fasa, shi Kuma Dan uwanta na wajen kanena yace karatu Babu gashi tunda tana ganewa Kuma tana so, kaga yanzu duk gurin nan namu ita me yiwa mutane Allura". Kallonta Alhaji Jafar ya karayi,sannan ya kalli Ardon Yana fadin. "Yaushe ta Fara karatun ne na ganta karama amma har ta hada diploma?" Gyara tsayuwa Ardon yayi Yana fadin "wallahi am tun tana aji hudu na furamare Dan uwanta ta kaita aji daya na sakandire tunda yayi wani zuwa suka zauna da kannen nasa yaga tana da kokari shine yace Mata idan ta Gama makarantar tana son taci gaba da karatu, shine tace Masa tana son ta Zama malamar asibiti, to tunda sukayi haka ya kudurci aniyar tsayawa akan karatunta shi yasa da akayi Mata chaaaa akan maganar aure yace Bai Hana ayi maganar aure ba. Amma ya Dora sharadin saidai idan mijin ze barta tayi karatu abinda ya gagara kenan aka fasa Amma duk yan uwanta anyi musu". "Masha Allah. Allah ya Sanya Albarka, haka ake so a rinka barin Yara Mata suna karatu barin ma na bangaren lafiyar da malaman makaranta, yanzu ba cewa kayi ita ke yiwa mutane allura ba da sauran abubuwa? To da batayi karatun ba da basai an tafi wai gurin an nema ba? Ba komai in Sha Allah zatayi auren ta Kamar kowa". Ardo ya amsa da "Allahumma Amin". Ma'un Alhajin ya kalla "Asma'u kin amince na tafi da project din naki na duba a hankali in yasa said dawo Miki dashi". Kai ta gyada alamar Eh. Sunyi sallama da Ardo tawagarsu suka wuce zuwa Yola inda zasu bi jirgi zuwa Abuja. Wannan shine silar haduwar Alhaji Jafar da Ammah, ya koma maida project da Kuma kafa gwanatinsa cikin ikon Allah suka yarjewa juna. Lokacin da magana tayi karfi Rabi'a taso tada hankalinta saida Nanna ta taushe ta da kalamai masu kwantar da hankali. Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu. Amarya ta tare cikin ikon Allah zaman Rabi'a da Asma'u ya kasance Zama Mai tsabta. Wata uku da auren Asma'u ciki ya bullo duk masoyin Alhaji Jafar ya Taya shi murna sosai a lokacin ne Alhaji Jafar ya biyawa Rabi'a makka kusan abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta. A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye amfanin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida. Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji. Murna gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu. Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi wata biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza y
🏠