Azare ne ta jihar Bauch a unguwar fanfon shanu, su hudu ne iyayensu suka Haifa uku maza sai autarsu daya mace amman su biyu suka rayu biyu tun suna Yara suka rasu, sun taso shi da kanwarsa Amina a hannun Babarsu Hajiya Fatima wadda ake kiranta da Nanna, kasancewar Babansu Malam Ibrahim Wanda ake Masa laqabi khalilu Allah yayi masa rasuwa tun Yana aji day na babbar sakandire Amina Kuma tana aji shida na primary.
Sun Sha wahala kasancewar mahaifan su ba Mai karfi bane Bai bar musu wani Abu Mai yawa ba daga gidan da suke cikin sai konaki biyu, tunda Jafar ya Gama babbar sakandire yake zaune a gida saidai dinkin hula da aikin hannu na riguna kusan dashi yake rike Nanna da Amina said Kuma 'yan kulle-kullen kayan Miya daaya kafawa Nanna jarinsu.
A hankali Jafar yana Tara kudinsa lokacin daya da yaga kudin sun danyi auki ya nemi Shawarar Nanna akan yana son ya Fara sayar da Yadiddika na maza, tayi murna sosai ta dinga saka Masa albarka.
Cikin ikon Allah ya Fara kasuwar da kafar dama Nan da Nan abun ya Fara bunkasa da taimakon wani uban gida da Allah ya hada jininsu yake bashi Kaya akan farashi Mai sauki har takai ga Fara tura shi aba Yana sawo Masa Kaya a hankali ya bashi aron kudi masu Dan yawa yace shima ya hada da nasa jarin ya sawo nasa kayan zeyi Masa kokarin shago kafin ya dawo.
Nan da Nan al'amura suka kankama ba'a rufe shekara ba arzikinsau ya Fara habaka da taimakon Ubangidansa ya samu Yara masu amana ya zuba a shagon shi Kuma ya shiga cuku- cukun nema admission Nan University ta Bauchi cikin ikon Allah ya samu course din da ya nema Agricultural science.
Cikin ikon Allah karatu ya kankama, yayin da a gefe ga kasuwanci Yana ta habaka. Lokacin Yana shiga level 300 lokaci Amina ta kammala secondary dinta manema sukayi Mata chaaaa, Amma an kada an raya ta fitar da gwani ta Kiya Wai duk Bata sonsu.
Haha aka tattara aka kyaleta Jafar yaso ya nemar Mata gurbin karatun N.C.E Amma Nanna tayi tsalle ta dire ba za'a wannan aiki da ita ba, haka suka zauna har kusan shekara Amina ita ba karatun ba ba auren ba.
Wata ranar juma'a lokacin su Jafar sunzo hutun karshen first semester na level 400, Nanna ta aiki Amina kasuwa gurin Jafar ta karbo Mata wasu kudi uzurinsu ya taso Mata na gaggawa.
Lokacin da taje baya shogon nasa Yana shagon Ubangidansa Alhaji Dauda, can ta nufa tunda tasan shagon nasa.
Suna ciki Hira da bakon Alhaji Dauda kawai ya hango Amina ta nufo shagon tana gaishe da Alhajin daya fita a lokacin, kafin ta karaso har taso ya nufo ta Yana fadin"lafiya Amina? Daga Ina kike?"
Dariya tayi kyawawan hakoranta jerarru farare tas suka bayyana tana fadin "kai Yaya ba komai fa Nanna ce ta Aiko ni".
Fita sukayi ta fada Masa sakon sukaje shago ya Bata ai Bari ta hau abin Hawa ba ya dauketa a mashin dinsa suka tafi gida.
Da dare Yana zaune a inda suke Hira yaga motar Alhaji Dauda ta tsaya a kofar gidansu da sauri ya tashi ya nufi inda yayi parking sai yaga harda bakon Alhajin Zakariyya suke tare, sun gaisa sosai kafin Alhaji Daudan ya fada Masa Amininsa Kuma Dan uwansa ne yaga Amina Yana so shine nace yazo muji da zafi -zafi akan bugi karfe.
Jafar yaji Dadi sosai zaifi kowa murna idan hakan ta kasance Dan ya yaba sosai da hankalinsa sosai.
Cikin gidan Jafar ya shiga ba jimawa ya fito Yana musu iso ciki sun gaisa da Nanna Alhaji Dauda ne yayiwa Nanna bayanin koma itama irin amsar Jafar ta fada idan tana so ba matsala ba inda aure baya Kai mace Nasarawa batayi nisa ba.
Cikin ikon Allah kuwa Amina taji Alhaji Zakariyya ya kwanta mata a rai Kuma zata iya aurensa duk da fada Mata Yana da Mata harda Yara biyu.
A cikin wata biyu akayi bikin Amina da Alhaji zakariyyan, Jafar yayi Mata komai da uba yake aka kaita can Nasarawa state cikin garin Akwanga.
Wannan kenan.
Haka Jafar yaci gaba da karatunsa har ya Gama ya dawo gida Yana jiran shiga camp.
Lokacin da saki post na tafiya service sunan Jafar ya Fado a cikin masu zuwa Jos yayi murna sosai ko banza Yana jiyo kamshin gida tunda suna makotan jahohi.
Bayan gama zaman camp wata makarantar 'yan Mata jeka ka dawo aka Kai Jafar, Baiyi wata biyu ba Allah ya hada shi da wata yarinya Rabi'a yaji yarinyar ta kwanta Masa tana Kuma da irin Qualities din da yake fatan Samu a gurin matarsa.
Zuwa lokacin gama service dinsu har magana tayi karfi inda iyaye suka shiga.
Wani gida Jafar ya saya kusa da gidansu ya gyara' ba'a dauki lokaci ba akayi bikinsa da Rabi'a suka tare a gidansu. Duk wata kulawarsa da soyayya ya tattara ya baiwa Rabi'a ba abinda ta nema ta rasa sai abinda baza'a rasa ba. Rabi'a irin matan Nan ne masu kissa kafin wani lokaci ta kanainaye zuciyar Nanna.
Kwanci tashi ba wahala a gurin Allah aurensu ya shekara Amma kalubaken da suka Fara fuskanta na Rashn zaman ciki a jikin Rabi'a kusan barinta uku. Ana haka Jafar ya samu aiki da ma'aikatar gona ta jihar Bauchi BARDA.
Cikin kankanin lokaci kofofin wadata suka budewa Jafar kafin shekara biyu ya gina gida Mai kyau sunje makka shida Nanna.
Nan da Nan likafa tayi gaba Amma dai matsalar su na Nan ta rashi