sunan Alhaji Jafar ya shigo cikin tawagar vice president.
Sun jajje guraren da b'arnar ta afku anyi rubuce rubuce sosai da Alkawarin ka na gwamnatin tarayya sanan an bada kayan agaji ga wadanda iftila'in ya shafa a hanyarsu ta komawa ne Alhaji Jafar suna tattaunawa da Ardon filanin Yana Karayi Masa bayanin abinda ya faru.
Suka jiyo maganar mace daga bayansu lokacin ayarin sun danyi nisa dasu, da sauri Ardon ya juya Yama fadin "ho! 'yar nema Saida Kika biyoni Nan ko ma'u?"
Dariya tayi tana kare fuskarta da wani littafin Mai Dan fadi dake hannunta cikin shiga take ta Kamala Riga da siket na lace brown sai takalman ta da jaka da mayafinta farare.
Har kasa ta tsuguna tana gaishe da Baffan nata kafin ta Dan kalli gurin da Alhaji Jafar yake ta gaishe shi.
Baffan nata ta mikawa littafin hannunta tana fadar "Baffa ga project din nawa komai ya kammala".
Baki sake Alhaji Jafar ke kallonsu wannan 'yar yarinyar har ta Gama karatu ake nufi ko me"
πβ€οΈ
πβ€οΈ
AUREN HUCE HAUSHIN
πβ€οΈ
πβ€οΈ
WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH
PAGE NINEπ·(9)
____Akwatuna ne na garari masu tsadedden kyau har set biyu aka shigo dasu, sai wasu irin manyan jakunkuna guda uku, guda Zilai ta dinga gud tana fadin "wani kaya sai amale wane jaki. Allah ya Kara daukaki Fatima ya Dora ki akan makiyanki lallai girma sai dan girma kaga wadda ta gaji arziki gaba da baya"
Inna maimuna ce ta jimko kudi ta dankawa zilai tana fadin "na fanshi jikata tunda kin koma roko".
Dariya tayi tana fadin "wallahi Inna Dana iya kirarin da yafi wannan da nayi Mata. Uwar dakina murucin kan dutse ce Bata fito ba Saida ta shirya, yakuwar akan kabarice bakin cikin 'yan taushe, bikin cikinka sauro yau ga xanzaro a bene" .
Ta Kara kwarara wata gudar.
Da sauri Mama ma tazo ta dankawa zilai kudi tana fadin yau ai ranar farin ciki ce maza bude Mana muga karamar Arziki"
Tunda aka Fara shigo da kayan Zahra tayi dakinsu tabar su Sajidar anan.Hameeda da zilai ne suke fama bude kayan suna santinsu komai na ciki Mai kyau ne ba karya duk wadda ta hado kayan 'yar gayu ce ta gani kasheni komai na ciki classic ne.
Saida suka bude kowa ne akwatin duka Sha biyun.
Ba abinda Inna maimuna ke maimatawa sai Masha Allah,Allah ya kade fitina yasa gurin zamane Allah ya hada arzikinsau.
Duk bidirin da ake Salma na tsaye Bata taba ko tsinke a ciki ba sai cika take tana batsewa Kamar anyi Mata dole sai ta zaune a gurin.
Su Sajida da Mujiba da Hameeda ne suka shigar da kayan falon Ammah.
Sai da suka jerasu sannan Hameeda ta nufi dakin Mama su Kuma su Mujiba suka nufi gurin Zahra.
Wata uwar harara Salma da dokawa Hameeda tafin tayi dogon tsaki tana fadin "Allah wadaran naka ya lalace yanzu ke ko kishin Kai Baki dashi Kika bige gurin jidar kayan kanwar bayanki kina wani washe Baki ke game kirki". Baki Hameedar ta murguda Mata tayi gaba tana cewa "Ina ruwanki Aunty Salma danke bakya ra'ayinta dole Nima sai nabi naki ra'ayi kowa yayi ta kansa kawai ni bana ara na yafa abinda Babu ruwana ba.
Mama ce ta fito daga bed room dinta fuskarta a hade da waya a hannunta kallon Hameedar tayi "to rasa kunya b'eran tanka Dan ta fada Miki gaskiya Zaki kare Mata tana din rashin mutunci cewa nake koni Dana tsuguna na haifeki ban Isa kizo inda nake ba Saida Kika dangana da gurin kanwar uwarki".
Baki Hameedar ta zumbura tayi gaba tana magana kasa -kasa.
"Ai Daman za'a rina tunda Naga kin biyo Mama daki, wallahi mutum ya kiyayi gulma da munafurci in dai yansla son yaga ci gaba a rayuwarsa"
Tana Gama fada ta shige uwar daki.
A waya Ammqh ta Kira Aunty Hasana ta fada Mata an kawo lefen Zahra.
Lokacin da tazo taga kayan ta kadu da gasken gaske, Amma dai Bata furta komai ba kada Ammah taga Kamar Bata son auren ne ko wani Abu.
Sai bayan sallar magariba Mujiba tayiwa su Ammah sallama Sajida ta rakata ita Haidar din Aunty Hasana.
Tun Zahra na tsammanin ganin Hameeda har ta hakura saboda dare ya fara so sai Dan Sajida har tayi barci, sai tayi Kamar ta kirata a waya saita fasa, da taga zaman yayi yawa sai ta dauko alqur'ani ta Fara karatu har Saida daya ta gota sannan tayi addu'a ta shafa.
Kwantawa tayi rigingine tana tariyo rayuwartan ta baya komai ya ringa dawo Mata Kamar lokacin yake faruwa
************_
_
TUSHEN LABARIN
AZARE KATAGUM L.G.A
BAUCHI STATE
UNGUWAR FAMFON SHANU.
Yarinya ce 'yar kimanin sheKara goma Sha biyu haka, kyakykyawar gaske fara irin farin Nan Mai hade da Kamar golden yellow , idanunta dara-dara farare tas sai gashin kanta bakirkirin har gadon bayanta hancinta irin dogon Nan ne har baka bakinta Dan karami Mai dauke da 'yan jaja-jaja pink-pink din lebe, bazaka kirata doguwa sosai ba irin tsaka tsakiyar nan, jikin lublub Kamar Mai rayuwa a kasanshen sanyi komai nata Mai kyau ne Wanda idan ka kalleta saika Kara kallonta Dan Allah s.w.a yayi Mata sura Mai kyau na a gani a Kara kalla. Da sallama ta shigo cikin gida tana fadar "wash Allah Ammah wallahi na gaji wadannan littatafan sunyi nau