, Kara dukar da Kai yayi kafin yace "Daman maganar kayan lefe ne dazu Oga Sameer ya kirani yace ya hado tasa gudunmawar kenan, shine nace Bari na fada maka Dan kasan da zuwansu".
"Ikon Allah shi wannan yaron baya gajiya ne Kamar baisan ciwon nema ba tunda yazo ya riski maganar Nan yake Yi kan jiki kan karfi. Allah ya saka Masa da Alkhairi yabar muku zumunci".
"Ameen" ya amsa.
Harya Mike ze tafi sai malam din ya dakatar dashi, dawowa yayi zauna.
Gyaran murya malam din yafa kafin ta jefo Masa tambayar.
"Sai zuwa yaushe ne kake ganin zamuje ga mahaifan naka kaga dole muje musu tunda wannan lamarin ya faru".
Kai ya sadda kasa Yana fadin "zamuje in Sha Allah Amma Dan Allah a Kara min lokaci da kaina zanyi maganar ayi hakuri".
"To ba laifi Allah ya iya Mana kaje ka Samu su Habibu kuje acan gidan ku kwana kaga sun zuba dukiyar kasan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba".
"To in Sha Allah za'ayi hakan amma ni Ina Nan sai dai su Habib din suje".
"To ai hakan ma yayi Allah yayi Albarka".
Saida ya dudduba dakunan yaran ya tabbatar da komai lafiya lokacin sha biyu ta wuce, dakinsu ya nufa wanka yayi ya saka kayan barci sannan ya hau gado ya bude laptop dinsa. Email dinsa ya shiga Yana duba sakknnin daya samu sakon daya shigo ne ya dauki hankalinsa.
"Ya Salam!".
Abinda ya iya ambata kenan sai Kuma sautin daddad'an ringtone dinsa ya karade dakin.
"Sameer!" Ya fada a hankali yasan za'ayi haka, ya haga wayar Yana fadin "Ta Yaya hakan ya faru?"
Daga can bangaren Sameer din yadan furzar huci Mai zafi Yana fadar "wallahi nayi duk yanda zanyi Amma abun yaki yuwuwa dole ka daura ka kawar da komai muje gaskiya Dan kasan tunda akaje Nan zuwan nake ne Kawai mafita".
"Amman ai kasan halin da ake ciki so kake ace na gudu nabar 'yar mutane Eyeh?".
"Cool down Mana my man abin Bai Kai nan ba aikin daine ya taso na gaggawa Kuma dole sai da Kai za'ayi Dan haka suyi hakuri su aje maka ita zuwa sanda ka dawo ko Kuma ka dauko abarka ku tafi, kaga ai tafiyar tafi yi maka armashi ko?"
Ya fada cikin zolaya.
"Dan Allah ka Zama serious mana, kayi duk abinda ya kamata a Nan goben ka hakura da zuwan ka turo wannan friend din naka tunda yasan gurin ya kawo kayan kawai, Kai Kuma ka Kira Baba malam ka fada Masa daga can sun nemi ganin wakilansu na kasa da jahoshi da kananan hukumomi nasan dai kome ake ciki baze wuce kwana buying zuwa uku ba kaga lokacin na tare a gidana nafi son na barta a Nan gidana akan na tafi Bata tare ba".
"Ko dai.......?"
Sameer ya fada Yana dariya.
"Allah ya shiryeka ko dai me? kasan ni salihn ne ba ruwana da wannan sabgar sai ku".
Kit ya kashe wayar sannan yayi switch off dinta.
Misalin karfe Sha biyun Rana wata tamfatsetsiyar mota Parker a kofar gidan malam.
Akwatuna Yara suka dunga saukewa suna shiga falon malam saida suka Gama sannan baki nufi falon malam din bisa jagorancin Habib sun gaisa sosai da malam suka gabatar Masa da kayan daga Sameer.
Malam yayi godiya ya saka Albarka ba adadi.
Falon malam ya bar musu sukaci abinci suka huta sannan Habib ya rakasu can gidan suka gaisa da Mahmud din.
Sai bayan Azahar suka tafi malam yayi musu Sha Tara ta arziki.
Kayan malam yace suje su duba su gani saboda da an jima za'a Mika musu can gidan Alhajin.
Kaya ne na gani na fada an zubasu Kamar ba gobe, an shigarwa da iya Abu ciki ta gani malam yace ta turawa makotanta na kusa suzo su gani anjima za'a Mika musu.
Bayan fitowa daga sallar la'asar ne Malam Bukar ya fadawa Alhaji yanzu su malam Mudi da Alaramma malam Haruna zasu kawo kayan Zahara'u.
Fada Alhajin yayi akan kayan da za'a kawo Yana fadar "Haba malam Dan me za'ayi min haka ko wancen da aka fasa auren Kai sheda ne ban karbi lefe ba da suka matsa cewa nayi suje da kayan idan tazo saiya ba matarsa".
Kai malam yanjinjina Yana fadin "Anyi hakan Kam amma wannan shima bamu muka hada ba wannan yaron Sameeru ne ya turo dasu dazu yace gudunmawarsa ce aba Amarya"
"Ikon Allah shi baya gajiya da dawainya haka daga wannan sai wance Allah ya saka da Alkhairi ya bar.zumunci na jima banga yaro mai karqmcinsa ba abin duniya Bai rufe Masa ido ba".
Da yamma su sajida suna zaune suna Shira ita da Zahra da wata kawar Zahra Mujiba Nan take makotansu suna dasawa da Zahra sosai sun Kuma yi sabo sosai da Sajida tun lokacin da sake zuwa hutu da Sajidar lokacin suna makaranta.
Ba zato ba tsammani Yara suka shigo da manyan jakunkuna dasu cylinder din gas, ai Zahra na ganin haka ta tashi da sauri ta nufi hanyar shigowa gidan da gudu ta karasa Kamar karamar yarinya suka rungume juna da Hameeda Kamar zasu fadi. Suna rike da hannun suka shigo ciki su Mujiba suna ta faman yi Mata sannu da zuwa, sai daga baya Salma ta shigo tana wani shankanshi Bata kula su Zahra ba Suma ba Wanda ya kula ta, directly dakin Mama ta nufa.
Kamar jira ake Salma ta wuce saiga su Magaji da manyan Akwatunan lefe suna shigowa da sauri Zilai Mai aiki ta warto Babbar tabarma ta baza tana rabsa guda tana fadin "Masha Allah! Alherin Allah ya sauka. Fara Mai farar aniya sukari bakai farin banza