ita.
Wani matashin ne shima ya shigo da manyan warmers da wata yarinya da basket Mai dauke da plates da cokula da cups Suma suka gaishe dasu suka fita.
Tunda aka Fara shigo da wannan karamar arzikin Alhaji sulaiman ya sadda Kai kasa zuciyar idan tayi dubu to a bace take.
"Bismillah kuci abinci kafin mu shiga sallah tunda Azzahar ta gabato".
Alh Jafar ya fad'a Yana nufar kofar fita.
Bayan fitar Alhaji Jafar Alhaji Ismail ne ya kalli Yayansa Alhaji sulaiman "Nifa duk na rude wallahi har na rasa ta inda zamu Fara fad'a musu irin wannan magana duba da irin karamcin wannan bawan Allah".
Ya fad'a yana Jan siririn tsaki.
Dan matashin daya tukosu ne yayi magana "wlh Daddy naso kun hakura da zuwa ita Hajiyar tazo da kanta ta fad'a musu abinda ta kulla, ni ban taba ganin irin wannan ba anyi Abu cikin mutunta juna har an kawo wannan gabar Amma Rana tsaka irin wanna ta taso Babu Dadi ni wallahi tausayin Musbahun nakeyi ya shiga wani hali Amma ita ko a jikinta".
Shi dai Alhaji sulaiman Bai Kara magana ba haka Bai ko kalli abincin ba duk da yunwa da yakeji leonm da ruwa kawai ya sha, Alhaji isma'il da Al-Amin ne sukaci abincin suka fita zuwa masallacin kofar gidan.
Tare suka shigo gidan bayan idar da sallar har da Malam bukar domin shine limamin masallacin.
Sabuwar gaisawa suka karayi Amma wannan lokacin Al-Amin Bai biyosu ba.
Alhaji sulaiman ne yayi Qarfin halin Fara magana Yana kallon Malam Bukar "Dan Allah malam ayi hakuri da abinda mukazo dashi WALLAHI badan Nan gidan bane Babu abinda zai Kara dawo Dani garin Nan".
Yayi shiru ya kasa karasa maganar saboda wani abu daya tsaya Masa a makogwaronsa yana masa tukuki.
Shima Alhaji Jafar wani abune ya tsirga masa har tafin kafarsa ga wata irin faduwar gaba taba gaira ba dalili.
Shiru falon ya dauka na wucin gadi kafin Malam Bukar ya magantu "Alhaji ka Fadi ko menene ba wata matsala ita rayuwa ba yanda Bata zuwarwa bawa ko Dadi ko akasin hakan, Kuma duk musulmin kwarai ai yasan kaddara, ba damuwa ai and Zama daya".
Alhaji Ismail ne ya karbi maganar ganin yayan nasa bashi da niyyar cigaba da maganar.
"Ayi hakuri Malam kan maganar auren yaron gurinmu ne da yarinyar gurinku, wata fitina ta taso yau kwana uku kenan ana Abu daya mahaifiyarsa ta kafe kaida fata Bata amince ya auri Zahra ba duk yanda mukaso gyara abun ya gagara karshe ma cewa tayi idan har Musbahu ya auri Zahra Bata yafe Masa nononta daya sha munyi munyi da fad'a Mana dalilinta na wannan cin zarafin Amma ta kekashe taki fad'a karshema abun ya zamar Mata lalura kamar ta jinni". Tunda ya Fara kora bayani Alhaji Jafar ke maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, domin duk wani karfin gwaiwarsa ya Kare wannan wace irin musiba ce kullum idan auren yarinyar nan ya taso sai an Sami wani akasin ya taso shi Lamarin Nan ya rasa yanda zeyi dashi.
Malama Bukar ma rasa abin fad'a yayi duk wani kuzarinsa ya Kare.
Yayin da su Alh Sulaiman suketa nanata ban hakuri.
Cikin muna juriya da dattako Malam Bukar yace "haba Alhaji ba komai kasan komai nufi ne na Allah Daman Bai Qaddari shine mijinta ba, Allah yasa hakan yafi musu Alkhairi su duka'.
Gaba data suka amsa da Amin.
"Amma dai Abu baiyi Dadi ba wallahi ba Baki nayi musu ba Amma kafin a Sami Mai nagaratr yarinyar Nan zasu Dade suna nema" cewar Alhj Ismail.
Har gurin mota suka raka bakin, har suka daga bakinsu Bai Dena bada hakuri ba.
Bayan tafiyarsu falon su Malam suka dawo jiki a sanyaye duk Lamarin ya cakule wannan wace irin kaddara ce ke bibiyar karamar yarinya haka aure dai dai har uku ana fasawa.
Cikin nuna damuwa Alhaji Jafar ya kalli Malam Bukar yace "malam inshallah Allahu wannan karon zan aurar da Fatima tunda Naga lamarin bana arzki bane ko meye in Sha Allah sai Naga bayansa'.
Tunda Alh ya Fara magana Malam Bukar ke girgiza Kai shima lamarin ya kaishi makura yasan lamarin yarinyar akwai magauta a cikin Amma ganin an samu rata Mai yawa a tsakani ya dauka abun ya wuce ne.
Cikin nuna alhini Malam ya kalli amininsa yace "Dan Allah Alh kayi hakuri kada kayi Abu cikin fushi da kace zaka aurar da ita kada azo ayi aikin Dana sani".
Kujerar dake daura da Malam din ya zauna kafin ya sauke ajiyar zuciya.
"Ko daya banyi fushi da ikon Allah ba kawai dai na gaji da wannan wasan ne kullum na Zama karamin mutum saina Raba I.V na daurin sure azo ace an fasa wasu ma sai su zageni ace Dan bani na haifi Fatima ba na saka ido ana Mata wannan cin zarafin wlh da banyi alkawarin daina hada auren zumunci ba da yau ba sai gobe ba zan aurawa Abdul Hakeem ita. Amma yanzu ma Bata baci ba ka nemi shawarar Mahmud na Nan gurinka idan ya amince na bashi auren ta".
Cikin kaduwa Malam Bukar ya kalli Alh Jafar yace
"Wane Mahmud din, ba dai na Nan gurina ba?".
Cikin yadda da Kai Alh Jafar yace "shifa nake nufi ko akwai wani Mai wannan sunan a gurinka?".
Gargiza Kai Malam din yayi tare da fadar "Babu, Amma Alhaji al'marin Mahmud ba boyayye bane a gurinka kada duniya ta zagemu fa".
Gyara Zama Alhajin yayi kafi ya fuskanci amininsa sosai.
Wallahi Malam bana gudun duk