tsaya mini a cikin zuciya".
Aunty Hasana ta fada.
Sun jima suna tattaunawar kafin Mama ta koma daki tabar Autty Hasanar da Ammah.
Zama Aunty Hasanar ta kyara ta fuskanci Ammar ta Kira sunanta "Anya wannan Mahmud din ba abinda yake boyewa kuwa Ammah Kinga gidan kuwa ga wannan uwar wayar daya canza Mata kinsan kudinta kuwa ? gaskiya I doubt much, ni dai kiyiwa Abban magana da kanki Kamar zefi daukar abun serious akan na Mama".
Can Kuma sajida ce tasa Zahra a gaba tana ta faman zuba.
"Innalillahi! Kinga gidanki kuwa? Allah ya bamu ya taku wallahi Zahra ki godewa Allah. Wallahi Allah ya Gama miki duk wata ni'ima ta ko Ina kinyi gaban da Nan kurkusa dai kafin a fiki za'a Dade ana lalube. Zahra Naga mijinki har mun gaisa ada Ina adawa da auren Amma tunda na ganshi Naga Yana yinsa nasan yanzu ne kikayi aure da mijin daya Dace ke.Kawai dai matsalar za'ace ba Mai kudi bane,amma a yanda gidan da zaya ajeki yake wallahi ko minister ne sai hakan, akwai abinda na gani a gidanki wallahi ban taba gani a gidanki kowa ba duk yawona sai dai a film amma dai a zahiri A'a ban taba gani ba Allah Bai kaini gurin ba".
Tunda ta Fara zuba Zahrar ke bin sajida da idon lokaci daya duk ta wani rude sai zuba take Kamar 'ya 'yan kanya.
"Kin Gama?"
zahrar ta tambayi sajidar.
"Eh na Gama aini an ma yanka ta tashi na fasa tafiyar zanyi waya da Mom taje can Rimin sumailar gurin Baffan kawai, tunda Daman zatazo nan din ba suna kwantagora".
"Ke Kika sani dai tunda Naga kina nema ki Zama wata daban ko dai an canza min ke da wata ne ko Kuma wani abun ya fada Miki ya goge Miki hadda ne?".
"Eh da alama Kam Dan ya fiki iya lafazi gaskiya inaga na Zama 'yar team dinsa fa tunda Naga ke Baki da wayo".
Ta fada tana dariya.
Washe gari tun safe Abba yasa aka Kai furniture's din Zahra gidan Daman Aunty Hasana sunyi magana da Wanda zasu hada musu kayan, kayan kitchen da sauran kayayyakin duk suna gidan Aunty Hasana daga can aka ringa daukowa, masu aikin su suka hada komai na gidan hatta kitchen su suka gyara komai, gidan ba karamin kyau yayi ba, ba karya duk Wanda yaga gidan yasan na 'yar gata ne.Dan wasu irin mahaukatan Turkish furniture's ne wanda kakanninta ta gurin uwa sukayi Mata duk wani abun more rayuwa akwai shi a gidan Nan, bangaren electronics ma sai a cikin lockers aka zuba wasu, komai yayi.
Lokacin da aka Gama gyaran Aunty Hasana da sajida ne sukazo gani ba karamin burgesu gidan yayi ba Dan sai yanzu ne ya fito a asalinsa na kyau da kayatar da Mai gani, komai na gidan unique ne Masha Allah.
A waya sajida ta daukowa Ammah komai. Ita kanta Ammah Kai Kawai take jinjinawa Dan ba karamin burgeta abin yayi ba, sai dai can kasan ranta rudani ne kala-kala domin abin ne duk yazo a hagunce.
Tana tsoron lamarin sosai sai da har abada baza iya jayayya da Alhajin ba Dan da gaske ubane tsayayye Wanda baya nuna banbanci tsakanin abinda ya Haifa da Wanda yake bashi ya Haifa ba, amma harga Allah tana zulumin wannan AUREN HUCE HAUSHIN da Alhajin yayiwa 'yar marainiyar Allah, mazan yanzu sunce suna sonka ma ya kukan kare idan Zama yayi Zama ballantana matar cushe ta San komai Daren dadewa ranar da yaga irin matar da yake so Sai dai zahra tayi hakurin zama Kawai, duk da tasan Bata da haufi akan yarinyar Tata Dan macece har mace abin alfaharin kowa ne namiji ace ya mallaki Kamar ta, to Amma shi lamarin so daban yake duk kyan mutum da asalinsa ba lallai ne ace yana burge kowa ba domin shi dai so makaho ne.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk jikinta yayi Mata wani irin Sanya ta kalli Aunty Hasana tace "Hasana Ina jin wani irin rauni a zuciya ta game da lamarin nan Ina tausayin yarinyar nan rayuwa tana ta walagigi da ita sai nake ganin Kamar laifi nane Dana kafe a barmin yarinyar Nan na hana kakanninta ita ni Kuma nayi sakacin da aka maida rayuwar ta Kamar kwallo ana ta dokata daga Nan zuwa nan".
Ta karasa maganar hawaye na zubo mata.
Abinda tunda Allah ya kawo Aunty Hasana duniya Bata taba gani ba a zahiri gurin Ammah Nan da Nan hankalinta ya tashi sajida ma kukan ta Fara duk da batasas takamaimai man abinda ya saka Ammah kukan ba, tashi tayi ta fice daga dakin jin an Fara Kiran sallar magariba.
Aunty Hasana ce tace "Haba Ammah duk yanda Kika jure bakin cikin baya na abubuwan da suka faru Baki taba zubar da hawaye ba sai yanzu da Allah ya nufa akayi ai godiya Zaki yiwa Allah daya kawo karshen wahalar ba kuka ba".
Gefen zani tasa tana goge hawayen.
"Hasana Ina hango abinda ke bakya hangowa ne,masu iya magana suna cewa matar shige Bata daraja ba irin wannan rayuwar na sowa Zahra ba to sai dai kana naka Allah Yana nasa Kuma nasan ne gaskiya. Ba komai haka Allah ya tsara komai mukaddari ne daga gare shi, naji Alhaji Yana maganar zuwa juma'a za'a kaita".
*******Tun bayan kammala karatunsu na bayan insha'i da suke na littafin iziyya yake zaune a kusa da Baba malam har kowa ya watse ya rage saura su biyu tunda malam yaga haka yasan da magana a bakin Mahmud ne.
"Ya ya akayi ne Mahmuda?"
Malam ya jefo Masa tambayar