NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 136

ida ta fada min halin da ake ciki wallahi daba final muke ba Allah da barinta zanyi c/o na taho gida har fada mukayi da Salma Wai ai sai inje na baiwa Mushahun hakuri ya dawo ya aure maganganu dai gasu nan ki Bari kawai ai jibi zamu Gama in Sha Allah komai dare a gida zan kwana". "Allah ya yarda ki Bari kawai wallahi Ina cikin yanayi akwai damuwa Dan Allah kizo ko naji sauki abubuwan". Ta fada tana share hawaye, sukayi sallma Dan it ma Hameedar kukan take. Wai ita Mushahu ya yiwa haka, duk wadanda suka fasa aurenta Bata taba Jin Wanda ya Bata Mata Rai ya Kuma tsaya Mata kamar wannan ba ai ko wace irin matsala ce ita ya kamata ya Fara fadawa ba ya yanke mu'amala da ita ba a lokacin da take matukar bukatarsa ya manta shakuwar dake tsakanin su da alkawarirrikan da suka yiwa juna. Kwantawa tayi tana tunanin baya a haka wani wahalallan barci yayi gaba da ita. **********Tun Yana tsammanin ganin ta bude data ta duba sakon har ya cire Rai da hakan. Lambar Abdul Hakeem ya Kira sun jima suna waya kafin suyi sallama. Laptop dinsa ya janyo yaci gaba da aiyukansa sai kusan azzahar ya Gama. toilet din cikin dakin ya shiga ya dauro alwala,a masallacin hotel din Yaya sallah lokacin daya fito Kiran Habib ya shigo Masa "Wai Dan Allah kana Ina ne tun dazu muke nemanka kazo masu aikin hada furniture's din Nan ne suka Gama da cabinet din kitchen". "Ok gani Nan inaga kada kayi nisa zuwa an jima su Aunty zasuzo suga gurin" Ya fada. Yana nufar gurin da ya saba aje lifan din Habib. Wayar Ammah Abdul Hakeem ya Kira ya fada Mata Mahmud yace a turo a gano gidan an Gama gyaran, dakin Mama Ammah ta shiga ta fada Mata sannan Kira Aunty Hasana ta fada Mata kafin ta wuce gurin Alhajin ta fada Masa tunda shiya dawo daga gidan gonar sai su Abdul Hakeem ya baro suna yiwa shanu Allura da Basu magunguna. Wurin karfe biyar Aunty Hasana ta debesu a mota harda Sajida suka nufi Hayin bankin cikin jagorancin Habib, lokacin Inna Bata Nan taje MIYA gurin wata aminiyar ta da sukayi aikin Haji shekara daya. Duk cikinsu ba wadda Bata kadu da ganin gidan ba domin ba karaya an narka mahaukatan kudi a gidan bazaka tab'a cewa renovation akayi Masa ba, bedroom's ne guda uku biyu suna kallon juna dayan Kuma daga gefe da alama yafi sauran girma Kuma shi kadai ne a rufe, sun zagaya ko Ina sai santin gidan Sajida tace tana ta daukar video, falon kadai abin kallo ne duk da ba komai a cikinsa sai fitilu da aka kunna sai Kuma AC da aka ware. Hajiya mama ce ta kasa hakuri ta leka ta Kira Habib Nan falon ya shigo Yana fadin "gani Mama" Yana Dan rankwafawa. Aunty Hasana mama ta kalla "Hasana Dan Allah ki tayani tambayar yaron Nan tunda shi namu ne na gida baze cucemu ba, Wai wannan yaron sana'ar me yake daya iya Kama hayar wannan uban gidan"?" Kara risinawa yayi Yana fadar "ba haya ya Kama ba Baba malam ne ya bashi kyauta, sai Kuma kungiyar yake yiwa aiki suka kawo masu aiki suka yiwa gidan 'yan gyare -gyare harda kayan daki ma suka zuba masa, Bismillah Bari na bude muku ku gani yanzu ba dadewa zuka Gama hadawa da kitchen din suka tafi". Dakin ya bude musu ba Hajiya mama da take ta kwana biyu ba, ko Aunty Hasana da Sajida Saida suka Zama 'yan kauye Dan tunda suke Basu taba ganin irin wanna gadon a zahiri ba, ita kanta aunty Hasana lamarin Yana neman ya gagari tunaninta fa ance Almajirin Baba malam to Amma idan aka saka mizanin hankali abin yafi karfin yanda aka fada to wane irin NGO's ne da suke irin wannan aikin akan daidaikun ma'aikatan su haka?" Gaskiya abin akwai abin dubawa. Lokacin da suka fito harabar gidan ne wata Hilux ta shigo da kaya a bayan motar mutane uku ne a motar bakar fata biyu fari daya Kamar balarabe Kamar kwara. Kameme Hajiya mama ta hanasu tafiya sai da aka sauke kayan ta gani abinda da suka Gane irin katuwar plasima din Nan Mai cin Rabin bangon Nan ne kawai amman sauran tarkacen Basu Gane komai ba, haka suka kada suka tafi mama nata mitar "A'a da sake Alhaji ya titsiya yaron Nan saiya nuna Iyayen shi kafin a Kai Masa yarinyar Nan haka kawai aje ayi kitso da kwarkawata mutanen yanzu ba abin yarda bane sai kaga mutum har mutum Amman a Baki malam a ciki Kuma Fir'auna". Maganar data Basu Aunty dariya kenan. 💋❤️ 💋❤️ 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ 💋❤️ 💋❤️ STORY AND . WRITTEN BY MAMAN FATIMAH PAGE EIGHT Lokacin da suka shigo gidan ana ta kokarin daura alwalar sallar magariba. Sai bayan sallar insha'i ne Mama ta shigo dakin Ammah suka hadu da Aunty Hasana suna fadawa Ammah yanda suka gano gidan da Kuma yanda abin ya daure musu kai. Nisawa Ammar tayi tana fadar "Mama ki Sami Abban kiyi Masa bayani yanda ze fahimta kinsan yanda suke da malam bana tunanin wannan abun ze saka ya canza ra'ayinsa duba da yanda ya yanke hukuncinsa Bai nemi shawarar kowa ba". "Aiko dai ya kamata ayi wani Abu gaskiya Nima lamarin ya
🏠