i Ina ma ita ce haka, wasu hawayen ne suka ciko idanunta a hankali tace "Ya Rabbi ga baiwarka Mai rauna ka jibinci lamarina dan Isar Manzon Allah s a.w.w. kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka kada ka Bari makiya su yi min dariya ka bani rinjaye ka dorani akan duk Wanda yake son Hawa kaina".
Ta Mike tsam ta nufi toilet din cikin dakin sai Kuma ta fito saboda shaf ta manta kafin su kwanta taga famfon ya dauke Kuma da alama ba'a kunna layinsu na tanki ba. Cikin rashin tsoro ta bude kofar ta fita zuwa bayan part din Mama don ta kunno ruwan, gurin ta dosa gadan gadan sai Kuma tayi turus, magana take jiyowa daga wurin da sauri ta koma baya dan bata San abinda zata gani ba. Tana tsuma ita fa duk da Bata da tsoro amma tana tsoron ganin abinda yafi karfin idonta ko Kuma wani mugun abun.
Dole tayi hakurin yin sallar a koma ta kwanta tana ta sake-sake har kusan Asuba, ba Kuma taji motsin wani na tada hankali ba.
Saida Sajida ta tashe ta lokacin har an Fara sallah a masallacin gidan nasu.
A gurguje tayo alwala da alama Sajida ce ta shigo da ruwan.
Bayan sunyi sallah zaman Azkar sukayi har lokacin da gari yayi shahhh alamar wayewa, sannan suka koma suka kwanta. Dukkan su ba barci suke ba, Zahra ce ta danyi tsaki kadan ta tashi zaune.
Kallonta Sajida tayi.
"Yaya Bestie akwai damuwa ne?"
Dan juyowa zahrar tayi tana kallon sajidar tana Kara wani tsakin "nifa wallahi na fada Miki tsoron mutumin nan nakeji tun ranar Dana Fara ganinsa a gidan Baba malam nake Jin wata irin shakkarsa. Dan Allah a haka zamu rayu bana ko son kallon idanunsa? Kinsan wani tarin abin haushin jiya fa hannu yasa ya dago fuskata Wai dole saina bude idona na kalle shi ko Kuma ya bani mamaki, Kuma fa ranar Nan a asibiti har wani shafar min fuska yayi Yana fadar nayi hakuri da wannan hadin shima ba so yake ba, kawai yayi biyaya ne tunda baze iya yiwa su Abba musu ba, amma ni Ina iya fada musu bana so".
Baki Sajida ta rufe tana kunshe dariyar ta. Kai ta shiga girgizawa tana fadar Babbar magana ki fadawa su Abba bakyaso! Wato ke ga marar ta ido ko? Shima har yasan kimarsu da baze iya yin musu dasu ba saike ce marar kunya Zaki Fadi Baki so, ki rabu dashi kwaai abinda nake so dake yanzu ki koyi dakewa a gaban nasa sannan ki daina tsoron idanun nasa, Wai tsaya fada min menene a cikin idon nasa da yake firgitaki duk girmanki da wayonki da wayewar ki?"
Wani shagwabe fuska tayi kamar Mai Shirin fasa kuka.
"Bazaki gabe ba, ni kaina bansan ya zanyi ba saboda shi fa na daina zuwa gidan Baba malam tunda lokacin kullum Yana tare da shi kuma sai yayi ta kallona yana tsareni da wadannan idunuwan nasa kamar Mai jin barci".
Yanzu dariya sosai Sajida keyi harda kwalla tana fadar Babbar magana tab kice abin asali ya Samo shi ai kaya ne suka tsinke Masa a gidin kaba kece dai kike bulayi"
"Kamar yaya?"
"A'a bazakiji mutuwar sarki a bakina ba ai tunda an hada anyi Mai walahar...".
Sautin kiran waya ya dakatar da shegantakar da sajidar ke mata.
Wayar da aka kawo Mata jiya ce ta dauki kida, Sajida ce ta Mika hannu ta dauka M.M DANGE ta gani Yana yawo akan screen din.
Zahra ta mikawa tana fadar oga ne da alama a Sha soyayya lfy. Tayi waje tana fadin Bari naje nayiwa Ammah shara.
Bata daga Kiran ba har Saida ya kusa katsewa kana ta daga tasa a kunnenta. Daga can taji Yana fadar "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyar ta a amsa Dan da gaske in dai zata ganshi ko taji maganarsa kasa samun nutsuwa take.
Sake maimaita sallamar yayi, da kyar ta amsa masa tare da fadar " Ina kwana?"
Shiru taji ba'a amsa ba kamar ma an sauka daga layin, amma ga mamakinta tana dubawa sai taga Yana nan, itama shirun tayi kudin sunata tafiya saita saka handsfree ta aje wayar kusa da daga gefe tana kallon ikon Allah.
Saida ya mula Dan kansa "yace ya jikin naki I hope kin shan maganinki?"
"Eh" ta fada a takaice.
"Fine"yace shima a takaicen.
Ita mamaki ma yake Bata har wani turanci yake jefawa a magana kamar gaske.
"Sai an jima ta fada tana kokarin katse Kiran.
"Kada ki kuskurs ki kashe min Kira" ya fada in serious tongue.
Shiru tayi tana mamakinsa sai wata izza yake Mata kamar wani abin azo a gani.
Muryarshi ta tsinkaya Yana fadin ki bude data na turo Miki sako idan da abinda kike bukatar ayi ko a Kara sai ki fada min, take care".
Kit ya kashe kiran.
"Kutt!" Ta fada "amman gayen nan yama Raina ni wlh Wai kada na kashe Masa waya"
Kwafa tayi "zakaga na kiraka ganin idon ka" ta Jafar da wayar tana mita.
Taso yin barci Amma ta kasa dole ta hakura, wayar ta Kara daukowa tana kare Mata kallo.
Number din Hameeda ta Fara sakawa tunda taga sabon layi ne ya dauke natan, ga mamakinta sai taga sunan Hameedar ya bayyana ba bata lokaci ta kira.
Tana ta ringing kamar baza'a dauka ba sai Kuma ta daga da sallama ai tana jin muryar Zahra ta Fara mita "yanzu Dan Allah kin kyauta tun jiya nake neman layinki Amma shiru na Kira Mama nace ta Baki tace min bakya Jin Dadi kina barci, wallahi Kinga yanda hankalina ya tashi kuwa ki Bari lokacin da Saj