NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 136

nkin suka Fara zuwa gurin masu aikin gidan Masha Allah aikin yayi nisa kamar ba jiya aka Fara ba Sam an canzawa gidan fasali kamar bashi ba, duk abinda ake bukata Sameer ya danka shi a hannun Binya. Sannan suka nufi cikin gari. Wani mall suka shiga Mahmud ya jido kayan fruits dasu kayan tea sai chocolates dasu farm fresh yogurt da fresh milk. Leda uku aka cika manya Saida suka dauki hanya Sameer ya kalli Mahmud yana fadin "wadannan kayan fa yallabai na waye". "Dubiya zamu saika Bata tunda ni dai kowa yasan bani da kudin sayansu. 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️ 🔷 Page six🔷 P📖🖋️ ________Sun jima a gurin Baba Malam Yana yiwa Sameer godiyar dawainiyar da yasha akan wannan lamarin, sannan yayiwa Baba Malam din sallama akan zai wuce sai hutu ya Kare zasuzo da mutanen su suna son su kawo wasu ayyukan da za'ayi. Har gurin mota Malam dasu Habib sukayi Masa rakiya, Baba malam Yana fadin "Bari muyi addu'a". Nan yaja doguwar addu'a akan Allah ya tsare hanya, har Sameer ya shiga mota ya fito ya nufi Malam Wanda har ya Fara tafiya, sai Kuma yaja ya tsaya Yana jiran karasowar Sameer din. Dan risinawa yayi Yana fadin "ko za'a samu Wanda ze rakani na Kara dubo jikin wannan yarinyar?" Wani kallon kasan ido Mahmud ya bashi dashi "Wai yarinya". "To! To! Masha Allah ai sai kuje da Mahmud din da Habibu kuga jikin, ai wannan tunani ne Mai kyau.Nima na shiga da safe gurin Alhajin naji yata kwana". Har cikin harabar gidan Sameer ya shiga da motar, Abdul Hakeem Habib ya Kira kafin su shigo ma ya fito Nan Harabar gidan Yana jiransu. Shi yayi musu jagora zuwa falon Abban, yayi murna sosai da ganinsu sun gaisa sosai sun masa godiya sosai da karamcin da yayi musu, yaji dadi sosai Dan har ya ringa tsokanar Sameer Yana fadar "wato tunda kazo gabatar da aikinku ban sake ganin kafarka ba a gidan Nan sai yau dana baku Mata ko? Dan na lura baka da aminin daya wuce Mahmud a garin nan. Masha Allah, Malam ya fada min duk Fadi tashin ku akan lamarin Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci". Suka Amma da "Amin ya Rabbi". Mahmud Alhajin ya kalla Yana fadin "kayi hakuri fa Mahmud munyi maka nauyin kuka". Kai ya gairgiza Yana fadin "ko daya wallahi ba komai nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya Kara lafiya Nisan kwana Mai albarka" "Allahumma Amin. Allah yayi Albarka, ya baku zaman lafiya ya baku zuru'a Mai Albarka, sai ayi ta hakuri da lamarin Mata fa. Abdul Hakeem ku shiga ciki su gaisa da Iyayen nasu". Wannan shine shigar Mahmud na biyu gidan, na farko lokacin da magaji yayi accident da mashin suka shigo shida Abdul Hakeem da Hamza ya duba shi a dakin Ammah, dan ma lokacin ba kowa a gidan sunje gaisuwar mutuwa. Directly dakin Hajiya Mama Abdul ya nufa dasu, Zilai Mai musu wanke wanke ce tayi zuruf ta shiga dakin Ammah. Tana fadin "Ammah Ina Jin fa ga mijin Zahara'u Nan sun shiga dakin Mama shida Abdul Hakeem da wasu inaga abokansa ne". Ta juya ta fita. Gyalen Inna maimuna Ammar ta dauka dake kusa da ita ta yafa a jikinta. Da sallama Abdul Hakeem din ya shigo Yana fadin Bismillah ku shigo Mana, a nan kan carpet a kasa suka zauna suna gaishe dasu Ammar tare da tambayar Mai jikin. Abdul Hakeem ne yace " Inna mijin Zahra ne da ubangidansa suka shigo duba ta shi yau ze wuce shine yace a rako shi ya Kara dubata da jikin nata". "Kai Masha Allah an gode madallah Allah ya saka da Alkhairi ya maida ka gida lafiya". Inna maimuna ta fada sannan ta kara da cewa "to waye angon nawa Dan nice ta karfe ita wannan Farafarar ba wani abun azo a gani zata iya ba ni kuwa ko banza na tuka maka tuwon dawa da man shanu ko ba haka ba?" Ta tambaye shi tana kallonsu. Duk dariya sukayi Amma shi gogan Dan murmushi yayi kadan Yana basarwa. Abdul Hakeem ne ya nuna Mahmud Yana cewa. "Ga angon naki nan nagama kamar kunyarki yakeji" "A'a! Masha Allah tubarakallah Mai gidan nawa wanke hannu daka taba ne, kaga dago ka kalleni ni Kaka ce kada kaji wata kunya ta". Kara sadda Kai yayi shifa duk jinsa yake wani iri Wai shine a zaune a dakin surukai Ashe da gaske ana jin kunyar shi wallahi da ji yake kawai fada ake ba wani nauyin da akeji Saida ya same shi yanzu yake gaskata hakan. A kaikaice Ammah ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a zuciyar ta, ita bataga wata makusa ba a tare dashi Kuma idan ba idon tane yake Mata gizo ba sai taga duk cikin Wanda zasu auri Zahrar a baya bataga Mai nagarat wannan yaron ba. Albarka da nasiha dai ya Sha ta gurin Inna maimuna. A haka suka fito daga dakin har suka fito compound din Abdul Hakeem Bai fito ba sai duba agogo Sameer keyi Yana mita. "Nifa bana son nayi Rana a tafiyar Nan gaskiya, Naga alamar kuma neman kuke kusa nayi yamma ma". Kafin Mahmud ya bashi amsa Abdul Hakeem din ya fito da sauri da key a hannunsa Yana fadin "kuyi hakuri key din ne ba'a gani ba da wuri ku karaso ciki kafin Zahrar ta fito ku gaisa". Mahmud ne yace "Kai haba da an kyaketa ta huta ita da Bata da lafiyar kirki". Karamin falo ne da kujeru masu kyau sosai da kayan kallon alama an tana deshi n
🏠