NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 130 of 136

dan a cikinsu, to shi yaushe ya dawo? Haka zuciyarta ta dunga sake-sake. Fita Umma tayi ta Bata guri ta canza Kayan, jiki a mace ta fito ta iske Umma da Ya Abba a parlourn, gaishe da Ya Abban tayi ya amsa Yana fadin "wallahi kin wahalar da mutane da wannan Daren Kika sakasu fitowa har da mace Ina jinma mijinta ne" .ita dai zahra Shiru tayi Masa ta nufi Hanyar fita daga parlourn tana fadin "ummah na tafi Saida safe". Ta fada tana yin gaba "to Allah ya tashemu lafiya kiyi hakuri da safe idan Allah ya kaimu ki bude wayar zamuyi magana". "To Ummah in Sha Allah Zan bude". Suka fice daga Fallon. Ya Abban Yana biye da ita tun kafin ta karaso Rukayya ta taho cikin sassarfa ta ringume Zahra tana fadin "wallahi kin dauki alhakina da Hajiyar makwarari Kinga kukan da muka Sha yau? Tambayi Ya Sameer kiji duk kin tashi hankalin mu". Wani sanyi ya ratsa Ya Abban Jin Rukayya ta ambaci Sameer da yayanta, daman Kuma yaga Kama ta zahiri duk da dare ne Bai Hana shi ganin kamannin nasu ba. Shiru zahrar tayi Mata ita sai Yanzu taji wata kunya duk ta rufeta, me kenan tayi? Shike Nan zasu dauka fa tayi yaji ne dole ta magantu. "Wai Dan Allah Aunty Rukayya ku kasa barina nayi kwana ko Daya ne a gurin Ummata nifa bada wata manufa ba na taho kawai dai nasan idan nace zanzo ba Bari Oga sameer zeyi ba zece saina nemi izinin....." Sai tayi Shiru. "Izinin wa za'ace ki nema?". Gaba tayi kawai ta nufi gurin da Sameer yake tsaye jikin kofar driver, da wannan damar Ya Abba yayi amfani ya matso kusa da Rukayya yana fadin "Ashe Aunty tasha kuka zanso Naga kina matse hawaye". Kallonsa tayi haka nan taji yayi Mata kwarjini. 'yar dariya tayi tana fadin "Ina yini?" "Lafiya kalau beauty, ki saka min number ki Zan kira naji ya kukaje gida tunda sister Zahra har wayar tayiwa tawaye". Ya karasa Yana murmushi itama murmusawar tayi tana karbar wayar, number ta saka Masa ta Mika Masa wayar tana fadin "bari na wuce ya Sameer Yana jirana" Tayi gaba. "Ok saina kira shima gurin Sameer din ya nufa sukayi sallama, ya leka ta window Yana yiwa Zahra magana. Tunda suka dauki hanya ba Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciyar Zahra ke sauka kadan- kadan. A hankali zahra ta bude Baki tace "Dan Allah oga sameer kayi hakuri na Bata maka Rai bada niyya nayi ba kawai dai Ina son Naga Ummah ne Naga kuma kamar bazaka yarda naje na kwana ba". "Ba komai kawai, Daman Yanda su mommy suka tada hankalin su ne ya daga min hankali nasan ba Bata zakiyi ba tunda da kafarki Kika fice". Shiru tayi tasan magana ce ya fada Mata a kaikaice, tasan a kule yake da ita kawai dai Batasan dalilin Daya hana yayi Mata buyaji ba, Dan taga alama ya iya tijara Yanda ya karewa Rukayya dazu ko shi yasa taja bakinta tayi shiru Yanzu. Sha biyu da minti goma yayiwa Mai gadin gidan horn Saida ya leko shima Sameer din ya fito Yana ko waye sannan ya bude. Yana shiga da motar Maimakon yaje kofar main parlourn sai taga yabi ta baya ya nufi wani gani Mai azabar kyau ko Ina tar kamar dauko ginin akayi aka aje ga wata 'yar baranda data hade ginin biyu an saka glass anyi kamar katanga da wasu irin flowers masu kyau a jere ana ganinsu gurin yayi matukar kyau da burgewa a kusa da steps din da ze sadaka da Main parlour, Zahra ba tayi kokarin bude side din da take zaune ba, dan juyowa Sameer yayi "Dan Allah kada maganar nan ta fita kawai da safe ki fada musu mun Dade a Asibitin ne yasa Kika bamu dawo da wuri ba sun kulle, kiyi using da Nan kawai ki barsu su a can, Rukayya zata kawo Miki kayanki da safe kiyi idan Allah ya kaimu". "To nagode". Abinda ta iya fada kenan, ta bude ta fita Rukayya man ta fito tana fadin " Bismillah kizo muje na rakaki". Tare suka jera suka hau zuwa kofar, ita Kanta kofar abin kallo ce ita Yanzu zahra abin har ya daina Bata mamaki so take taga iya gudun ruwan bayin Allah nan Kullum lamarin su ba baya yake ba gaba yakeyi daga Nan sai can suna shiga ta Kara jinjina girman lamarin Wai shi wannan abokin nasu wane irin kusancin ne a tsakanin su da za'a dunga sauke ta a duk inda akayi ra'ayi. Wannan part din yafi wancan komai parlour sun Kai hudu, a cikin parlour na uku ne suka taka steps ya Kai shida sannan suka shige want korido ko Ina tadal sai wani special kamshi ke tashi bedrooms ne guda biyu a jere, Rukayyar ce ta Dan juyo tana murmushi "to madam gasu Nan saiki shiga Wanda kike so ki kwanta, tunda kin samu muna yawon dare kamar marasa gaskiya, Zan Baki shawara sai kin Zama jaruma fa a gidanki Dan Ya Mahmud wallahi Mata rubibinsa suke, idan kikace Abu kadan Zaki fece kece ki tafi kece a kwana Dan idan yayi wata tafiyar sai ki kwana hamsin Baki saka shi a idonki ba, pls you have to be very strong gaskiya kada ki yarda a gano Ina kike da lapse akwai damuwa kwarai ki rike mijinki da kyau ki mutunta shi ki girmama iyayensa zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah, zabi na rakaki dakin na wuce barci Kuma nakeji tunda Allah yayi Mana gyadar dogo ya rabamu da kwanan zaune to matar big bro ta Bata Ina Ni Ina barci ai sai kwana sallah". Ta fada tana 'yar dariya. "Ki sakani
🏠