NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 136

dewa Allah s.w.a a cikin kowane Hali mutum ya Samu kansa, kowa yasan yanda lamarin Auren Uwata ya ringa kasancewa a baya abune ba Mai dadin maimaitawa ba, to wannan karon ma tarihine yaso maimaita kansa Amma na yanzu sai yafi sauran tada hankali ni Kuma Naga a wannan gab'ar bazan Kara bada wata kafa ba wadda za'a dunga walagigi da rayuwar yarinya karama ba kamar Uwata. Sunanta Ya kira Fatima dago ki kalleni, cikin girmamawa ta dago kanta kamar yanda yayi Mata umarni. Hannunsa yasa ya nuna kansa yace kina ganin zan iya zaluntar k?" Da sauri ta girgiza Kai hawaye na zubo mata. Yace "To Fatima na daura Miki aure da bakon yaron Nan Mahmud na wajen Aminina Malam Bukar". Duk da taji haka daga bakinsa a jiya Amma Bai hanata kara shiga rudu ba saboda wannan taji daga bakin da bazeyi Mata karya ba, Nan da Nan ialahirin jikinta ya shiga rawa wallahi ita a jiyan jinsa kawai take gani take kamar almara ce kawai. Muryar Abbansu ce ta Kara katse Mata tunani "kiyi hakuri Uwata kowa da irin jarabawar da ubangji yake Masa ki dauka taki jarabawar kenan, ki yadda da kaddararki sai Ubangiji ya jibinci lamarinki wannan ba hadin kowa bane hadin Allah ne, kiyiwan mininmi biyayya in Sha Allah zakici ribar rayuwa, ki cire yaron Nan Musbahu daga zuciyarki ki rungumi abinda Allah ya baki. Allah yayi Miki albarka yanda Kika yi min biyayya Allah ya Baki 'ya'ya Wanda zasuyi Miki biyayya kema, Allah ya albarkaci aurenku ya tsone idon makiya da mahassada". Hajiya mama ce ta fasa Kuka tana fadin "Haba Alhaji wannan wane irin danyan hukunci ne? ya zaka dauki 'yar marainyar Allah ka baiwa Wanda ba'asan asalinsa ba, ai duniya saita zage ka Dan Allah ka janye maganar Nan da wannan ba gara kaba salmaun gidan Hajiya Dago ba tunda ya jima Yana son yarinyar Nan Amma ka Hana shi" Kowa a falon kallonta yake ba Wanda ya tofa sai danta Hamza yace "haba mama menene haka kikeyi Dan Allah kiyi shiru da wannan maganar salmanun me Allah ya sauwake me za'a da wannan zuri'ar". Hannu Abban ya dagawa Hamza Yana fadin "ya Isa haka tunda ka Bata amsa basai nace komai ba, Amman ki rubuta ki aje in Sha Allah sai wannan auren ya Zama abin kwatance Kuma abin alfahari duk Wanda ze zageni ya Dade Bai zageni ba, Kuma duk Mai ganin zalunci ne yasa na aurawa Fatima Mahmud na barshi da Allah wallahil Azeem ban taba kallon Uwata a matsayin 'yar wani ba kullum Ina Mata kallon 'yata malak malak a makaranta ne kawai ban saka Mata sunana ba shima nayi haka ne Dan tasan nata mahaifin ta rinka Yi musu addu'a". Addu'a Abban yasa Imama yayi yaba kowa izinin tafiya Amma yace Ammah ta tsaya ita da Hajiya mamar da Inna maimuna da Maman lafia. Aunty Hasana ce ta kamo hannun Zahra zuwa dakin Ammah tana kuka, yarinyar tausayi take Bata kamar yanda Abban ya fad'a ana walagigi da rayuwar ta. Cikin bed room din Ammah suka wuce, bayan sun zauna ne Auntyn ta riko hannun Zahrar "kiyi hakuri kinji Allah Yana sane da halin da kike ciki, Dan Allah kad'a ki watsawa Abba kasa a Ido ki bijirewa auren nan wallahi irin wanna auren Yana albarka fiye da tunanin". Wasu sabbin hawayen ta goge. Cikin shashhshekar kuka tace "wallahi Aunty nifa tsironsa nakeji idan muka hada Ido wani Abu nake gani a idonsa". Sororo Auntyn tayi kafin tace "ban Gane ba tsoronss kamar Yaya, Daman kinsansa ne runtuni?. Kai ta gyada Mata alamar Eh. "Allah ya kyauta" kawai Auntyn tace. "Ko meme ma dai wannan tsakaninku ne kin gyarota can". Ta Mike tana fadin "Bari na koma gida sai zuwa an jima zamu shigo da Sajida da Amatu itama Bata tafi ba jiyan. ********Tun bayan suka dawo daga sallar Asuba Mahmud yake ta faman aiki a cikin laptop dinsa, Yana kallon Sameer Yana kwasar barcin gajiya. Bai gama aikin ba sai kusan karfe takwas na safe, kai tsaye toilet ya nufa ya jima a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunsa karami Kuma a hannunsa ya goge sumar kansa me baka sidik Mai laushi Saida ya shirts cikin wani farin yadi filtex marara nauyi ya feda turarensa Alburaq sannan yaje gefen bedside ya dauki wayarsa ya kunna. Abinci ya bukata a kawo musu, yana Gama wayar Kira ya shigo sunan Habib ya gani, ya daga da sallama daga cen Habib Fara fadar. "Habe Dan Allah dukka tadawa Baba malam hankali baka kwana a gida ba abinda baka Saba ba Koda wasa duk dare zaka dawo Amma jiya daga Bari kaje ka dawo shi kenan kayi layar zana Kuma ka Kama ka kulle waya". Dariya yayi Yana cewa "kana tunanin Kona bi dare nayi Gudun auren dole ko?" Shima Habib din dariyar yayi. "Ka Gudun Mana idan ka Isa mai wannan tsaleliyar Ina zaya ya barta koka gudu ka dawo da kafarka, kawai da malam ne ya matsa yaji kana ina". "Ok shi kenan Bari na kira shi Dan hankalinsa ya kwanta Ina Nan tare da Oga Sameer shine ya rikeni nayi Masa wani aiki". Yana kashe wayar ya nufi sofa ya zauna yana janyo stool din da aka Dora abincin. "Oh ni Sameer yaushe na rikeka? ka rikeni dai ka Hanani tafiya ka barni da kame kame ga madam can tana fama da kanta ba mataimaki gaskiya yau in Sha Allah sai kano". Ya fad'a yana nufar toilet shima. Can hayin ba
🏠