ar wannan lokacin".
Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida.
Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa.
Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 42.
_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.
Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga".
"Yanzu ya za'ayi kenan?"
Rukayya ta tambaya.
"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba.
Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.
Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"
Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.
Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.
A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala.
"Wai menene?"
Ta fada cikin damuwa.
"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".
Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".
Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta".
Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta.
"Ka Kira ka fada masa?"
Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".
*** *** *** ***
Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"
Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".
"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya".
Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"
Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan".
"Eh zamuzo Aunty zahra".
Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta.
Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.
Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne.
Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".
"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare".
Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.
"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta n