dan Kaya ne".
Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.
Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa.
Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan.
Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini".
"Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa".
"Muje Zan baka kudin drop din".
Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai"
Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi.
Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?"
Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare".
"Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka".
Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin".
Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa".
***********
Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da adudu biyu.
Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share hawaye.
Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?"
"Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba".
"Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota".
"To mommy". Ta fada sukayi waje su uku.
Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi".
Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane".
"Ungo Nan".
Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu.
Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa.
Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa.
A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko.
"Gani mommy lafiya na ganku haka?".
Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta".
Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?"
"Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka".
"Ok, Bari naje Nan Ina zuwa"
Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?.
Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema.
Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane"
Jiki ba kwari ya koma ciki..
***** ***** *****
Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".
Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.
"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"
"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".
"Allah sarki ko kawu Musa?"
"Shine Ashe kin sanshi".
Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"..
"Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai h