ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 125 of 136

ake son fada min Kuma? naji komai me Za'ayi bazan zauna a garin Nan ba wallahi, gida Zan tafi kuma idan ma ciwon ne ai Ina da inda za'ayi min maganin ba sai Nan ba, da gata na da komai na zauna sai watangaririya nake yi Dani".AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 41. ๐Ÿ“–๐Ÿ–‹๏ธ ________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala. Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi". Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" . Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala. Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" . Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya. Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa". Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna". Ta taso tana karbar tabarmin. "Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki". Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi". "Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita". Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar. A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki. Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?. Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah". Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita. "Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi". Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron. "Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa" 'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi". "Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiรงi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba". Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba. Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata". "Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida". Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata". Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata. "Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi". "Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba" Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi i
๐Ÿ