ukayya sun daga Mata hankalin kenan da wata jikakkiya a tsakanin wannan likitar da Mahmud.
Wallahi ko likitoci sun Kare wannan ba zata Kara dubata ba shi yasa Kennan jiya ta damu da sanin waye mijinta da dangartakar ta da Mahmud.
Tunda Sameer ya yiwa Rukayya buyagi Bata kara magana ba har sukazo junction din gidan shatima. "Wai yaushe mommy taje gidan Hajyr makwararin?".
"Dazu da safe na kaita Wai zasu karbi lefen mujahida".
"Ok Allah ya Sanya Alkhairi. Dan Allah ya Sameer Zan sayi alawar Madara idan ka tsallaka Zan kaiwa Hajiyar makwarari".
"Kice dai Zaki saya bawai Zaki sayawa Hajiyar makwararin ba".
"Allah tana son shi sosai"
A kofar gidan Hajiyar yayi parking Babar mommy ce.
Da karadi Rukayya ta shigo gida yayin da Zahra da Sameerke biye da ita a baya, suna runfa ana hira da kunnen Rukayya da 'ya'yan dangi da mommy masu karbar lefen basu Fara zuwa ba gaishe dasu yaran sukayi suka fice, sukabar mommy kawai. Cikin nuna kulawar mommy ta kalli Rukayya dake gaba. "Ba dai har kun gama da asibitin ba?"
" Mun Gama kin ganta Nan Wai doctor Haseena tace zata yankata tayi Mata tiyata Dan nace ban yarda da ita ba shine ya Sameer yake ganin bekena".
Sallama Zahra tayi tana Dan tsugunnawa tana gaishe da mommy cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa da Kuma alamun tasha kuka.
Mommy kallonta tayi tana fadin "Masha Allah tabarakalla sannu ya jikin naki?"
Da sauki sosai".
To Allah ya Kara lafiya naji Rukayyar na fadin tiyata za'ayi Miki".
"Eh haka suka fada"
Hajiyar makwararin ce ta fito tana fadin "wa nakeji kamar Rakiya a gidan nan waye ba lafiya naji ana magana tiyata".
" Kin ganta Hajiya, matar Mahmud mutumin ki ce".
Mommy ta nuna zahra.
" Wai Amaryar ce? Sannu kinji menene ya sameki?"
Rukayya ce ta fada Mata.
Mommy ta kalla "Ni Zan hada Mata maganin wannan lalurar ba sai anyi Mata aiki ba, ki huta Rukayya ki shiga Nan kurmi ki sawo min abin hada maganin a Nan na hada Mata insha Allah sai dai ya narke yabi jinin al'ada.
"Amma gaskiya ba wanda ze yanka ta Kamar kabewa ku 'ya'yan zamani komai a yanka ta haka ne daji yake shiga ai ta fama da rai idan yazo da karar kwana kiga an mutu, daina kuka, samiru kiwawo min mijin nata na fada Masa da bakina Babu me yi Mata danyan aiki ko haihuwar fari Bata yi ba a jawo mata tsuguniya mazan yanzu marasa hakuri".
Ta fada tana nufar uwar dakanta.
Ita dai mommy Shiru tayi Saida Hajiyar ta shige sannan ta dubi Rukayya "Wai Ke Sai yaushe hankali ze Gama Miki jiki? Kinzo kin kwatsa zance gashi Nan kin tubzura Hajiya Mai hanata hada maganin Nan sai Allah, itama Kuma Mai lalurar maimakon ki kwantar mata da hankalinta A'a tashin farko kin sokawa zancen wuka, ai kin kyauta".
"Wallahi ba haka bane mommy Kinga dai muna good term da Haseena amma wallahi yau kamar ma Bata taba gani na ba sai cin magani take yiwa mutane da dacin rai want ya Hana Ya Mahmud din ya aureta taga yarinya ta gigice zatayi mata illa haka kawai".
Maficin dake kusa da ita Mommy ta jefawa Rukayya tana fadin fita ki bani guri tunda kin Zama babbar kwabo kin tasa yarinya gaba kina fadar abinda be Dace ba".
Wata uwar harara Sameer ya saukewa Ruky ji yake kamar yayi Mata duka duk ta cakude lamarin tana kokarin ta saka jinin yarinyar mutane ya hau, tun sassafe Mahmud ya Kira shi Yana fada Masa ya kira Rukayya yace ta fadawa Zahra ta bude wayarta ya manta shaf sai fa yanzu ya tuna.
Wayarsa ce ta Fara ringing "shine ya kira" ya fadawa mommy.
"Ka dauka kayi Masa bayanin halin da ake ciki".
"Nasan Haseena ce ta fada Masa shine ya Kira yaji".
Wayar ya saka a speaker yanda zahrar ma zataji.
Bai jira komai ba ya Fara fadin "Sameer wace magana naji Haseena tana fada min? kada ka Bari su taba min yarinyar nan Zan kaita inda ya Dace, naji tana fada min wasu nonsense wallahi idan na shigo saina Bata Mata rai, ita harta isa ta fada min son ranta who is she? Yanzu ina ita zahran take? Tun jiya jikina ya bani an samu problem wayar ta fa ta rufe ta Hana nayi magana da ita fa".
Tashi Sameer yayi tsam ya fita ya cire wayar daga speaker saboda kada yayi katobara.
"Gamu Nan a makwarari gidan Hajiya Zahrar sai kuka takeyi,ita Kuma Ruky sai tinzira ta take kada ta Bari a yankata har Hajiyar makwarari taji tayi tsallen Albarka tace bata san wannan magana ba, ita zata hada Mata maganin hausa Wanda ze narke ciwon, wallahi sun caza min kai har na rasa yanda zanyi da rigimar Hajiyar, yanzu haka kasuwar kurmi zata aiki Rukayya ta sawo Mata mahadin maganin da zata hadawa zahrar".
"Yanzu dai bazan Gane kome kake fada ba hadani da Zahrar muyi magana"
"Ok Bari na kira ta dakin mujahida Naga ba kowa a ciki ka kwantar Mata da hankali duk ta shiga damuwa sosai sai kuka takeyi"
Rukayya dake zaune a tsakar gida ya yiwa nuni data Kira Zahra, lokacin da suka fito Yana tsaye suna ciga da maganar.
Wayar ya Miko Mata ya nuna Mata dakin mujahida yayi nufi waje.
Tana shiga cikin dakin tana Jinsa Yana faman hello, hello tayi shiru karshe ma ta sakata wayar a flight mood tayi kwanciyarta a katifar mujahadar tana goge hawaye.
"Me k