NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 123 of 136

ta tana mamakin gidan Wai wane irin gida ne wannan gari guda compartment guda kawai ya hada irin wadannan mahaukatan falukan da bedrooms din Nan to yaya sauran parts din suke?. Dakin dake hannun hagu ta nufa ta bude, daga inda Zahra take ta hango wani Royal bed milk Mai azabar kyau, Bata Kara gaskata maganar zilan ba Saida ta shiga ciki, a gefen bed din Zahra ta zauna tana fadin "Bari na Dana gadon Aunty zilai". Dariya sukayi su suka "kin gani ko wallahi nifa a jiya da kyar nayi barci duk zulumi ya isheni ji nayi Ina tsoron gidan yayi girma da yawa, na jinjinawa matar gidan". "Wai Mai gidan Bai taba aure ba a gaba dai ze kawo matar". Baki zilai ta Kama tana fadin "to shi wane irin kudi ke gareshi da ze Gina irin wannan gidan Yana saurayinsa". "Bani wayar Aunty zilai wannan hirar ba karewa zatayi ba kada lokaci ya kure yau daga Asibitin cikin gari zamu gidan su oga Sameer na gaishe da mommy". Wayar ta Bata suka fito tare ta Kira Ammah suka gaisa sun jima tana fada Mata abubuwan da akayi mata jiya da Kuma komawar da zasuyi yau, karfafa Mata gwiwa itama Ammar tayi tana fada mata ta kwantar da hankalinta In Sha Allah ba komai. Lokacin da suka fito har Iya Rahane ta shirya table din Rukayya ma ta fito. Kallon su Rukayyar takeyi ganin daga bangaren da suka fito. "Aunty Rukayya Ina kwana?" Zahra ta fada. ",Lafiya kalau matar big bro, ya Naga kin fito daga bangaren mu". "Au kema a can Kika zauna kika ki zama a dayan dakin kusa Dani". Baki ta bade tana kallon Zahra. "Na shiga dakin Mai gidan na zauna tab ai wannan part din sai ku". "Mu suwa daga zuwa bakunta sai mu zaqe Ina laifin can din wallahi transfer zanyi, Ina dalili Ni kadai kamar mayya kufa Nan ku uku ko ihun neman taimako kayi an taimaka maka amman Ni kuwa ko kasheni za'ayi sai dai a dauki gawar da safe". "Tab wallahi ba inda Zaki zauna a Nan ba haka big bro yace ba,a can yace ki zauna Dan haka Babu Mai canza wannan Umarnin". Dan turo Baki tayi "Ni na taba ganin haka mutum ya ringa saka doka a gidan mutane inaga baisan girman gidan ba shi yasa yake bada wannan Umarnin, gaskiya da sake". Time Rukayya ta duba a waya kizo muyi break yanzu zakiga ya Sameer yazo tunda da wuri za'ayi Miki sauran gwajin". Suna cikin break din Sameer yazo Saida ya jira a mota suka Gama sannan suka tafi, a ANC department suka samu doctor Haseenar sun awon ciki. Ba yabo ba fallasa ta tarbesu ba kamar jiya ba ko yanda suka ringa Yi jiya da Rukayya yau ba haka bane daga gaisawa Bata Kara cewa komai ba, itama Zahra saita Kama kanta Rukayyar ma haka. Gwajin jini ta Kara tura Zahrar ta hadasu da wata ma'aikaciyar su ta rakasu main lab aka dauki jinin. Lokacin da suka dawo sun Gama ante-natal din gwajin jira ta dauko da scanning din ta Kira Sameer tana fadin mu hadu a office dina". Ta kashe tana fadin Bismillah Ruky muje office dina tunda mun Gama da Ante-natal sai zuwa anjima zamu Fara gyne". A kofar office din suka samu Sameer din ya rigasu zuwa. Sai da suka zauna sannan suka gaisa da Sameer din, bayani ta farayi Masa na gwaje-gwajen jinin jiya "a cikin jininta ba wata cuta ko kadan kawai scanning ne ya nuna Mana akwai matsala a mahaifarta ta fibroid amman be wani girma sosai ba za'ayi aiki a cire mata tun kafin ya girma Amma zamuyi admitting dinta zuwa one week tana karbar magani kafin ayi surgery din, Dan haka sai ta Kira mijinta ta fada masa yazo da mutane muna son jini leda biyu, zamu jira results din Nan ya fito total blood count za'ayi Mata". Rukayya ce tayi farat ta tambayi doctor Haseenar "yanzu dole sai tiyata baza'a iya Shan magani ba a warke?" Kallon tsab Dr Haseenar tayi Mata kafin tace "hanya mafi saukin rabuwa dashi ta sai dai aikin gaskiya". Tunda doctor Haseena ta Fara bayani gaban Zahra ya yanke ya Fadi idan da abinda taki jini a rayuwar duniyar Nan to tiyata ce. Nisawa Sameer yayi kafin ya samu karfin halin fadin. "Thank you so much doctor kome kenan zakiji idan munyi communicating da mijinta saina kiraki later" "Ok.ba damuwa Allah ya sauwaqe". "Amin". Rukayya ta fada Dan zahra ba bakin magana har suka shiga mota tana cikin tashin hankali, kuka takeyi irin na zuci din Nan sai dai hawaye kamar an bude famfo. Saida suka fita daga Asibitin har sun shiga court road sannan Sameer ya Dan juyo, Madam kiyi hakuri in Sha Allah ba wata matsala idan Allah yasa yin surgery din ne yafi Alkhairi ayi kawai Kinga kema saiki huta da zulumin ciwo duk wata". Rukayya ce juyo tana fadin "gaskiya kada ki yarda a yanka ki haka kawai Ni banma yarda da maganar Haseena ba, kawai ta jawo Miki wahala Ni Daman da anyi shawara Dani da Babu abinda zesa Haseena ta duba matar big bro haka kawai taje ta jawo Mata matsala da gangan bakaga yau sai wani share mutane takeyi ba, wani ya Hana big bro din ya aure ta". Wata uwar harara Sameer ya zubawa Rukayya "Billahillazi Zan saukeki a Nan ke wace irin mutumce da bakinki bashi da controlto me kikayi ke Nan? wannan ai shashanci ne keda Zaki kwantar Mata da hankalinta shine Kika sokawa zancen wuqa". Ita dai Zahra maganganun R
🏠