NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 120 of 136

ji da ze ganta Bai Kara kallonta ba. Kasa hakuri Rukayyar tayi Saida ta magantu. "Allah yasa kiyi ta haifowa big bro Yara masu Kama dake gaskiya Ya Mahmud ya Dace ai shi wallahi gaba ta kaishi gara da aka samu wannan incidence din da Bai faru ba yaushe ze gano Mana ke". Ita dai zahra murmushi kawai takeyi, amma Kasan zuciyar ta tambayoyi ne fal, Ta Ina Mahmud ya zama big bro din Rukayya da alama akwai wata dangantaka Mai karfi a tsakanin Sameer dashi bawai aikin NGOs din Nan bane gaskiya. A haka suka fito main parlour suka tarar da Iya Rahane da zilai suna kallon Arewa 24 suna program din mata a yau. "Masha Allah, Allah ya kade mugunji da mugun gani". Iya Rahane ta fada tana kallon Zahra. "Allahumma Amin. Allah ya tsare uwar dakina ya Baki lafiya yasa a dace". Zalai ma ta fada, Rukayya tace "Allahumma Amin, sai mun dawo". Suka nufi hanyar fita, a cikin mota suka iske Sameer, gaba Rukayyar ta shiga ita kuma zahra ta shiga back seat. Basuyi wata tafiya Mai nisa ba suka shiga cikin Asibitin, bayan sun fito daga motar number Dr. Haseenar Sameer ya Kira, saiga wata sub-staff da wayar a hannunta tana fadin "sunnunku da zuwa doctor tace na tafi daku office dinta tana zuwa suna wani aiki ne" "Ok mun gode". Rukayya ta fada. Har cikin office din ta kaisu ta fita Nan Sameer yabar su yace zeje yaga wani friend dinsa Dr. Sulaiman. Bai jima da fita ba aka turo kofar su duka suka juya suna kallon Mai shigowa macece wankan tarwada Mai matsakaicin tsawo fuskarta doguwa ce da maidadaicin idanu da hanci tana sanye da doguwar Rigar material coffee Mai haske tayi rolling da milk din veil fuskarta fal fara'a ta shigo tana fadin " wa nake gani kamar Rukayya a office dina rabon daki tako Nan harna manta Sai dai a waya". Dariya Rukayyar tayi tana fadin "Ina laifin Kiran wayar ma Shima zumunci ne yafi ace ba'ayin ko daya". Direct gurin da suke zaune ta nufa " Kinga kin dauke min hankali Ina ta zuba ban yiwa bakuwa ta sannu da zuwa ba, sorry na barku a zaune ta fada tana kallon zahra" "Lah haba doctor ba komai yanayin aikinku ne hakan". Zama tayi kusa da Rukayya tana maida hankalinta akan Zahra. Patient din dangen ce?" Ta jefawa Rukayya tambayar, da alamun mamaki a fuskar ta. Kai Rukayyar ta gyada mata. "Anyway Bismillah ta fada tana tashi daga gurin ta nufi table dinta. Zahrar ta Mike tabi bayanta. Tambayoyi sosai ta rinqa yiwa zahrar wasu har kunya take kamata ta kasa Bata amsa, tambayar data fi Bata mamaki shine inda take tambayar ta meye tsakanin ta da Mahmud Dange?" Kafin zahrar tayi magana Rukayya ta rigata "sister din abokinsa ce daga Bauchi, kuma matar aure ce Dan naji Baki tambqyeta ba, ita Kuma Bata fada Miki ba". Wata ajiyar zuciya ce ta kubcewa Dr Haseenar har Saida Zahra ta kalleta. "Ai ban sani ba Ruky Naga DANGEN yayi matukar damuwa ne ko yanzu kafin na shigo saida ya kirani yana fada min Kuna Nan Kuna jirana na dubata sosai". Dan smile zahra tayi kawai ita Kuma Rukayya tace "kinsan halinsa baya Wasa da rashin lafiya komai kankantar ta, kinsan suna China Aunty Fateeha ta haihu sending Ya Sameer yayo Nigeria shi ya wuce Dubai". Dan murmushin itama Dr din tayi "zeyi abinda yafi haka in dai Dange ne yanda ya damu Zaki dauka matarsa ce wallahi duk yafa rikice kamar ba dangen da Mata ke fada a kansa ba ko kallo basu isheshi ba Sanda muna school a UK da yawa mutane sunyi mamakin yanda muka Dade dashi ba wani matsalar data faru fatana ya dawo su hadu da Daddy ayi a wuce gurin kawai, kinsan halinsa tunda aka samu matsala Nima fa ta shafeni tunda lokacin da abun ya faru munje gida sokoto shiya Hana ayi abinda za'ayi ta fice yabar kasar Kinga Banda case din Nan ta sister din friend nan tashi Bai Kara kirana ba wlh na tura Masa sako ta email dinsa Amma ba reply". Ita dai zahra ba baka sai kunne wata magana sukeyi wadda ta jefata a kogin tunani akan Mahmud abinda kunnen ta keji daban abinda yake nuna mata daban. "Hum lamarin big bro sai a hankali kin sanshi da zuciya kafin dai yayi fushin ana dadewa Amma idan yayi jam'i yakeyi gurin yanke hukunci sai hakuri komai ze Zama normal". Rukayyar ta fada. Forms ta cikewa Zahra ta test-test Wanda za'ayi Mata ta Mike ta fito daga mazauninta tana fadin kuzo muje ayi wannan testses din Sai Kuma muje ayi scanning mu gani akwai abinda nake tunanin yana kawo matsalar Amma bazamu tambbatar ba sai mun duba. "To Allah yasa a Dace" Rukayya ta fada. Sai da suka Fara zuwa lab sannan suka nufi radiology department inda za'ayi hoton cikin. Dr karima ce tayi mata scanning din tambayoyi ta Riga yiwa Zahrar harta gama. Basu jira karbar result din ba, da safe doctor Haseena zata shiga dasu can Asibitin malam Aminu inda za'a mata saura gwaje-gwajen Nan sun Dan rage ne saboda cunkoson can din. Har gurin mota doctor ta rakasu suna 'yar tsama da Sameer, sannan sukayi sallama Sameer na Mata godiya saboda taki yarda ya biya ko sisi tace patient din DANGE nata ne, itama Zahrar godiya tayi Mata Rukayyar ma haka. Har Sameer yayi ribas doctor Haseena ta daga Masa hannu alamu
🏠