NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 12 of 136

ana fadin "Ashe Kuna Nan ai tare muke da Ya Abdul Hakeem ma". "Ok" abinda Mahmud ya fad'a kenan Shi Kuma Magajin ya karasa gurin Auntyn Yana gaishe ta. Abdul Hakeem ne ya shigo Yana rike da wayarsa a hannu da sauri ya karasa gurinsu Mahmud din Yana fadin "A'a angon ne da kansa" Yana Mika masa hannu. Saroro Aunty Hasana tayi ita wace iri ce kawai dai taga sun shigo sun gaisa wallahi Sam Bata kawo ba ita da akace Mata Alamajirin Baba malam ne ai ta dauka irin wannan gaddawan ne, yo ta Ina wadannan sukayi wani Kama da kolaye ai ita zallar ilimi ta gano da wayewa a tattare dasu. Hanyar wajen ta nufa tana janye da hannun magaji duk sai taji kunya ta kamata Ashe sukanta ne. Ita kuwa Mai gayya Mai aikin ai tana jin an ambaci ango ta bude idonta girjinta Yana wata irin dokawa "ango a nan to waye a tsakaninsu da suka shigo tare? Abdul Hakeem ne ya kalli gurin gadon Yana fadi. "Masha Allah! Ashe kin tashi, ya jikin?" Ya fad'a Yana karasawa jikin garon Sameer ma Dan matsawa yayi Yana dubata Kai kawai ta gyada musu, tana kallon Ya Abdul Hakeem din, kallo irin na neman Karin bayani. Yi yayi kamar Bai Gane ba ya juya yana yiwa Sameer magana suka fita. Har suka fice Bai dago ba Yana ta faman tab'a waya sai da ya Mula Dan kan shi sannan ya tashi ya tunkari gadon. "Ya jikin?" Ya fad'a Kai tsaye, Bai Kuma jira ta amsa ba Dan ko kwakwkwaran motsi ta kasa sai tunanin da yake Mata Kai komo. "Badai wannan bane ake nufin an daura min auren dashi Amman da Naga ta kaina". Shine ya katse tunaninta. "Ki kwantar da hankalinki ki daina saka damuwa a ranki da kannan shekarunki, ki kuma dagawa Ammah í nata hankalin, idan nine bakya so ba damuwa Nima kusan hakan take. Amma kada mu watsawa iyayen mu kasa a ido Mana tun yanzu gara ki nutsu ki kwantar da hankalinki daga baya sai a duba Mai yuwuwa tunda nasan bazaki so Zama da almajiri marar karatun boko mai zurfi, ga karqncin wayewa ga rashin madafa ta yau da kullum, Nima kasada ce tasa na yarda da tayin da akayi min tunda Naga nema ake a tozarta min da iyayen a kunyata su a idon duniya aci mutuncin su". Ita da'i ko motsin kirki ta kasa da gaske gani take duk ya cika dakin, ga wani fitinan kamshinsa duk ya cika Mata hanci. A bazato taji ya Dan shafi gefen fuskarta idan ba kunnenta ne suka jiyo Mata ba da'i dai ba sai taji kamar yace "my previous" a hankali sannan ya Mike Yana fadin "Bari a kawo maganin ki saimu wuce gida tunda doctor yace zamu iya wucewa, Amman yace ki rage yawan tunani Yana haddasa cututtuka". Har dakin Amma Abdul Hakeem ya raka Zahra lokacin duk yawancin bakin sun tafi sai 'yan uwan Amma na Mubi Dana Jimeta sai Kuma Aunty Hasana da take dakon dawowar su, ai tunda magaji ya Kara Kora Mata bayani akan Mahmud ta tafi daga asibitin tunda Mai dungurungum din yazo ita bataga ta Zama ba. Saida ta matsawa Zahrar tayi wanka Tasha tea da magungunan ta kwanta sannan tayi haramar wucewa gida. Sai wurin karfe Tara sannan Hajiya mama ta shigo dakin tana fadin "wallahi daga idar da sallar ta barci ya dakeni sai Dana tashi zilai Mai wanke wanke take fad'a min an dawo da Zahra har sun shigo sun duba ta". "Wallahi kuwa ai jiki da sauki yanzu Tasha magani ta kwanta" "To Allah ya Kara lfy, Wai Hajiya wanene mijin yarinyar Nan ne naji ana fadar Wai cikin Almajiran baba Malam ne, shine nace haba yaushe Alhaji zeyi wannan danyen aikin ya rasa bazai bawa aure Sai a cikin Almajirai". Inna maimuna ce tace "ai mu Hajiya ko waye Alhaji Jafar ya aurawa Fatima wallahi mun karba da hannu biyu mun gode tunda mun San har abada Babu cutarwa a tsakanin Asama'u da dashi da ita Fatiman da abinda ya Haifa bamu taba ganin banbanci ba, Dan haka mun karba da kyakykyawan niyyarsa Allah ta tabbatar Mana da Alkhairi". Gaba daya suka amas "Amin" Hajiya mamar ta Dan jima a dakin kafin ta koma dakinta. Bayan Zahra tayi sallar Asuba ta gama Azkar dinta komawa tayi ta kwanta har lokacin kanta Yana Mata ciwo kadan kadan, sai gurin takwas da rabi Inna maimuna ta tasheta tana fad'a Mata tayi maza ta kimtsa Abbansu Yana nemanta. A gurguje tayi wankan ta fito lokacin an kawo Mata kunun gyada da fanke, kunun gyadar kawai tadan Sha kadan ta shafa lotion dinta ta saka doguwar rigar atamfa ko dankwalin Bata daura ba ta fito cikin takunta na nutsuwa Wanda da yawa mutane ke gani a matsayin yanga da jiji da Kai. A tsakar gidan suka rinka gaisawa da tsirarun yan uwansu na Mubi da sauran ma'aikatan gidan Mata. Da sallama a bakinta ta shiga falon Abban nasu, tayi mamakin ganin kusan duk 'ya'yan Abban suna Nan sai su Ammah da Inna maimuna da kanwar Abban Maman lafia. "Zo nan kusa dani Uwata". Abban ya fad'a Yana murmushi, itama murmushin tayi ta karasa kusa dashi ta zauna nata fadar "Abbana Ina kwana?". "Lafiya kalau Alhamdulillahi Uwata". Sannan ta juya tana gaishe da jama'ar gurin. Said Kuma dakin yayi shiru. Abban ne yacewa Imam "Mai sunan Malam ayi Mana addu'a". Ya jima Yana addu'a sanan aka shafa. Sannan Abban ya Dora da cewa. "Alhamdulillahi ala kulli halin, dole ne mu go
🏠