NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 118 of 136

ari kawai bazance naji ba Naga iya gudun ruwan ya Sameer sai wani cewa yake kanwar abokinsa ce". Ita da zahra Dan murmushi take tunda ba gane Kan zancen tayi ba. Abinci ne yakai kala biyar Rukayya ce ta bubbude wa zahra tana fadin "Auntyn mu ki zabi Wanda kike so a zuba miki". "Kaji Aunty ni basai kin zuba min ba haba dadin sai yayi min yawa hakan ma na gode, ina Aunty zilai tazo muyi lunch din". "A'a nan naki ne ke kadai na Kai Mata nata dakin ta tun dazu". ******** Knocking din kofar akeyi a tana zaune ta Sha uban gayu kamar wadda zata wuri dinner ta biki sai kanshi ke fita a jikinta Mai Dadi tana rike da wayar ta tana addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba. Umarnin shigowa ta bayar tana kallon kofar, Basira ce yarinyar dake aikin shara da goge-goge a bangaren ta, tsugunnawa tayi tana fadin "barka da Asuba Ammi". "Barka kadai Basira har kin fito da wuri haka, lafiya dai ko?" "Lafiya kalau Ammi Daman Hajiya Inna ce tazo ita da Abie". Littafin ta aje akan bed side tana fadin "Hajiya Inna kuma"?" Kai Basira ta gyada alamar eh. "Kije gani Nan fitowa in Sha Allah". Ta nufi clothset dinta ta dauko gyale mahadin shaddar ta fito daga bedroom din. A hankali take saukowa daga stairs din shar da ita tun kafin ta karasa saukowa kamshinta yayi musu sallama, cikin takunta na nutsatstsiyar mace Mai aji da yarda da kanta ta da tarin ilimi Hadi da wayewa, sallama tayi musu tana nufar gurin Hajiya Inna ko inda general yake Bata kalla ba. Kusa da Hajiyar ta zauna lokacin da take amsa sallamar tata. "Ina kwana Hajiya". Cikin nuna kauna da kulawa Hajiyar ta amsa tana tambayar ta Ina su uratu Ammin tace Basu tashi ba tunda yau ba zuwa school. Ammin ta Dan juya bata yarda sun hada Ido dashi ba tace Masa. "Barka da Asuba". Shiru yayi Mata kamar beji abinda ta fada ba, itama Bata kara bi takansa ba, Hajiyar na ankare dasu. Ammin ce tace "Hajiya me yasa Kika fito yanzu da sassafe idan kina son ganina basai ki turo nazo ba basai kin taso da kanki ba Dan Allah kiyi min wannan alfarmar kada wani Abu ya taso nason ganina ki taso ki taho saboda ni". "To in Sha Allah hakan baze Kara fatuwa ba nima ba zuwan kaina bane jiya Muhammadu ya sameni da dare yake fada min wata maganar da banji dadin ta ba, shin da gaske ne bakije inda yake ba tunda Kika dawo? Idan ya Kira wayarki bakya dauka, yazo da kansa yafi sau biyar kin rufe kofa?". Shiru Ammi tayi shi Kuma general kamar ya rungumeta a gaban Hajiyar haka yakeji Dan gani yayi ta wani Kara yin fresh da ita bazaka taba cewa ita ta haifi wadannan yaran ba, ta koma masa danya sharab da ita ga uwa uba ko runhu ka rike Kan sakko bazaka taba ganinta a hargitse ba ta San kanta sosai yanda ya kamata, da kyar ya iya saita kansa a gaban Hajiyar. "Kinyi Shiru zainab kenan abinda ya fada gaskiya ne?" Sadda Kai ta Karayi kasa sai Jin shashshekar ta sukayi. "Subahaballahi haba zainab ko lokacin da lamuran suka jagule Baki zubar da hawaye ba sai yanzu, kiyi hakuri na fada Miki duk Wanda za'ace yayi hakuri to an zalunce shi ki yafewa mijinki wallahi rashin samun kulawar ki tasa ya runtse ido ya iya fada min abinda Bai kamata na sani ba, na roqi arziki ki dubi girman Allah da manzonsa ki rungumi mijinki da 'ya'yan ki kiyi boyayyiyar aure yanda Kika saba". Sai da tayi kukanta Mai isarta sannan ta share hawayen ta sai lokacin taji wani gululo ya fice daga kirjinta. "In Sha Allah ya wuce Hajiya har abada ki tayani bashi hakuri hakan baze qara faruwa ba". Dan karamin tsaki Hajiyar tayi "Babu hakurin da za'a bashi, shida ya shuka rashin kirki, kece dai da hakurin ai cewa nayi bana zuwa shi daya Bata yaje ya gyara kayansa tunda Allah yasa kikazo gidan Nan Baki taba kawo min qararsa ba sai shine gemai gemai dashi ze dauko jiki ya kawo korafi ashe Babu dadi king... Dan gyaran murya yayi "Hajiya kiyi Shiru komai ai ya wuce basai kince komai ba, tunda dai nayi abinda takeso ai shike Nan kowa ya ganni a Nan da ranar Allah na taso tsohuwa ta gaba ta min biko". Ammi dai Shiru tayi Bata tanka ba sai Hajiya Inna ce tayi dan murmushin su na manya Wanda suka San jiya suke ganin yau. Ammi duk sai taji wata kunya ta lullubeta, wani lokacin maza kunyarsu kadan ce wallahi duk girmansu idan sukayi wani abun sai kaji kamar kananun yara, kome ya fadawa Hajiya ya taso ta da wannan safiyar?. "To shike nan sai ka bamu guri ko tunda Allah yasa taga girmana ta yafe". "To shike nan yaushe Zaki koma gida?". Kafin Hajiyar tayi magana Ammi ta rigata. "A Nan zata wuni da magari ba za'a maidata gida". ",To kaji sai ka tafi naka uzurin tunda 'yata ta yanke hukunci". Baice komai ba ya nufi part dinsa da yake bangaren ta, harya danyi nisa ya juyo Yana kallonta ido cikin Ido da wani yanayi a tattare dashi. "Kuyi breakfast Dani a kawo min ciki". Kai ta gyada masa ya wuce ciki. Yi Hajiya Ina tayi kamar bataji me yake fada ba ta cewa Ammi. "Muje ki bude min dakin ko lazimi ban Gama ba yaje ya daukoni Dana ce yaje za'a kawoni ma cewa yayi A'a". Ita dai Ammi ba baka sai kunne tare suka sh
🏠