Dan haka ta Dan zamo kadan tana janyo luggage dinta tana fito da abinda ke ciki,wanka take sonyi duk jinta take a takure indai tana period sai a hankali sam Bata da sakewa ko misqalazarratin, Banda dole Babu abinda ze sakata barin gida a irin wannan condition din.
Luggage dinta ta janyo a hankali ta Fara fito da abinda ke ciki, na Kan mirror ta Fara diba ta nufi inda yake lokacin data karasa ba karamin mamaki tayi ba ganin irin kayan shafar da take amfani dasu har da wasu daga cikin irin turarukanta ta gani Banda su freshner na fesawa.
Bata fasa aje na hannunta ba, gurin kayan ta dawo ta bude cloth set din data gani tana budewa tayi arba da kayan Mata Babu abinda Babu, harsu shoes da bags, dasu inner wears.
Mayarwa tayi ta rufe ta dawo da kayan a hannu ta mayar inda ta dauko su.
Wanka ta shiga Nan ma wata duniya ce aka hada, ta jima tana gasa jikinta Dan idan Tana irin wannan condition din Bata kaunar abinda ze hadata da ruwan sanyi ko kadan.
Bata wani Bata lokaci ba gurin shiryawar ta saka doguwar Rigar atamfa glitter purple, Rigar tayi Mata das a jiki mayafi light brown ta saka touching din jikin atamfar sai takalma suma light brown din plat, haka nan taji tana son saka turarensa Mai sanyin kamshin Nan dauka tayi ta fesa ta nufi hanyar ficewa daga dakin.
Saida ta fito yanzu ta karewa wannan parlourn kallo yafi duk Wanda ta gani a baya tsaruwa kunjerun dake ciki ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba Bata taba ganin irinsu ba duk kuwa da gidajen Alfarma data shiga ta bangaren Ummee.
A hankali ta ratsa ta wuce tabi hanyar da suka biyo suka shigo.
Ba kowa a parlourn lokacin data shiga sai dai tana jiyo Dan Karan plates haka kamar ana wanke-wanke.
Zama tayi taga ta inda wani ze gitta tunda ita dai ba sanin Kan gidan tayi ba. Wata Mata taga ta fito daga wajen dining ta wata kofa da manya food warmers a hannunta,ta aje a kan table din har zata juya ko jijinta ne ya Bata da mutum a gurin yasa ta juyo tana duban cikin parlourn, Ido suka hada da Zahra da sauri matar da gangaro daga steps din dining din tana fadin "Masha Allah, ko surukar tamu ce ta fito?".
Ta fada tana nufo Zahra dake zauna tana murmushi, itama iya Rahanen murmushi take har ta karaso gurin zahrar.
"Sannu Mama Ina yini"
Zahrar ta fada.
"Yauwa sannu yarinya ya kukazo?"
"Lafiya kalau Alhamdulillahi".
"To Masha Allah, sunana iya Rahane nice mommy ta turo na zauna dake kafin ki gama abinda ya kawoki".
Ta fada tana Dan tsugunnawa a gefen zahrar.
"To Mama na gode, Amma Dan Allah ki daina tsuguna mini kinyi jika Dani idan Ni ban Baki irin wannan girman ba to kema bai kamata ki bani ba, Dan Allah ki tashi"..
"A'a 'yata Allah ne ya Baki Dan na tsuguna Miki Babu laifi".
Kafin zahrar ta samu zarafin Mai da Mata amsa Rukayya ta fito daga inda iya Rahane ta fito ganinta da Zahra yasa Rukayyar ta karaso gurin su tana fadin "har kinyi me?"
"Harna fito Ina Zan iya Zama a wancan lungun Ni kadai kamar mayya ai Naga kokarin matar gidan nan data iya zama a cikinsa, Daman jiranki nake dakin da Kika rakani na matar gidan ne gara ki hadani da zilai mu zauna tunda duka kwana nawa zamuyi mu tafi kada a samu matsala kinsan halinmu Mata da zargi naje na manta wani Abu daya danganci namu na Mata a samu rashin yarda a tsakanin masu gidan Dan na bude cloth set Zan zaka kayana saina tarar da kayanta a ciki Kinga ai Bai kamata na shigar Mata dakin ba ya Zama Bata da sirri kenan".
"Wannan gaskiya ne ranki shi Dade kinyi tunani me kyau a kam".
Iya Rahane ta fada.
Zama Rukayyar tayi gefen zahrar tana fadin ai gidan Mai shi ko auren fari baiyi ba, kayan da kika gani duk nakine bana kowa bane Dan ya Sameer ya bani kudi nayo siyayyar jiya Dan a Nan na yini nida su suhaila Dan furnitures din dakin ma jiya aka sakasu Ina ga ba wata macen data taba zama a cikinsa Banda Mai gidan to kece ta biyu da Kika zauna, bama a dakin yace a sauke kiba dayan yace sai Yaya Sameer yace na Baki wannan ya wadatar kawai.
"Iya aje a fito da sauran abincin sai muje kiyi lunch din tun, shigarki ciki ya Sameer ke kirana Wai kinci abincin Baki da lafiya na tabbar kin Sha magani ni har mamakinsa nakeyi Bai dauki lamarinki da Wasa ba gaskiya".
Iya Rahane ce tace "Haba Rukayya yaushe Alhaji karami Zeyi wasa da lamarin iyalin Mahmud, Nima da Mommy ta kirani Saida ta Kira shi ta fada Masa nice zanzo ya amince kafin Nazo, ya jaddad min na kular Masa da ita yanda ya kamata, Kinga kuwa ai baiyi laifi ba ko?".
Kai kawai Rukayyar ta iya gyadawa mamakin duniyar Nan ya gama kasheta a zaune "matar Mahmud? Haba biri yayi Kama da mutum, tasan ba banza ba ya Sameer keta rawar kafa ya kasa tsaye ya kasa zaune akan lamarin, Kuma da alama itama yarinyar ninketa sukayi ta bai-bai Dan da alama batasan waye hakikanin mijin nata ba, gaskiya ta tayata murna dan ta zama Mai sa'a duk da shima Saida ya dauko diamond a cikin zinarai, Dan Daman wannan irin matansu ne.
Gurin dining din Rukayya tayi Mata jagora suka nufa tana fadin "kice min matar big bro ce Amma nayi mamaki gaskiya sun lullubeni Amma ki B