NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 116 of 136

rs, sai wani special kamshi daya hadu da sanyin A/C ya bada yanayi Mai dadi, sai plasma kusan bango guda. Zilai dai 'yar kauye sak ta koma ko Zama kasayi tayi sai da Rukayya ta juyo tace Mata Bismillah ki zauna Mana ku Sha ruwa". Ta fada tana yin gaba ta nufi wani steps gurin dining table ta shige wata kwana. Zahra zilai ta kalla "Wai Ina ne Nan din Kuma gidan na wanene nifa duk a rude nake na kasa samun nutsuwa ko kadan, irin wannan gidan ai sai sarki ko wani gagarimin Mai kudi". Da watsa hannu Zahra tayi. "Toni Ina nasan amsar tambayar taki, Nima duk daya muke dake bansan komai ba, nasan dai yace zamu zauna a Nasarawa GRA kawai ba wani Karin bayani da yayi min". Rukayyar ce ta shigo dauke da babban tray da robobin farmfresh dasu ruwa da Shani na gwangwani, sai fruit fresh ones. "Bismillah kusha ruwan sai muje ku huta sai kuci abinci". Sannu Zahra tayi Mata, itama zilan tayi mata, Sameer ne ya shigo da wani matashin saurayi da luggage din Zahra da 'yar madaidaiciyar jakar zilai a hannunsa ya gaishe su ya aje ya koma. Rukayya ce nufo inda Sameer din yake tana fadin "Ya Sameer Dan Allah ka jirani Zan bada sako gurin mommy ka taho min dashi" "Kefa Ruky kina da damuwa kiyi Abu Mai mahimmanci sai ki tsaya kina Wasa". "Allah Yaya da gaske nakeyi ka taimaka min". "Ok" Gurin su Zahra ya duba Yana fadin "sannunku madam kun sha hanya ki huta zuwa dare zamu fita Asibitin doctor tace mu hadu da ita a Nan Asibitin Nasarawa zataga patient yau a can da dare saita dubaki idan yaso sai mu hadu da safe a malam din". "To ba damuwa in Sha Allah Zan shirya da wuri nagode". Ya juya ya fice daga parlourn. Zahra tayi mamakin ganin favourite drinks dinta da aka kawo, more especially farm fresh Amma Bata kawo komai ba ta dauki abin arashi ne kawai. Bayan Sameer Rukayyar tabi suka fice daga parlourn. Saida suka sauka daga steps din gurin sannan Rukayyar ta dubi Sameer tana fadin "big bro Dan Allah wacece wannan din? Meye matsayinta a gurin Ya Mahmud nasan wlh ba banza ba yace a bude Mata wannan apartment din nasa". Tsaki Sameer yayi "na dauka want important Abu Zaki fada min Ashe tsabar gulma ce a cikinki, ba abinda yayi Miki zafi a lamarin yarinyar Nan yanda Kika ganta haka Nima na ganta bansan ko wacece dinsa ba tunda baiso in sani ba, Dan haka kada rawar kanki tasa ki fadawa Dr Haseena wani Abu Koda zata tambayeki kice Baki San komai ba". Tunda ya Fara magana Rukayya tayi zuru tana kallonsa yanda ya kiciccife yasa tayi masa alamar (?) Tasan there's something behind. Amma fadan dayafi karfinka sai ka mayar dashi Wasa. Dan jinjina Kai tayi tana fadin shake Nan Bari na koma kada suga an barsu su kadai". Ta juya ta koma Zuciyar ta fall da tambayoyin da Babu Mai Bata amsarsu. Lokacin da ta shigo sun gama suna Dan hira. Cikin bada uzuri Rukayyar tace "kuyi hakuri na barku ku kadai Bari na Fara rakaki naki masaukin kafin na dawo na rakaki Aunty ta fada tana kallon zulai". "Babu komai muje na shigar Mata da jakar kayanta. Rukayyar ce a gaba su Zahra suna bayanta, saida suka wuce parlour uku kowanne Yana wane na Bata zulai da abin harya daina Bata tsoro tunda taga abin bana karewa bane, wani corridor ta nufa suna biye da ita wasu steps suka gangara suka shiga, wani parlourn suka shiga Mai azabar kyau fiye Dana baya, kofofi biyu ne a cikin wani arc suna kallo juna, kofar hannun dama Rukayyar ta nufa saka Kati ta bude kofar tana tana fadin Bismillah". Tana murmushi. "Mu shiga Mana". Zahra ta fada. "A'a iyakata Nan, dakin na manya ne bani fa hurumin shiga ciki". Jin haka yasa zilai Jan burki, itama jagabar da tasan ciki da Bai na gidan tana fadin haka inaga ita 'yar karere. Aje luggage din tayi tana fadin. "A fito lafiya uwar dakina". Suka juya Rukayyar na fadin Bari muje sai kin fito. "Ok, nagode. Zahrar ta fada tana janye da luggage din ta murda handle din da siririyar sallama a bakinta. Bata iya karawa ba taja ta tsaya tana waro idanu waje na mamakin abinda idonta yayi arba dashi... AUREN HUCE HAUSHi. MAMAN FATEEMAH. Page 38. A hankali ta ringa tafiya kamar wadda ke tsoron kada a kamata, abinda ta gani ne ya Bata matukar mamaki wannan bed room din tamkar an dauko na can Azare na Mahmud an aje a Nan, hatta da curtains din windows din iri daya ne ba banbanci, Abu daya wannan yafi wancen shine girma wannan yafi balance akan wancan, Amma tamkar an dauko shi an aje, ita abin da farko tsoro ya bata hatta kamshin turarensa taji a dakin jiki ba kwari ta dosana ta zauna a gefen bed din tana Kara karewa dakin kallo tabbas a gizo idanunta ke Mata ba abinda ta gani haka yake, bata Kara tabbar da kamshin Mahmud takeji ba Saida ta zauna kamar lokacin ya saka ya fita daga dakin. Dan dam tayi Jin ta Fadi sunan Mahmud fatsal sai taji wani bambarakwai a bakinta duk sai wani irin Abu ya darsu a zuciyar ta. A shagwabe kamar tana magana da wani ta Fara fadin "to me ma zance masa ne? Kuma Wai Nan din dakin waye da suke kamanceceniya da nasa har kanshin ba banbanci?. Ba Mai Bata amsar tambayar
🏠