NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 115 of 136

nzu". Bai jira abinda zata fada ba ya kashe Kiran. Wani Kiran ne ya shigo masa, shima dai yana da alaqa da zuwan nasu duk dai zahrar naji tayi mamakin Yanda Sameer yake magana cikin ladabi irin haka to shida waye yake wayar Wanda ya jibinci lamarinta haka? Wata qila inda sukeyiwa aiki ne suka dauki nauyin zawa Asibitin nata, haka ta ringa sakawa da kwancewa, shi Kuma Sameer shiga can kurda can har suka shigo Nasarawa G.R.A sultan road. Tunda suka shigo Kano zilai ke baza idanu, Tana bawa idonta abinci, ita fa zilai duka zuwanta Kano baifi sau uku ba, Shima Ammah take yiwa rakiya idan wani uzurin ze kawota. Gidaje ne na garari take gani da ban mamaki yinsu ake kamar baza'a mutu a barsu ba, tana ganin gidajen da take mu'amala dasu sun Kai sun kawo Amma yanzu sai take ganin tamkar akurki ne kan wadan da take gani Bata gara sarewa ba Saida taga gidan da Sameer ya dosa, take hantar cikinta ta kada, innalilllahi takeyi a zuciyar ta, Nan da nan jibi ya Fara karyo Mata Daman tana mamakin gidan da zahrar ke ciki na can Azaren to kuma saiga wani, duk da Bata San mamallakinsa ba, wata Kila karar kwanace tasa ta biyo zahrar irin wannan gidan da sai ayi dambun Naman ka na waje baiji ba. Kofar wani mahaukacin gate ya tsaya yayi horn sau biyu aka bude suka shige. Ba zilan ba ita kanta Zahra ta sare da lamarin gidan Dan tasan yes Sameer masu kudi ne ko kungiyoyin su suna sakin kudaden aiki kamar ba gobe amma Bata taba tunanin ya mallaki irin wannan mahaukacin gidan ba. Dan da gani ba tambaya mamallakinsa yaci ya tada Kai. A kofar parlourn ginin da yafi ko wane tsaruwa da kyawun gani ya tsaya yana hamdala ga Allah s.w.a. Wata matashiyar buduruwa ce ta fito daga parlourn cikin rigar atamfa fitted tana takun yanga da gayu ta nufo motar tana fadin "sannunku da zuwa, Amma wallahi I am very surprised Dana ganka yanzu". "Rukayya Kenan kin dauka Ina Miki Wasa ne idan Kinga banyi driving ba nine bansa kaina ba". Dariya tayi "ai na yarda Kuma nasan wannan assignment ne me mahimmanci a gurinka". Fitowa yayi Yana fadin "yauwa sannunki da kokari, kuma haka ake tarar Baki a garin ku? kinzo kinata surutu kin tare Mata kofar fita". "Oh! Sorry" ta fada tana budewa Zahra kofa duk da Bata ganinta sosai saboda tintac glass ne a motar. Dan matsawa tayi ta bude Mata kofar, kanshin da yayi Mata sallama ne yaja hankalin Rukayya ta kalli kofar lokacin Zahra ta sako kafarta daya Kan fuskar zahrar idanun Rukayya suka sauka. "Kam bala'i" Rukayyar ta fada a zuciyar ta "wacece wannan din Kuma? Tun jiya lokacin da ya Sameer ya aiketa shopping na abubuwan amfanin gida da kayan Mata ready made take Masa kwawar ya fada Mata na waye? sai dai yace Mata wata ce Zaki ganta yarinya ce ko sa'ar ki Bata kai ba yayanta ne ya hada su ya kawota Asibiti, sai oga yace a sauketa a gidansa har su gama da asibitin. Rasa wane yare Rukayya zatayi Mata tayi saboda tasan wannan ko zo da hausa Bata sani ba duk da shigarta ta hausawa ce. Aunty zulai ce tayi magana lokacin data fito "haba yallabai Ina laifinta gashi ta fito ta tarbe mu". Dan murmushi zahra tayi lokacin data fito daga motar gaba daya ta kalli Rukayyar tana wani smile Mai daukar hankali tana fadin "sannu Aunty mun gode" ta fada tana mika Mata hannu, ba Karamin mamaki Rukayya tayi ba Jin zahrar na zazzaga tsantsar hausa bako gargada. Bangaren Sameer zahrar ta kalla tana fadin "Haba oga Ina laifin Aunty na ko wannan fitowar da tayi ai shima Yana cikin entertaining ne mun gode". Ta fada lokacin data rike hannun Rukayyar. Sai lokacin zilai ta Dan samu Peace of mind ganin Rukayya tasan dai da alama gidan bana macuta bane duk da ba tana zargin Sameer bane,yau din ce wata iri baka saurin amincewa da mutane. "Sannunku da hanya". Rukayyar ta fada tana kallon Zahra, yayin da Sameer ya shiga motar ya nufi parking lot ya ajeta. "Yau Aunty mun gode" Zulai kuwa sai kalle kalle take tana jinjina girman gidan Dan wasu gine - gine take hangowa na Alfarma ga shuke-shuke Nan sai wani sanyin kamshi ke tashi a gidan ko Ina Kuma tas ba alamar datti a cikin, dukiya dai Mai sunan dukiya an kasheta a gidan Nan. Ita tunda uwarta ta kawo ta duniya Bata taba shiga irinsa ba, sai yau da dalilin uwar dakinta Zahra ya kawo ta. Maganar Rukayya ce ta dawo da ita cikin hankalin ta. "Bismillah mu shiga daga ciki". Rukayyar ta fada tana nufar kofar parlourn numbers ta daddanna ta bude musu kofa ita dai zilai yau jinta take kamar ba cikin kasar take ba. Lokacin da suka shiga parlourn ba zilai ba kifin rijiya ita kanta zahrar sai da wani shock ya shigeta na wucin gadi, badan Zahra tana fita waje ba Kuma kakanninta masu dashi ne kuma tayi zaman syprus taga guraren hutawa da yawa da gidajen Alfarma da Babu abinda ze Hana ta zabga kauyanci, dan Babu karya naira tayi kuka a cikin parlourn Nan tamkar fadar sarauniyar ingila komai na ciki off-white ne da sirkin ash colour ba tarkace da yawa sai dai an kawata shi da wasu irin cutains masu azabar kyau dan shi kadai abin kallo ne, sai fremes masu kyau da tsari da wasu irin flowe
🏠