NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 113 of 136

a ta daina kallonsa sannan tace Masa. "Nifa each and every month sai nayi wannan ciwon". Ta fada tana Kara juyar da kai. Cikin damuwa yace. "Pls juyo muyi magana Ina son sanin yanda ciwon yake ne Zan fadawa wani doctor Kinga ai saina San komai kafin na fada Masa yanayin ciwon" Cikin Jin kunya da nauyinsa tace. "Nifa idan zanyi period ne nake yin ciwon cikin Baya sauki sai anyi min doclofenic injection yake denawa". "Ok, to idan period din yazo Kuma shike nan baya Kara ciwon?". Kai ta gyada masa. "Ki cire hijabin Naga yanda Kika rame tunda Nima daba ciwon nayi ba na rame lokaci daya dubi yanda nayi Rama? a lokaci aiki ma zanyi amma na kasa tabuka komai". Rufe bakinta tayi cikin mamaki tace. "Dan Allah ka daina haka ka manta a dakin Ammah fa nake idan ta shigo fa ta ganni a yanda nake me kake son na fada Mata?". "To ya za'ayi Kenan Ranar data ganki da ciki Kuma a jikinki tunda kina kunyar taga muna video call ba hijabi kamar Wanda ta aikata alfasha Allah idan na dawo dole asan abinyi na Fara gajiya gaskiya sai ragaita nake kamar marayan da bashi da uwa, alhalin Allah ya Gama min sutura, koba haka ba?". Shiru tayi Kamar ruwa ya cinyeta idan ta biye masa kunya ze Bata tunda taga alama Yana neman fitsare idanunsa. Jin tayi Shiru yasa Shima ya bar zancen ya koma Kan batun tafiyar su Asibiti. "Goben idan Allah ya kaimu magaji ya kaiki ki dauko wayarki tunda tana gida ki dauko Yan abun bukata tunda sai kun Gama komai kafin ku dawo wata Kila zaku dauki lokaci ba'a Gama gwaje-gwajen da zasuyi Miki ba, itama wannan Matar ta dauki abinda ya Kanata nata saiki fada Mata". Sun Dade suna wayar har Ammah ta wuce part din Abba Basu Gama ba, sai kusan Sha daya ya hakura sukayi sallama. Da safe tunda wuri Ammah ta saka magaji yakai Zilai gidan ta karkashe kayan electronics, ta cire duk abinda ake ganin ze iya lalacewa ta Mika gidan maman junior bisa Umarnin Ammah. Karfe bakwai da rabi Mai kyau su zilan sun koma gidan Ammah da kayan Zahra a jaka set biyar da sauran tarkace na bukatar yau da Kullum. Sam Mama Bata da labarin kwanan zahrar a gidan Sai da zilai ta shigo da Kaya a hannu magaji Kuma karamar luggage a hannunsa da sauri ta aje bowl din dake hannunta ta nufo Zilai tana fadin "lafiya kuwa daga Ina haka zilai?" Gaishe ta zilan tayi tana fadin "munje mun daukowa Zahra kayan sawarta tunda Bata koma gidan ba Nan muka kwana daga asibitin gida mukayo". Ikon Allah wallahi ban sani ba, Babu Wanda ya fada min tun daren, Bari na shiga Naga jikin nata". Suka nufi part din Ammah. ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI ✨✨✨ MAMAN FATEEMAH. Page 37. _______Cikin wani irin takun Jin Dadi da karsashi Mama ta shiga parlourn Ammah tana fadin "Ina patient din take? Ashe nan Kuka kwana jikin ne yaqi Dadi bayan mun taho? wlh ban sani ba sai yanzu da naga zilai ta shigo da kaya ta fada min". Ammah ce ta fito faga kitchen din part din ta tana fafin "ko daya sangarta ce kawai Wai kada ciwon ya tashi cikin dare, kamar an fada Mata a Nan din ciwon baze tashi ba". Dan murmushi Mama tayi "ai kinsan yanda take da son gida ai inaga idan sun dawo ma saita zauna a nan din tunda ba'a San ranar da mijin nata ze dawo ba gara tana kusa tunda Naga alama ba wani iya riqeta zeyi ba da farawa da iyawa, Allah ma yasa Bata da juna biyu ai da abun yayi yawa ga zawarci ga goyo".Dan Jim Ammah tayi Dan da gaske maganar ta doketa wane irin mugun fata ne haka bako kawaici gurin fadin maganar. "Allah ya rufa asiri, duk abinda Allah ya tsarawa zahra Zan karba da hannu biyu ba komai, idan Allah ya hukunta Mata rabuwa dashi bani da tsimi bani da dabara,kinsan shi dare ga Mai rabo hantsi ne, fatan da muke dai Allah ya rabata da wannan ciwon me bibiko". Zahrar ce ta fito Shar da ita cikin doguwar Rigar material Baki da pink din flowers manya ta saka gyale medium a kafadarta tana baza kanshi kamar anyi barin turare a jikinta a hankali ta shigo cikin takunta na rausaya tana amsa wayar sajida wadda ta kirata tana dubata da jiki. "Ke kuma waya fada miki bani da lafiya?" Zahra ta fada tana Zama kusa Auta da yake breakfast ze tafi school. Tunda zahrar ta shigo idanun mama ke bin zahrar da kallo. Wayar taci gaba da amsawa tana fadin "jikin fa da sauki kawai shine yake ta bankama abun kema fa kinsan ciwon tun Mana kazaure shi ne fa yaketa faman tsallen tsinka tsimma akansa". Ta fada tana dariya kasa kasa. "Amma Baki da kirki mijin naki ne me tsallen tsinka tsimman? Saura kadan nayi Miki tawaye bestie irin wannan cin fuska haka?". "Sai anjima Zan kira". Ta fada a hankali duk da Daman idan ba Kuna kusa sisai ba bazakaji abinda take fada ba. Sai da ta kashe wayar sannan da dubi inda Mama take zaune ta Dan rankwafa kada daga zaune tace "Mama Ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ta amsa tana fadin "ya jikin duk da dai ba alamar ciwo a tare dake, Banda son yawo Ni banga abin tafiya har Kano ba akan ciwon mara na Mata". Badan Ammah ta jawa Zahra layi ba da Babu abinda ze Hana ta bawa Mama amsar maganarta ba to ba Hali sai zilai ce t
🏠