NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 112 of 136

n ko gaban kanta tayi nasanta da kulafucin gida ganin ta samu dama zata iya fakewa da haka ta taho kaima Abba kasan halinta".. D'an Bata fuska tayi "Kai Ammah Dan Allah fa....." "Kinga uwarta wuce ki kwanta ki huta Keda Baki da lafiya gida dai ai na danki ne, ba Mai hanaki shigowa Zan Kira shi Mahmud din na fada masa ". "To Abba na gode". Ta fada tana shigewa cikin Zilai ta bita da ledar magungunan ta. Abban Bai jima ba ya fice saboda ya baro mutane masu son ganinsa da yawa a kofa. A bakin kofar bedroom din Ammah suka had'u da zilai tana kokarin fitowa. "Ku kuma sai koyo gudun hijira bakwa tsoron maganar mutane masu jiran k'iris su karawa miya gishiri?". "Kayya Ammah idan za'a biyewa maganar mutane ai ko ruwa ruwa ka shiga sunce ka tada k'ura, Kuma ma waye ya ganta Kuma gobe da safe zamu wuce Kano idan Allah ya dawo damu ta wuce dakinta". Zahra na shiga ta fada toilet Dan babu abinda take bukata sama da wanka du ji take jikinta na warin Asaibi. Ta jima tana zubawa kanta ruwa kafin ta fito, sabuwar rigar barci ta dauko cikin kayan Ammah ta saka, ta dauko zumbuelen hijabin Ammah ta Fara sallah. Ammah ce ta shigo dakin lokacin Zahra ta Idar da sallah Tana addu'a, sai da ta shafa sannan ta juyo tana fadin. "Sannu da dawowa Ammah". "A'a ke za'a yiwa sannu, ya jikin naki?". "Da sauki sosai nifa da Abba ze fada Masa bama sai munje wani Kano ba, na warke tunda Daman na Saba duk wata inayi wannan ne kawai ya matsa min sosai". "Kamar Yaya Abba ya fada Masa shi wa za'a fadawa?". Ammah ta fada tana kallon zahrar, Baki ta turo tana fadin. "kema Ammah kin sani fa kowa nake nufi". Dan murmushi tayi kawai. "Ki Kira ki fada Masa bazakije ba Mana sai Abba ne ze Miki tafinta, tunda yace ga yanda yake so ai haka Zaki hakura kuje a duba ki tunda Naga alama Nan din be kwanta Masa ba, Kuma dazu naji kina maidawa Asabe har da Mama magana tona Hana kada na k'ara Jin makamanciyar magana irinta daga bakinki, ki bar mutum da halinsa kedai ki Zama me kauda Kai kawai ki Kuma rike Addu'a takobin mumuni ce kuma hassada ga Mai rabo taki ce". "Kiyi hakuri Ammah in Sha Allah bazan Kara tankawa kowa ba,gani nayi basuji kunyar maganar a gabanki ba shi yasa na rama Nima". Knockig da Sallamar Abdul Hakeem ce ta dakatar da abinda Ammah zata fada. Ammah ce ta amsa sallamar ta bashi uzinin shigowa. Sannu da dare ya Kara yiwa Ammah sannan ya mikawa Zahra wayarsa dake Hannunsa da alama vedio call yakeyi, Yana fadar "gashi Mahmud zeyi magana dake". A d'an kaikaice ta kalli gafen da Ammah take kafin ta Mika hannu ta karbi wayar. Tana karba Ya Abdul Hakeem ya juya, Ammah tabi bayansa tana Masa maganar danyar Madarar da akace ya Aiko da ita da yamma lokacin tana Asibiti. Saida Zahra ta tabbatar sun fice gaba daya daga dakin sannan ta dubi Screen din wayar fuskarsa ta gani Yana kallon ta sai taga yayi wani zuru-zuru kamar Wanda yayi ciwo sai hancinsa ya Kara fitowa zuwat dashi hakensa ma ya qaru. "A hankalin tayi masa sallama tana fadin "Ya M baka da lafiya ne Naga ka rame?". Bushashshen lebensa ya da tura cikin Bakinsa ya lumshe idanunsa tun lokacin da aka fada Masa Bata da lafiya bai samu peace of mind ba sai yanzu daya ganta. Dan ita ke ciwon Amma shi keda zulumin da ramar Dan tun daga lokacin zuwa yanzu daya ganta Baya Jin yaci wani Abu na kirki a cikinsa. A hankali ya bude idonsa ya Dora akan tata fuskar dake kallonsa, wani yarrrr taji da suka hada idon. Cikin tsantsar kasala da jigata ya bude Bakinsa a hankali yace. "My previous hankalina ya tashi, wallahi gani nakeyi kamar Zan rasaki, ya jikin naki? Kuma tun yaushe ciwon ya kamaki Baki fada min ba? sai Zayyan ne yayi min text Wai an wuce dake Asibiti, kinsan kuwa yanda hankalina ya tashi? Daman kina yin irin hakan ne ko yanzu ya Fara Miki?". Dan walainiya tayi da idanunta tana fadin " Naji fa sauki Daman inayi kawai wannan ne yayi min tsanani sosai, amman tunda akayi min allurai da drip na warke, kaga ai ba sai munje Asibtin Malam din ba ko?". Wani kallon Baki da lissafi yayi Mata, shi Yana can ya kasa tsugun da ransa ita Kuma tana fada masa wani shirme. "Zuwa can ba fashi, kuma da izininwa Kika taho gida jinya kin tambayeni Zaki zo gida?" Narai narai tayi da Ido abinda ke tsuma shi kenan yaji Yana neman sakin layi. "Kai Yaya wallahi na fada maka Zanzo gurin Ammah Kuma ka amince kace nazo koka manta Ranar da zaka tafi?" Ta fada a shagwabe tana zubawa Masa sexy eyes dinta da suka Kara wani hasken wahala data Sha. "Kawai dai kin min wayo tunda kin fini sanin takan duniya kin fini ilimin boko me zurfi shine zakiyi min education, haka ake cewa ko?". Shiru tayi Masa. "Kiyi magana Mana nifa bana son Shiru sai Naga kamar jikin ne" "Nifa na fada maka na warke sai wani jikon Kuma". Zaro Ido yayi Yana Mata kallon mamaki. "Sai wani jikon kamar Yaya? Kenan har kina tunanin Zaki qara fuskantar wani ciwon bayan wannan?". Kai ta gyada Masa alamar Eh. "Pls talk ki bude Baki kiyi min bayani as how kike expecting Zaki Kara irin wannan ciwon?". Sai da ta kauda kant
🏠