.
Zahar ce ta juyo tana fadin. "Abbana sannu da Zuwa, ina yini?".
"Yauwa uwata lafiya kalau Alhamdulillahi jiki yayi kyau".
"Eh Abba Daman Kai nake jira kazo kayi musu magana su sallameni mu tafi Nina warke na gaji da Asibitin tunda sunyi min hoton da gwajin da safe mun dawo mu karba bana son kwanan gurin Nan".
Ta fada tana hade rai.
"Eh Nima abinda ya taso ni Kenan maganar tafiyar taku gidan ne Dan yanzu haka daga office din doctor din muke sun bamu referral Zuwa Aminu Kano kamar yanda mijinki ya bukata yace da safe zaku tafi kiga gynecology doctor ayi bincke tunda ance kin jima kina fama da matsalar".
Kafin Ammah tayi magana Mama ta rigata.
"Wane irin Kano Kuma ana zaune lafiya, Wai ciwon har ya Kai haka ne idan Asibitin ake son canzawa aje Bauchi Mana Amma har kano akan ciwon mara kawai".
Dan murmushi Ammah tayi Bata ce komai ba.
Abban ne yace. "Yanzu kina nufin na Kira shi nace masa abinda ya fada baze yuwu ba Kenan ko Kuma Yaya kike son ayi?".
Shiru tayi Bata ce komai ba. Ammah ya kalla "kinyi Shiru ko kema hakan ne nufinki".
Kai ta girgaiza tana fadin "A'a tunda ga yanda ya fada ai shike da iko da matarsa ita da waye zasu tafi kanon?".
"Yace Sameer ne zezo sai zilai ta rakata haka dai ya fada min yanzu da Daren nan"
" To Allah ya kaimu yanzu tafiya zamuyi ke Nan?".
"Eh haka ne, ku kuje Abdul Hakeem ya mayar daku gida kafin ya dawo ruwan ya Kare sai na raka uwata gida" ya fada Yana murmushi.
Sororo Mama tayi Jin Abba da kansa ze maida su Zahra gida.
Badai ta tofa ba Amma a ranta taji ba dadi. Tun kafin Ammah ta dauko hand bag dinta Mama ta fice daga dakin.
******
MAHMUD
Bayan sun gama waya dasu Abba, Sameer ya Kira harta katse ba'a dauka ba sake Kiran yayi tana Fara ringing ta dauka.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Ya fada Yana Zama kusa da Fateeha tana shayar da jaririn su.
Daga can Mahmud ya amsa sallamar ya Dora da fadin "gobe in Allah ya kaimu ka shiga Azare ka taho da madam zataga doctor a Nan kanon na Kira doctor Haseena za'a kawo patient dina".
"Doctor Haseena fa! ita zata duba maka madam din?".
"Eh Mana ko da matsala ne?".
"A'a gani nayi kada taga anyi Mata cin fuska".
"Ba wani damuwa kawai,do what I said".
"Ok. In Sha Allah".
"Kada ka kaisu gidanka a kaisu gidan dake Nan DAWAKI ROAD su zauna har su Gama abinda zasuyi su koma".
"Kana ganin Bai musu girma ba kuwa? dana karkasara aka kaisu yafi kusa da Asibitin ma akan na Nasarawa GRA".
"A Nan nake son ta zauna kake maganar girma har wani babban gida ne ka barta ta saba da Zama a irinsu tun yanzu Kai dai kasan kuma abinda zaka fada Mata, a Kai musu duk abinda ya kamata sai dai na fada ba kayi komai kawai, ka fadawa momi ta Basu house maid daya su hadu da tata sai su ringa aikin tare, kayan sakawa dai nasan ba matsala ka Kira Rukayya ta duba abinda ya kamata sai taje ta sawo, ka Bata card din master bedroom na kasa ta sauka a nan.
"Shike Nan za'ayi yanda kace, amma baka tunanin taga wata shaida data danganceka a gidan?"
"Gaskiya bana tunanin akwai wata alama dake alamtani da gidan".
"Anyway, Allah ya kaimu goben, takwaranka na gaisheka".
"Oh sorry a shafa kansa sai nazo ganinsa, kaina ne ya dauki zafi".
Dan murmushi Sameer ya kashe Kiran Yana kallon Fateeha dake Masa kallon Karin bayani.
"Oga ne, Kinga yanda ya shiga damuwa kuwa nifa Banga abinda oga ya damu dashi ba irin yarinyar Nan idan Kika cire Iyayensa to ba na biyunta, ai ban Gama sarewa da lamarin sa ba saida ya nemi guri ya zauna a dakin kofar gida na almajirai duk da gurin bashi da wani aibu". Baki bude Fateeha ta bi Sameer da kallo "dakin Almajirai fa tace shi ogan da kansa? Tab lamarin Azimun ne, Allah ya bamu ko Rabin yanda tayi sa'ar sace zuciyar jarimi kamarsa Wanda Mata ko kallo basu isheshi ba".
Lakuce Mata kumatu yayi Yana fadin.
"Waya fada miki ba'a Miki so irin Wanda ake mata?" 'yar dariya tayi kawai tasan zance ne inji 'yan magana
*******
Lokacin da Ya Abdul Hakeem ya dawo ruwan ya qare har an cire Mata.
Cikin marairaita Zahra ta kalli Abban da Ya Abdul Hakeem.
"Dan Allah Abba ka tafi Dani gida wlh jiya nasha wahala gashi ba kowa a kusa dani kada na mutu Ni kadai a daki".
Saita saka Masa kuka.
Baki Ya Abdul Hakeem ya bude alamar mamaki.
"Ke! Amma wallahi wannan dai abun kunya ne ki wani kama kuka, kin manta yanzu ba da bane kema fa soon Zaki Zama uwa".
"Ungo Abdul uwata kake fadawa haka a gabana? Fita ka Kirawo zulaihatu ta tattara musu magungunan Nan sai mu tafi can din"..
Dariya yayi ya fice Yana mamakin Abba yanda yake nunawa Zahra soyayya fiye da kowa.
Ba zato ba tsammani Amma taga zilai ta shigo da Kaya a hannu Zahra na biye da ita.
"A'a ku kuma ya haka Naga Abba yace ze rakaki gida sai Kuma gaku a nan?"
Maganar Abban Ammah taji a bakin kofar parloun.
"Ni nace ta taho gida tunda batajin dadi Kuma gida su kadai, gashi Mai gidan nata yace goben zasu wuce kanon gara su kwana a Nan kawai tunda ke dai ba can zaki bita ba gara su tafi a gaban ki".
"Ok, ai ban sani ba nayi tunani