a naji Abban su Yana fadin Daman tana fama dashi ne Saida na yau yafi zafi fiye dana bayan gaskiya Dan har hoto da gwaje-gwaje zasuyi Mata inga in Sha Allah ba wani damuwa kome ake ciki Zan sanar da kai Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin".
Ya fada jikinsa a mace da duk ya shiga cikin damuwa.
Number zahrar ya Kira tana ta ringing Amma ba'a dauka ba tsaki yayi tunda yaji haka yasan wayar na gida Basu dauka ba.
A karo na farko ya Kira wayar Ammah lokacin wayar na hannun Auta Wanda ya biyo mama da Asabe Asibitin, Dan lokacin da su Ammah suka taho mamar Bata Nan Wai taje duniyar kanwar Babar su Asaben, shine da suka dawo.Abba ke fada Mata Zahra ba lafiya suka taho harda Auta, Autan dake kusa da Mama da wayar Amman a.hannu Yana game na football Mamar dake kusa dashi ta karbi wayar ta mikawa Ammah, batare da Ammah ta duba wayar ba ta daga tana fadin.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Cikin girmamawa Mahmud ya fara gaishe da Ammah, ita har ga Allah Bata tab'a kawo Mahmud ze Kira ba.
Dan Jim yayi Yana Jin nauyin tambayar ta Zahra, Jin shirun yayi yawa bayan gaisuwar yasa Ammar fadin "wa ake nema ne".
"Ammah nine na kirane naji ya jikin Fateemah? wlh ban sani ba tun safe ban bude wayar ba muna aiki sai yanzu dana bude ake fada min Bata da lafiya Kuna Asibiti, Dan Allah ayi hakuri in Sha Allah hakan bazata fatuwa ba".
Ammah ji tayi kamar ruwa ya cinyeta Ashe sirikinta ne wlh Sam bata Gane shi ba.
Ciki Jin kunya da Kara Ammah tace Masa "ba komai ai jikinta da sauki yanzu ma barci takeyi, ya akayi suka fada maka haba ka kwantar da hankalinka Daman takanyi irin wannan ciwon lokaci lokaci sai dai wannan ne ya Dan matsa Mata sukayi admitting din ta zasu bincike a Kai".
Ammar ta fada tana dan jin nauyinsa.
"To Ammah nagode in Sha Allah da safe Sameer ze shigo zasuje Kano Nan Aminu Kano zasu dubata sosai tunda suna da Gynecologist consultant Ina ga kamar hakan zaifi can suna da kayan aiki na zamani, Zan Kira Abba da Baba Malam muyi maganar, na gode Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin, Allah ya bada sa'a yayi Albarka".
Sukayi sallama.
Bayan sunyi sallama Ammah wayar tabi da kallo tana mamakin yanda yake magana da ita tamkar mahaifiyar shi, ya kama sunanta radau.
Mama ce ta kalli Ammah tana fad'in "ko mijin nata be? Naji kina masa bayanin yanayin ciwon nata gashi abin takaicin tun ba'aje ko Ina ba ya tsallake ya bar yarinya da wahala, Allah dai yasa ba juduwa yayi ba ya barta da jangwam yanda aka Fara 'yan ciwace ciwacen Nan ai karshen maganar ace ciki ya bayyana shi Kuma yayi masa wuri tunda Daman tsintacciyar magen ce Bata mage ya sulale yabar gari naji ance harda motarta ya tafi Kinga ribar kafa Kenan".
Duk surutun da Mama keyi akan Zahra ko kallon ta Ammah batayi ba Dan tasan tana fada ne dan ta Bata Mata Rai kawai, Zilai ma Mai aikin su tana tsaye kusa da Zahra tana gyara Mata hannunta da aka saka mata drip, itama ko tari be kunce Mata ba bata tofa tata ba, to me zata ce maganar ba ta ta bace.
Jin ba Wanda ya tofawa Mama ko A a cikin maganarta yasa Asabe cewa.
"Wallahi kuwa mama Allah abin tsoro mutum abin tsoro daman nasan in ba wani ikon Allah ba yaron Nan guduwa zeyi yayi gaba kinsan irinsu Yan hujja ne ba wani Zama zeyi na din-din-din ba a garin Nan, abin gudun ma ya jonawa yarinya ala kakai ya tafi ya barta da 'ya'ya, Kuma ki duba kiga yaro Nan a wanke yake Kar bashi da duhun jahilci ko kauyenci ko qanqani haka kawai ya jonawa yarinya alakakai ya gudu ya barta, idan tafiya ta Mike wata Ranar har azo ana yiwa yaro gorin mahaifi ga babu jinjinan dangi kana ji a sheganta yaro
ko yarinya".
Har Zilai ta baro bakin gadon da zimmar maida martani, sai maganar Zahra suka juyo suka juyo tana kallon Asabe Tana fad'in "lafiya kalau muka rabu, bai Kuma bar garin Nan ba Sai da ya fada min salinsa da iyayensa daga karshe ma mutum ya aje min saboda yana yin rayuwa koda ta Allah ta kasance shine ze kaini har dakin mahaifiyar sa Kinga kuwa ai bani da damuwa a Kan lamarin".
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨✨
MAMAN FATEEMAH.
Page 36
______Zahra tana Gama fadawa Asaben abinda ke cikinta ta juya musu baya, ko banza bazata kwana da fushin zuciya ba, dan tasan idan ba ita tayi magana ba Babu abinda Ammah zata ce Dan sau da yawa idan irin haka ta faru ko kallon Mama batayi sai dai ta bawa banza ajiyarta.
Daga Asaben har Mama ba Wanda ya Kara magana,haka Ammar ma da Zilai ba Wanda ko tari ya kuncewa, Auta kuwa wayar mamar ya dauka yaci gaba da sha'aninsa.
Shiru dakin ya dauka kamar mutuwa ta ratsa, sallamar Abdul Hakeem da Abba ta katse shirun cikin nuna tsantsar duniyanci Mama ta tashi da sauri tana fadin "Abba har kun karaso sannu da Zuwa" tana gyara Masa kujerar kusa da gadon.
Sai da ya zauna sannan ya amsa gaisuwar dasu Zilai da Asabe ke Masa suna jajanta masa, suka gaisa da Abdul Hakeem sannan suka fice daga dakin.
Mama ce ta Fara gaishe da Abban kafin Ammah ma ta gaishe shi, sannan Abdul Hakeem ya gaisu dasu Ammar Yana tambayar Mai jikin