a Kira Sameer sai ya Kira Abdul Hakeem, daga Jon yanayinsa kasan Yana cikin damuwa abinda ya Kara daure Abdul Hakeem Kai yandq Sameer yake amsa wayar Mahmud cikin kulawa da bada girma.
Sun dauki a kalla minti arba'in kafin babban likitan ya fito sannan sauran Suma suka fito.
Su Abdul Hakeem sun bin bayan likitan kamar yanda ya bukata Amma ganin an gungoro Zahrar a gadon daukar marasa lafiya yasa suka nufe ta da sauri suda su Aunty Hasana.
Wanda ya turo gadon ne yace "ai ta farfado ba wata matsala ana so ne dai ta samu hutu sosai jininta ne yaso Hawa Amma cikin ikon Allah anyi controlling dinsa".
"Oh no 'yasu Allah ka dubi lamarin wannan 'yar maraiya duk da Bata tashi da rashin gata ba sai yanzu ka kawo Mata Tata jarabawar Allah ka shiga cikin lamarinta".
Aunty Hasana ta fad'a itama tana goge hawaye.
Baba Tabawa dasu Sajida suka amsa da "ameen ya Rabbi"
Dakin 'yan da'i da'a aka kaita tunda tana bukatar isolation.
Saida komai ya Zama dai dai an saka Mata drip sannansu Sameer sukaje gurin likitan. Fad'a yayi so sai akan yanda akayi har karamar yarinya kamar wannan damuwa tayi Mata yawa har har take barazana ga lafiyar ta.
A can gidan biki Kuma Amma ta rasa inda su Hasana da Inna suka tafi Dan hankalinta Bai kawo Mata Hajiya kaltume ma Bata Nan ba sai da abokiyar zamanta tazo sannna ta fuskanci itama Bata Nan din wayarta ta dauko ta Kira Hasana, lokacin tana zaune gaban gadon da aka kwantar da Zahrar.
Sunan Ammah ta gani sai lokacin ta tuna Ashe Bata fad'a Mata ba.
" Assalamu Alaikum Ammah".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, wai Ina Kika tafi ne babu ke Inna maimuna ma Bata Nan Hajiya kaltume ma banganta ba".
Dan Jim tayi har Saida Ammah tace "kina jina?"
"Eh inaji Ammah duk muna tare dasu, muna Nan gurin Zahra Bata Jin dadi ne Amman da sauki yan haka barci take".
"Wane irin zance ne wannan kamar Bata Jin dadi Kinga Hasana fadi min gaskiya yanzu kina Ina?".
" Muna F.M.C wlh jikin da sauki sosai kawai sunce ana dai San ta huta ne, kada ki tada hankalin Dan Allah".
"To Allah ya kyau Amma Ina hankali ze kwanta".
Waje Aunty Hasanar ta fito gurin su Baba tabawa da sajida tace
"Baba tabawa Dan Allah kuje gida da sajida tasan inda aka aje abubuwan da zasu bawa kawayensu tunda yau zasu wuce sai ki fad'a musu tana gida gurin Abba, ta kalli Sajida ke Kuma duk tmbayar da saying Miki kice Baki Sani ba mu barsu a haka".
Kudi ta mikawa Baba tabawan sannan ta karasa gurinsu Inna maimuna da Hajiya kaltume, Suma bayi tayi musu na Kiran Ammah tace suje gidan Dan hankalinta ya kwanta.
*********
Da kyar Amma ta Bari akayi sallar magariba ta shiga bangaren Alhaji Jafar ta same shi da Hassan da Abdul Hakeem suna magana akan Zahra Hassan Yana ta mitar meyasa Abban yayi haka ai da hakuri kawai akayi har lokacin da Allah ze kawo Mata wani.
Dan murmushinsu na manya yayi Yana "fadin wannan ma in Sha Allah Babu Dana Sani a cikinsa ni nasan nagartar Dana gani tare da yaron yasa na bashi, Kuma ko bayan Raina zakuce na fad'a muku".
Jiki ba kwari Amma ta gaishe da Alhajin tana Masa ban gajiya tare da godiya.
Sannan ta Dora da fadin "Dan Allah ko zaka Bari naje Naga jikin nata?"
Tsai yayi Yana kallon ta "da kinyi hakurin zuwa Suma da anjima zasu taho gida yanzu ma daga cen muke ko zuwan mu Bai isar ba?"
Cikin Jin nauyinsa tace "A'a ya badatar"
Ta tashi ta nufi kofa da kallo Abban ya bita ita kanta tausayi take sashi da gani zuciyar ta ba Dadi.
Da sallama suka shiga dakin lokacin Aunty Hasana tana sallar insha'i ita Kuma zahra farkawarta kenan tana kokarin tantance Wai inane ma Nan din inda ta gani idan dai ba gizo idanunta ke Mata ba kamar asibiti.
Sallamar ce ta katse Mata tunani ta Dan dago kanta kadan sukayi arba dashi Ido cikin Ido da sauri ta runtse idanunta zuciyar ta na wata irin bugawa tana ambaton Allah a zuciyar ta, meya kawo wannan dodon nata gurinta, Kara rufe idanun tayi it fa wallahi zata iya rantsewa Allah duk duniya ba idanun da suke figitata kamar nasa.
💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️
Strory
&
Written
By
MAMAN FATIMAH
Page five
📖🖋️
_______ Shiru dakin ya dauka har zawan lokacin da Aunty Hasana ta idar da sallar.
Dan juyowa tayi kadan tana fadin "wa'alaikumus Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, sannunku da zuwa Bismillah ga kujeru nan ku zauna".
"To mun gode Aunty" Sameer ya fada.
Cikin ladabi da mutuntawa suka gaishe ta tare da tambayar Mai jikin, ta amsa musu da sauki, sai kuma dakin ya Kara daukar shuru Zahra dai tunda ta rufe ido Bata Kara gigin budewa ba, ita ji take duk ya cika dakin ita tun ganinta na farko dashi a duniya ya birkita Mata lissafi, Kuma saboda Allah meya kawo shi gurinta asibiti duk da tasan mutumin Ya Abdul Hakeem ne Amma sai taga kamar ba sai yayi Masa Kara ba, ko Kuma yazo wata sagbar ne asibitni ya Sami labarin shine ya shigo ya dubata.
Magaji ne ya shigo dakin da sallama sai Kuma ya Dan tsaya baiyi tunanin ganinsa ba Sam da fara'a ya karaso Y