NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 109 of 136

makin ogan nasa na neman gurin Zama a wannan Dan gurin shi ko takura ma yaga alama bayayi wata sabuwar rayuwa yake shimfidawa cikin kwanciyar hankali. Direct A&E magaji ya nufa zilai ce ta taimawa Zahra ta fito daga mota suka shiga ciki shi Kuma magaji ya nufi inda ze karbo file. Ba jimawa yazo ya kawo file din, bayan duguwar tambayar da wata likita da take on call tayi Mata ta rubuta Mata magunguna da allurai da drip ana cikin saka Mata ruwa su Ammah suka shigo dakin, ma'aikatan da masu jiyyar suna ta gaishe da Abba, gaban gadon Abban yaje ya tsaya sunan ta Abban ya Kira ta bude Ido ta kalli Abba tana kokarin tashi zaune "A'a uwata koma ki kwanta ya jikin naki?" "Da sauri Abbana, Ina kwana?" "Lafiya kalau". Ammah ce ta matso tana fadin "sannu Ashe ciwon cikin ne ya tashi?" "Eh Ammah wlh har yafi Wanda nakeyi kamar Zan mutu". Ta fada tana goge hawayen daya zubo Mata. "A'a uwata Banda kuka ai kin girma". Abba ya fada Yana dariya. Itama Zahra dan murmushi tayi ta juya Kai kunya ta kamata ta. Abba Bai bar Asibitin ba Saida aka Maida Zahra Aminity ward. Tun bayan tafiyar su Zahra Zayyan ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya nemi number Mahmud tafi cikin carbi amsa daya balarabiyar da akayi linking da computer ke bashi wadda ba fashimta yake ba, sai dai hasashe kawai number Bata tafiya take fada Masa. A gida Abba yayi sallar Azzahar bayan an fito ne ya fadawa Baba malam Zahra tana Asibiti Bata Jin Dadi. Cikin nuna jimami Malam yace "tun yaushe take Asibitin ba'a fada min ba, kuma menene yake damun diyar tawa?". "Wlh ciwon cikin ne take fama dashi tun cikin dare shine dazu Mai Taya ta Zama ta kita Asma'u ta fada mata, sai nasa magaji ya Kai su Asibitin sai suka Bata gado Wai zasuyi Mata hoton cikin da sauran gwaje-gwaje don su fadada bincike akan ciwon tunda ta jima tana fama da lalurar". "Ikon Allah! Allah ya Bata lfy yasa kaffara ne, ai da anyi magana tun a bayan da an Nemo Mata taimakon ciwon Amma yanzu ma Bata baci ba, idan anyi binciken an gano wane irin ciwo ne a fada mini akwai magungunan ciwon cikin Mata da yawa a gurina in sha Allah koda tsiron mahaifa ne da sauransu in Sha Allah zasu narke Koda na aikine zebi jinin al'ada ya narke ya zube". "To in Sha Allah Zan fadawa Asma'u kome Kenan Zan fada maka". Sun jima a harabar gidan Abban kafin suyi sallama. Bayan sallar la'asar malam yasa Habib ya tukashi zuwa Asibitin lokacin da sukaje Zahra tana barci sun gaisa da Ammah Malam ya jajanta Mata Habib ma ya jajanta Mata jikin Zahrar Basu dade ba suka tafi. **** Tun safe da Mahmud ya fita tare da daya daga cikin amuntattun hadimansa na kasar suka fice sun Kai ziyarorin bazata Dan tono wasu laifuka da ake son binnewa, ya dakatar da mutum hudu ya sallami mutane biyu wadanda sukayi sama da fadin maqudan kudade tun bayan rashin sanin inda Mahmud din yake ganin tafiya tayi nisa Kuma baya bibiyar su Sam sai kawai suka tsunduma cikin dukiyar sukayi dumu dumu a ciki, zuwan Sameer ne ya bankado badaqalar wadda tafi karfin shi wadda tasa dole Saida Mai takanas din ya taso, China Kuma issue ne na rufe musu kamfanin laces da materials da akayi Wanda suke zargin ba'a biya kudin harajin kasa ba a tun farkon bude kamfanin, Mahmud yayi kokarin tura duk evidence dinsa ta wibeside nasu Amma sunqi yarda Wanda dole tasa Saida yazo da kansa sannan lamarin ya gyaru. Sai dare sosai ya dawo masaukinsa yaso ya fita ya dan shaqata beach Amma yayi matukar gajiya sosai Koda yayi wanka coffee kawai yayi order da snacks, tunda garin Allah ya waye Bai samu kanshi ba sai yanzu wayarsa ya dauko ya kunna Dan rabon da ya kunna ta tun jiya, sakonni ne suketa shigowa rututu, amma na Zayyan da Habib su sukafi daukar hankalinsa lfy? Ya tambayi kansa. Sakon Zayyan ya fara budewa ai baisan lokacin daya Mike tsaye ba duk gajiyar dake tare dashi Nan take tayi nata guri, cikin tashin hankali ya Fara lalubar number din Zayyan cikin kankanin lokaci Kiran ya shiga, Bai saurari gaisuwar da yake Masa ba ya Fara fad'in "wace irin magana kake min haka? Ashe ajiyekan da nayi bashi da anfani,tun safe Amma kaqi fada min halin da yarinyar mutane take ciki sai yanzu da tsohon Daren nan? Kana son ace ban damu da halinda 'yarsu ke ciki ba tunda throughout yau ban kirata ba nayi busy sosai".."sorry oga wallahi tun lokacin nake neman wayar ka Bata shiga kwata kwata shine nayi make text". "Oh shit! Wlh ban bude wayar ba sai yanzu, yanzu ina zahrar?" "Wallahi Yallabai bansan inda take ba tunda suka fita ban Kara samun wani information akan komai ba". Tsaki Mahmud yayi ya datse kiran. Habib ya lalubo ai sakonma bai tsaya dubawa ba ya Kira shi. "A gaggauce ya amsa sallamar da gaisawar da Habib din yake Masa. "Wai meke fatuwa ne da Zahra?". "Wallahi Nima bani da masaniyar takamaimai kawai dai bayan anyi sallah baba Malam yace na kaishi Asibiti ya gano jikinta sai a lokacin na Sami labarin Bata da lafiya ance ciwon ciki ne, lokacin da mukaje tana barci Amma idan an jima zan koma na qara dubota kome kenan Zan fada maka ka kwantar da hankalink
🏠