NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 108 of 136

ciyuwa a irin wannan yanayin. Ganin Sha biyu tayi Zahra Bata fito ba yasa zilai nufar bedroom din nata ta gani anya lafiya kuwa? Knocking tayi taji Shiru ta qara you taji Shiru Bata kara ba uku ba ta tura kofar a can tsakiyar gadon ta ganota a kudundune, da sauri ta karasa gaban gadon tana ambatar sunan ta "Zahra kafiyarki kuwa har Sha biyu ta gota Baki tashi ba abin Karin ki har ya Fara sanyi?" Da kyar ta dago ta kalli zilan cikin miryar marar lafiya tace Mata "bana Jin dadi tun cikin dare marata take ciwo". "Subahaballahi Kuma Kikayi Shiru Baki fada ba idan haka ne bani da amfani Kenan ace tun cikin dare kina fama da ciwo ki kasa fada mini, ina maganin da kike Sha yake na dauko Miki Ni wlh cewa nake tunda ance idan Kikayi aure ze dena, to na dauka kin rabu dashi yanzu, ai haka wannan likitar ta fada Miki zuwan mu na karshen ko?". Kai Zahra ta gyada Mata kawai alamar Eh Dan ita kadai tasan azabar da takeji. "Fada min Ina maganin yake na dauko Miki" A hankali tace mata "Na sha". "Kin sha Kuma marar Bata Dena ciwon ba?" "Eh" ta fada tana runtse ido saboda azabar ciwo. Fita zilai tayi da sauri ta koma dakin da aka sauketa ta lakubo keyboard dinta ta lalubo number Ammah, lokacin tana tare da Abba suna maganar komawa makarantar Imam Kiran zilan ya shigo. "Abba Bari na daga Kiran Nan Zilai ce naji ko lafiya". "In Sha Allahu ma lfy". Abban ya fada. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu" Ammah ta fada bayan ta daga wayar daga can zilan ta gaishe da Ammah sannan ta Dora da fadin "wlh Ammah jikin Zahra ne ba Dadi tun cikin dare ciwon mararta ya tashi Tasha maganin Kuma a banza shine nace Bari na Kira na fada Miki Koda abinda zakiyi mata tunda kema Aikinki ne ko Kuma a turo Mana malam Bala ya kaimu Asibiti taga likitar ta" . "Ikon Allah! Yanzu ina zahrar?". "Tana daki tana faman mukususu kamar me nakuda wlh abin gwanin ban tausayinsa". "To shike Nan ki dubata za'a San yanda za'a yi ki jira". Ta kashe wayar ta dubi Abba Wanda Shima itan yake kallo, kafin tayi magana ya rigata. "Meya samu Uwata naji Kuna magana Bata da lfy ne?" Ajiyar zuciya Ammah ta sauke "wlh ciwon mararta ne Wai ta tashi tun cikin dare Tasha maganin da take Sha Amma ba wani cigaba shine zilan tace ko Asibiti zasu koma suga likitar da take gani Dan munyi expecting idan tayi aure zasu rabu to Kuma a yanda zilai ta fada min kamarma yafi na baya zafi". "Ikon Allah! Allah ya saukake Bari a tura musu magaji ya kaisu Asibitin tunda duk sauran basa Nan sai mu bisu daga baya mu kuma, ai hakan yayi ko?". Kai ta gyada Masa tana kokarin tashi da nufin tafiya, riko hannunta yayi ya mayar da ita inda ta tashi dayan Kuma Yana Kiran wayar magaji. "Ka dauki mota kaje can hayin banki zaka Kai uwata Asibiti". Ya kashe Kiran yana kallon Ammar. "Ina zaki Kuma Kika tashi? Ki kwantar da hankalinki in Sha Allah ba wata damuwa Kika sani ko jika zamuyi kwanan nan" Ya fada Yana dariya irin tasu ta manya. Itama Dan murmushi tayi tana fadin Allah yasa". "Amin yauwa kokefa dauko gyakenki mu bisu wata Kila muje tare tunda gani a gida araha sai nayi aikin bariki tilas ne". Zilan Ammah ta Kira ta fada mata su shirya ga magaji Nan ze kaisu Asibitin, Suma zasu samesu a can.. Dakin Zahra zilan ta koma yanda ta barta haka ta sameta, kusa da ita zilan ta matsa tana fadin na hado Miki ko ruwan shayi ne kisha Asibiti zamu". Kai ta girgaiza Mata alamar bazata Sha ba. "Ki daure ko kadan ne Dan Allah Kinga wata Kila ayi Miki allura gara kici ko kadan ne". "Cornflakes". Abinda ta iya fada Kenan ta koma ta kwanta. Ba laifi tasha cornflakes din da Dan dama, rolling kawai tayi suka nufi parlour zilai na rike da ita. Basu jima ba sukaji dirin mota alamar magajin ya karaso Kenan, zilaice ta bude kofar tun Bai karaso ba direct inda zahrar ke kwance ya nufa akan two seater. "Sannu Adda ya jikin naki?" Da kyar ta cira Kai ta dubeshi tana fadin "da sauki". "Allah ya Kara sauki, kamota muje kada Rana ta karayi yanzu twenty five minutes to one fa". Zalai ta riketa tana tafiya da kyar suka fito compound din Zayyan yana zaune Yana game a waya tunda bashi da aikinyi a Nan sai zama,ba zato yaga an fito da Zahra haka, da sauri yayi wurgi da wayar Allah ya taimake kan jacket dinsa ta fada da sai dai wata ba ita ba, ya nufo gurinsu Yana tambayar "Lafiya meya faru? Oga kuwa ya sani? sannu" duk a lokaci daya yake jero wadannan tambayoyin da gani a rude yake. Magaji ne ya nufi inda yake suka Kara gaisawa Yana farin. "Ba wani abun damuwa bane Bata Jin Dadi ne zamuje Asibiti kada ka damu". Zilai magajin ya duba "kun fadawa mujinta kada mu tafi babu sanin sa". "A'a bamu fada Masa ba ai ko daga bayane an fada Masa yanzu dai muje Asibitin wannan ma wani Bata lokacin ne". Da sauri Zayyan ya bude musu gate suka fita yayin da Zayyan din ya dauko wayarsa Yana Kiran Mahmud. Ya kirawo shi Amma Sam taqi shiga sai text kawai Zayyan ya tura Masa ya koma ya zauna yana ma
🏠