NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 107 of 136

suka taho harda Auta, Autan dake kusa da Mama da wayar Amman a.hannu Yana game na football Mamar dake kusa dashi ta karbi wayar ta mikawa Ammah, batare da Ammah ta duba wayar ba ta daga tana fadin. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". Cikin girmamawa Mahmud ya fara gaishe da Ammah, ita har ga Allah Bata tab'a kawo Mahmud ze Kira ba. Dan Jim yayi Yana Jin nauyin tambayar ta Zahra, Jin shirun yayi yawa bayan gaisuwar yasa Ammar fadin "wa ake nema ne". "Ammah nine na kirane naji ya jikin Fateemah? wlh ban sani ba tun safe ban bude wayar ba muna aiki sai yanzu dana bude ake fada min Bata da lafiya Kuna Asibiti, Dan Allah ayi hakuri in Sha Allah hakan bazata fatuwa ba". Ammah ji tayi kamar ruwa ya cinyeta Ashe sirikinta ne wlh Sam bata Gane shi ba. Ciki Jin kunya da Kara Ammah tace Masa "ba komai ai jikinta da sauki yanzu ma barci takeyi, ya akayi suka fada maka haba ka kwantar da hankalinka Daman takanyi irin wannan ciwon lokaci lokaci sai dai wannan ne ya Dan matsa Mata sukayi admitting din ta zasu bincike a Kai". Ammar ta fada tana dan jin nauyinsa. "To Ammah nagode in Sha Allah da safe Sameer ze shigo zasuje Kano Nan Aminu Kano zasu dubata sosai tunda suna da Gynecologist consultant Ina ga kamar hakan zaifi can suna da kayan aiki na zamani, Zan Kira Abba da Baba Malam muyi maganar, na gode Allah ya Bata lafiya". "Allahumma Amin, Allah ya bada sa'a yayi Albarka". Sukayi sallama. Bayan sunyi sallama Ammah wayar tabi da kallo tana mamakin yanda yake magana da ita tamkar mahaifiyar shi, ya kama sunanta radau. Mama ce ta kalli Ammah tana fad'in "ko mijin nata be? Naji kina masa bayanin yanayin ciwon nata gashi abin takaicin tun ba'aje ko Ina ba ya tsallake ya bar yarinya da wahala, Allah dai yasa ba juduwa yayi ba ya barta da jangwam yanda aka Fara 'yan ciwace ciwacen Nan ai karshen maganar ace ciki ya bayyana shi Kuma yayi masa wuri tunda Daman tsintacciyar magen ce Bata mage ya sulale yabar gari naji ance harda motarta ya tafi Kinga ribar kafa Kenan". Duk surutun da Mama keyi akan Zahra ko kallon ta Ammah batayi ba Dan tasan tana fada ne dan ta Bata Mata Rai kawai, Zilai ma Mai aikin su tana tsaye kusa da Zahra tana gyara Mata hannunta da aka saka mata drip, itama ko tari be kunce Mata ba bata tofa tata ba, to me zata ce maganar ba ta ta bace. Jin ba Wanda ya tofawa Mama ko A a cikin maganarta yasa Asabe cewa. "Wallahi kuwa mama Allah abin tsoro mutum abin tsoro daman nasan in ba wani ikon Allah ba yaron Nan guduwa zeyi yayi gaba kinsan irinsu Yan hujja ne ba wani Zama zeyi na din-din-din ba a garin Nan, abin gudun ma ya jonawa yarinya ala kakai ya tafi ya barta da 'ya'ya, Kuma ki duba kiga yaro Nan a wanke yake Kar bashi da duhun jahilci ko kauyenci ko qanqani haka kawai ya jonawa yarinya alakakai ya gudu ya barta, idan tafiya ta Mike wata Ranar har azo ana yiwa yaro gorin mahaifi ga babu jinjinan dangi kana ji a sheganta yaro ko yarinya". Har Zilai ta baro bakin gadon da zimmar maida martani, sai maganar Zahra suka juyo suka juyo tana kallon Asabe Tana fad'in "lafiya kalau muka rabu, bai Kuma bar garin Nan ba Sai da ya fada min salinsa da iyayensa daga karshe ma mutum ya aje min saboda yana yin rayuwa koda ta Allah ta kasance shine ze kaini har dakin mahaifiyar sa Kinga kuwa ai bani da damuwa a Kan lamarin". AUREN HUCE HAUSHI MAMAN FATEEMAH PAGE 35. ________Yana katse Kiran ya tashi tsam ya nufi masaukinsa laptop dinsa ya janyo ya shiga aiki sai kusan karfe daya ya kwanta lokaci bayan lokaci sai yayi murmushi idan ya tuno yanda suka rabu da 'yar gidansa yayi zance mata tana neman tikitawa kanta lissafi Wai ita me miji, kamar ta wani san dadin mijin,Saida yayi wanka yayi nafila sannan ya kwanta. * Zahra kasake tayi da waya a hannu kamar itace Mahmud din "me yake nufi da zasu rage Masa dare kenan neman Mata yajeyi?" Take wata zuciyar tace Masa A'a Yana zolayarki ne da manemin matan ne koda karfin tuwo saiya nemi wani Abu a jikinki, kauda wannan tunanin tayi daga zuciyar ta tasan zato zunubi ne, parlour ta koma gurin zilai sukaci gaba da hirarsu sai kusan Sha daya suka shiga ciki. Washe gari Zahra Bata tashi da wuri ba sai kusan Sha daya, tun cikin dare bata Jin Dadi wata irin murdawa mararta ke Mata, tana samun irin wannan pain din duk karshen wata idan zatayi period Amma wannan yanda yake mata yayi tsanani sosai tun wurin karfe ukun dare ciwon ya tashe ta farka a gigice, inda Allah ya taimaketa Bata sakaci ta rasa maganinta duk rintsi Yana tare da ita, a lokacin ta sha cikin ikon Allah lokaci kalilan ciwon ya lafa ta koma barci da Asuba ma data tashi sallah da sauki sosai sai Kuma yanzu data farka taji Yana neman dawo Mata, da kyar tayi wanka ta sake inner wears ta zura rigar matarial marar nauyi ta koma ta kwanta idan tana wannan yanayin ko turare Bata so sai guda daya kawai body mist ne na strawberry shi ta fesa ta koma ta kwanta Dan abinci dai baya
🏠