nace Mata matar yaron mijinta ce ko ba haka ba?
"Yayi Kam Amma saina dawo ki rakani muje tare anfi saurin ganeki ga kafarki ga tawa, kice na sawo Miki kayan baby na zuwa barka kenan? ko kema a hado Miki kayan naki babyn? tunda da karfina Zan dawo wata kilan ni double shoot ma zanyi tunda Nima Dan biyu ne Ina da twins sister Aishat".
"Twins sister da gaske?"
"Kin taba ganin nayi Miki karya? wlh mu biyu Ammin mu ta haifa first born dinta, mun B'ata ne da ita shiyasa bakisanta ba. Amma nan gaba zaki santa ne Amma fa Zaki Sha surutu Dan sister Aishat parrot ce".
"Amman laifin me tayi maka da zafi haka? Mu namu twins din basa doguwar batawa gaskiya gashi kaima Ammin irin na Ammah tayi mace da namiji".
"Ki Bari kawai labarin da tsawo sai na dawo ai nace Zaki San duk labarina kaf ba abinda Zan boye Miki tunda kin sarkafo min zuciya tun kina free matured dinki Kika Hana duniyata zaman lfy,da farko na dauki irin mutum ya burge ka ne Ashe diban Karan mahaukaciya Kikayi da gudan tsokar kirjina".
Dariya maganarsa ta bata.
"Au dariya ma kike min ko? bayani zakiyi da yarenki, yanda nayi ta fama da garari saina fanshe kayana tas idan Zaki shirya ki shirya".
Cuno Baki tayi kamar tana gabansa ta Fara turza kafa tana fadin "Ni yaushe kaga Ina maka dariya kawai dai... ni banyi maka dariya ba kaifa yayana ne koka manta my big bro....." Ta wani ja cikin salon da ita kanta Bata San tayi ba.
"Ya salam" ya fada a hankali Dan yanda tayi magana har cikin bargonsa.
"Kinaso ki karya min budget ko?"
Ya jefa Mata tambayar.
"Wane irin budget Zan karya maka kana Nan Ina Nan".
"Idan kina min irin haka ai sai kisa na saki layin Dana hau na tattaro ya nawa ya nawa ko komo gida ko ba'a gama ba".
"To me nayi daga magana tom shike Nan sai anjima".
"Wlh Kika kashe min Kira sai kinzo Dubai ko a kafa ne kuma saina yi Miki abinda bazaki manta ba Dan tarihi me kyau Zan kafa Miki ki kashe ki gani, muna hira kina bani nutsuwa Zaki gudu nida ake yashewa Yan canjina Baki tausaya min ba shine Zaki tsere ki barni da Mata masu farauta ta ko? Yanzu haka guda uku tun dazu suke shawagi a gabana suna tunanin irin nasu ne Dan hannu".
Gyara Zama Zahra tayi kirjinta ba dukan tara tara bama uku uku ba.
"Mata kace ko me?"
"Eh Mata Mana bake kina min rowar ganin halalina ba to gashi Nan free sai Wanda yayi maka ka zabi son ranka, ba nace ki bude data na kalli kayana ba Amma kika Kiya Kinga kuwa yanzu saina duba na darje na zaba ta rage min dare, koya kikace my previous?"
Ya Dana Mata kiss ta cikin wayar ya kashe abarsa.
Yana fadin gobe ma idan bace ki bude datar ki qiya, saina kowa Miki kishina ba gaske kafin na kaiki Ina zakiyi da hujja Amma ki shiga yanzu ai Africa ce da sauran gyara.
AUREN HUCE HAUSHI
MAMAN FATEEMAH
PAGE 35.
________Yana katse Kiran ya tashi tsam ya nufi masaukinsa laptop dinsa ya janyo ya shiga aiki sai kusan karfe daya ya kwanta lokaci bayan lokaci sai yayi murmushi idan ya tuno yanda suka rabu da 'yar gidansa yayi zance mata tana neman tikitawa kanta lissafi Wai ita me miji, kamar ta wani san dadin mijin,Saida yayi wanka yayi nafila sannan ya kwanta.
*
Zahra kasake tayi da waya a hannu kamar itace Mahmud din "me yake nufi da zasu rage Masa dare kenan neman Mata yajeyi?"
Take wata zuciyar tace Masa A'a Yana zolayarki ne da manemin matan ne koda karfin tuwo saiya nemi wani Abu a jikinki, kauda wannan tunanin tayi daga zuciyar ta tasan zato zunubi ne, parlour ta koma gurin zilai sukaci gaba da hirarsu sai kusan Sha daya suka shiga ciki.
Washe gari Zahra Bata tashi da wuri ba sai kusan Sha daya, tun cikin dare bata Jin Dadi wata irin murdawa mararta ke Mata, tana samun irin wannan pain din duk karshen wata idan zatayi period Amma wannan yanda yake mata yayi tsanani sosai tun wurin karfe ukun dare ciwon ya tashe ta farka a gigice, inda Allah ya taimaketa Bata sakaci ta rasa maganinta duk rintsi Yana tare da ita, a lokacin ta sha cikin ikon Allah lokaci kalilan ciwon ya lafa ta koma barci da Asuba ma data tashi sallah da sauki sosai sai Kuma yanzu data farka taji Yana neman dawo Mata, da kyar tayi wanka ta sake inner wears ta zura rigar matarial marar nauyi ta koma ta kwanta idan tana wannan yanayin ko turare Bata so sai guda daya kawai body mist ne na strawberry shi ta fesa ta koma ta kwanta Dan abinci dai baya ciyuwa a irin wannan yanayin.
Ganin Sha biyu tayi Zahra Bata fito ba yasa zilai nufar bedroom din nata ta gani anya lafiya kuwa?
Knocking tayi taji Shiru ta qara you taji Shiru Bata kara ba uku ba ta tura kofar a can tsakiyar gadon ta ganota a kudundune, da sauri ta karasa gaban gadon tana ambatar sunan ta "Zahra kafiyarki kuwa har Sha biyu ta gota Baki tashi ba abin Karin ki har ya Fara sanyi?"
Da kyar ta dago ta kalli zilan cikin miryar marar lafiya tace Mata "bana Jin dadi tun cikin dare marata take ciwo".
"Subahaballahi Kuma Kikayi Shiru Baki fada ba idan haka ne bani da amfani Kenan ace tun cikin dare kina fama da ciwo ki kasa fada