NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 103 of 136

n shigar ta sirri ce shi yasa ya canza sheka baya son asan ya shigo kasar mamaya sake son yakai wasu gurare, yanda har ya gama abinda yake yabar kasar wani be sani ba duk da abune mawuyaci hakan ta faru. Barcinsa yasha sosai dan har akayi sallar magariba be sani ba, lokacin daya tashi ana gab da kiran sallar insha'i, a gurguje yayi wanka ya zura sabuwar jallabiyar daya saya cikin kayansa a kasar, a cikin dakin yayi sallar magariba ya fito yabi lifter zuwa masallaci,koda suka idar da sallah be dawo daki ba a nan harabar hotel din ya Zauna da gaske yanayin gurin ya burge shi sosai, coffee yayi order ba'a jima ba wata matashiyar balarabiyar yarinya ta kawo masa coffeen sai yaga kamar 'yar gidansa, nan da nan yaji duk rintsi ita yake muradin gani number dinta ya lalubo ya kira duk ba baya son kira direct yafi son ta Whatsapp. Suna zaune a parlour ita da zilai tana Shan mutuniyar tata farm fresh, Kira ya shigo a wayarta dake kusa da ita, tayi mamakin ganin code din Dubai har sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, batayi magana ba Shima baice komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa zilan Fadin "naji kinyi shiru koba Kira bane". Karamin tsaki Zahra tayi "wlh na daga amma naji shiru inaga ko wrong number ne dan code din na Dubai ne ni kuwa waye ze kirani daga Dubai da dai Aunty Nawwara Bata saudiyya da saina dauka ko sunje ne da mijinta tunda business man ne, Bari na kashe wata kilama ba'asan an Kira ba".. Kafin ta dauke wayar daga kunnen ta taji yayi magana cikin husky voice kada ki kashe min waya, ki bude data zamuyi magana". kit ya kashe Kiran wayar tabi da kallo a zuciyar ta tana Fadin "ikon Allah shine Kuma a Dubai ya illahiy, to Wai wannan Dan talikin waye shi lamarin fa Yana neman Zama abin tsoro fa, yace Yana yiwa kungiyoyin waje aiki ita Kuma a gefe guda wani Abu yake yi irin na Mai bada umarni Kuma bataga yanayi gaban kowa ba sai ita, kamar Ranar da taji yana Kiran zayyan da umarnin daya Bashi akan lallai ya sameshi da safe Kuma Bai karya Umarnin ba" Wayar ta kalla tana mikiwa zuwa bedroom dinta Saida ta shiga ta duba data idan Babu ta saka tunda Sam Bata taba saka data ba tunda ta Fara amfani da wayar datar data gani tayi bala'in Bata mamaki 4.5 BT ta gani sub din shekara daya ne. Cikin sofa ta zauna Tana juya wayar Bata bude datar ba, wani Kiran ne ya sake shigowa still dai nashi ne, dagawa tayi tana fadin Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". "Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, meya hanaki bude datar danace a bude?" Shiru tayi ta kasa magana,. "Wai ko sai nayi ramuwar sayen bakin da banyi bane ake min jan aji irin haka. Dan Allah kimin magana kona samu nutsuwa wlh ji nakeyi Kamar na gudo tun ba'a gama ba duk kin mamaye ko Ina na kasa komai sai tunanin ki, Ni danasanin zuwan ma nakeyi gashi sun rarraba mu wasu suna London mu kuma suka kawo mu hadaddiyar daular larabawa, shine nace Bari na kira na fada Miki Koda abinda kike bukata na taho Miki dashi tunda da kudinki a gurina" "Kudina kuma? Name nene kuma yaushe na baka". "Bake Kika bani ba ke aka bawa na manta na Baki Sai a Nan na tuna danaga Kaya irin naku na 'yan Mata". Ya fada Yana dariya. "Wai 'yan Mata". Ta fada tana Dan turo Baki irin bataji dadin Nan ba. "Au ashefa an wuce wannan stage din ko?" Ya fada da alamun zolaya. "Wato kinki bude data sai kin cinye min 'yan canjin da aka saka Mana kinsan dai ni ba iya saka Kati zanyi a kasar Nan ba, pls Dan Allah ki bude datar na ganki kona samu nutsuwa nayi aikin daya kawoni, naso ace kina gefena a wannan gurin Kinga dakina kuwa? da Hali gareni anan zamuyi honey moon irin Wanda naji su Habib suna fada idan ana hira ko Zaki biya ki taho ki sameni?" Ido ta ware kamar Yana kallonta. "Na biyoka nayi maka menene?" "Kiyi min abinda mace take yiwa mijinta ai kin gane?". "Ya Salam haba Ya Mahmud menene haka kaifa yayana ne". Wata dariya ce ta kubce Masa "A yaushe na zama Yayanki? Ki gyara zancen niba Yayanki bane, haka kawai ki haramta min abinda Allah ya halasta min idan Zaki Ware ki Dan ina dawowa labarin ze canza salo gara mu fuskanci juna ki tausaya min Kinga Sameer fa ya Zama Daddy madam dinsa ta haihu sunyi min takwara,ai gara muma mu zage dantse ko?" Dokin haihuwar da aka fada Mata ita ta Hana ta gane inda nasa zancen ya dosa, cikin nuna farin ciki tace "Dan Allah da gaske yaushe Fateehar ta haihu? Masha Allah! Allah ya Raya kace mu sai Kano ko Yaya?". "Allah bakinki ya kiyayi fada min yayan Nan tsabar kinibibi kawai yau Kika tashi dashi Wai wani Yaya kamar a kauye, kibar 'yan garinmu su Fadi Amma Banda ke wato Ni da yake ba Dan bokon kirki bane ba baza'ace min sweetie ba ko irin su my love ko Dear, saboda almajirin soro ne ni ko?" "A'a wlh ni ban fada ba, kawai dai Naga abokin Ya Abdul Hakeem ne kai ai kaima yayan ne". "To anki wayon, Kuma da kike cewa Zaki Kano ganin yaro keda wa zakuje kuma waye ze kaiki Kuma kice Mata wacece ke". "Address zata turo min Mana, Kuma maganar kaiwa sai Malam Bala direba kaimu nida mujiba wuni daya dai, Kuma
🏠