NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 102 of 136

ya fisu Shirin jiki Dan da alama yanda sihiri baya tasiri a jikin ita yarinyar shima baya yi a jikinsa, Wai wasu Mata ne guda uku a da maza biyu tsaye a kansa duk juyi sihirin baya kaiwa inda yake, yanzu Kiran da nayi miki ina son Jin tabbacin kin koma kin tabbatar da Mai gadin ya saka wannan abubuwan da Kika bashi?". Dan murmushi tayi irin na kwararrun 'yan duniya din Nan kafin tace "Haba Hajiya shekara nawa muna tare ban taba ha'intarki ba sai yau an aiwatar da komai sai jiran sakamako kawai ai wannan yaron bama Azare ba Kasar Bauchin ma gaba daya shi da ita har abada, Kuma malamin da 'yar dagon ta fada min a wani gari yake cikin kasar katsina ana ce Masa Bakiyawa tace idan na shirya zata rakani garin iyayen mijinta ne daya rasu". Hake sukayi ta kullawa da kwancewa,Asabe nata Kara zugata akan ko nawa zata kashe kada ta Bari Ammah da 'yar zumunta su fisu komai, tunda ta Nan take samun nata rabon a jikinta idan Bata encouraging dinta itama zata rasa income nata. ** Tun bayan ganawa da Bakinsa Mahmud ya shige bedroom ya Haye gado yaso ya Kira Zahra suci gaba da Hira Amma saiya fasa Dan yasan yanzu gari ya waye sosai a 9ja Bari ya kyaleta sai dare hirar zatafi tafiya yanda yake so. Bai tashi ba sai lokaci sallah, wanka yayo ya saka kananu Kaya yayi sallah yana cikin addu'a yaji ana knocking din kofa umarnin shigowa ya bayar Sameer ne ya shigo Bakinsa yaki rifuwa. "Barka da Rana". Sameer ya fada Yana mikawa Mahmud wayar hannunsa. Hannu yasa ya karba yaga menene yasa shi irin wannan murmushin. Wani fine Baby ya gani nade cikin farin towel na jarirai fari sol. Kallon shi Mahmud yayi Yana neman Karin bayani. "Takwaranka ne madam ta haihu jiya cikin dare". Cikin madaukaikin mamaki Mahmud ya kalli Sameer "are you serious?" Kai ya gyada Masa Yana Fadin " yes sir". Mahmud sai juya wayar yake Yana Kara kallon babyn. "Masha Allah, my friend Allah ya Raya mana, amma me yasa ka taho ka baro yarinyar mutane a watan haihuwarta ai sai iyayenta suga rashin kyautatawar ka ga 'yarsu". Shafa Kai yayi Yana Dan murmushi "ba wani Abu,idan na zauna me zanyi musu duk abinda ake bukata nabar musu". Wani kallon baka da lfy Mahmud yayi Masa "an fada maka Bata bukatar kulawar ka ne a irin wannan lokacin?" wlh Dana San lokacin haihuwata yayi ba inda zakazo Kuma yanzu ka nemi visa ka koma gida daman Nan anyi clearing din komai U A.E din naji da komai kawai, naji kace takwara na nayi zaton sunan Abban koko za'a saka masa?". "Ai umarninsa ne yace nayi masa huduba da sunan ka". "To Masha Allah! Godiya ta har gida zanje na yiwa Abban tafi karfin ta waya Allah ya Raya Mana Mahmud yayi Masa Albarka, kaje ka Fara shiri tun yanzu ka shiga kasuwa kayi musu abinda ya Dace". "In Sha Allah". Godiya Sameer yayi ya nufi kofa Yana fita alarm na shigo Masa Wanda Saida ya girgiza shi baya yayo yana Murda kofar ze dawo ya jira yayi locking dinta, dariya yayi Yana Fadin "manya gatan Wasa, Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi". A Ranar cikin dare suka bar Kasar su duka Sameer yayi Nigeria shi Kuma Mahmud ya nufi U.A.E . ✨✨✨ AUREN HUCE HAUSHI. MAMAN FATEEMAH. Page 34 AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu. 'yan uwa muna barar addu'oin ku bisa rashin abokiyar aiki da mukayi ECCD co-ordinator ta KIRIKASAMMA LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE muna rokon Allah s.w.a ya jikaanta yayi Mata Rahama yasa Aljanna makomarta tare da Iyayen mu da sauran Al'ummar musulmi Baki daya ya Raya abinda ta Bari ya Albarkaci bayanta. ______ Misalin karfe uku da rabi jirgin sun Mahmud ya sauka a DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT (DXB) cikin amincin Allah, yana cikin kusan rukunin mutanen karshe a fitowa, yana sanye da suit ash colour na kamfanin Armani hannunsa sanye da ogogo Rolex, baya tare da komai sai jakar laptop dinsa a hankali yake gangarowa cikin takunsa na cikakken namiji me ji da lafiya da karfi, direct gurin da taxin airport suke ya nufa, baya bukatar asan yazo garin so yake ya tantance wata jimurda da aka hada, taxin ya shiga saida sukayi balance a titi sannan ya fadawa direban ya kaishi JW moritte marquis hotel cikin harshen larabci,sunyi tafiya mai tsayi kafin su karaso hotel din, bashi da matsalar kama daki dan tun yana china yayi booking din dakin ta online, katin dakin kawai ya karba ya koma waje yin 'yan uzurirrika daga baya ya nufi ciki, wanka ya fara kafin yayi order abinci, sai da ya gama komai sannan ya kwanta dan yayi matukar gajiya, yaso kwarai ya kira 'yar gidansa amma yana son su tattauna sosai, sai yanzu yake jin haushin wani ra'ayin nasa badan haka da suna tare da ita suna hutawarsu, yanzu kadaicin rashinta da be dameshi ba, wlh da beyi alkawari ba da visa zesa ayi mata ta sameshi a nan saboda hotel din yayi masa, yana daga cikin lattest hotels na duniya be taba sauka a wani hotel ba a dubai sai BURJ AL ARAB JUMAEIRAH dakinsa parmanent ne duk mai hulda dashi a dubai nan suka sani, duk da yana da gidaje a kasar shi be fiye son yakai abokanin bussiness dinsa gida ba. Wanna
🏠