rki gidan Yallabai muhmudu, ubangji ya kawo Mana kazantar daki Amma Bata shara ba".
Dan murmushi Zahra tayi tana Fadin kin jiki Aunty zilai ni kibar wannan maganar gaskiya, Ina kwana".
Ta fada tana komawa parlour biyota zilan tayi tana Fadin "yau fa abinda kikafi so nayi Miki" ta fada tana kokarin bude warmers din abincin,waina ce manya irin tasu ta Bauchi sai Kuma pepper soup na cow leg da kunun gyada Wanda yaji Madara.
"Wow! Amma aunty zilai kin gama min komai na gode" ta fada tana janyo plate din da zata Zuba, zilan ce ta karba da sauri tana fadin "haba dai gani a tsaye Zaki Zuba abinci da kanki to meye amfanina".
Rike plate din Zahra tayi tana fadin "Dan Allah kada muyi haka dake Ina laifin dafawar ma ai dadin sai yayi min yawa, Ina kwance Ina barci kina ta faman dawainya sannan Zuba abincin ma Sai anyi mini".
"To menene ai aikina ne".
"A'a wlh ba Aikinki bane a Nan cewa akayi ki tayani Zama kwarai".
Ta fada tana bude abinci akan dole zilan ta hakura ta koma kitchen inda take wanke waken alale zatayi musu cikin abincin Rana.
Bayan ta Gama yin break din parlour ta dawo ta kunna tasharta mbc max tana kallon wani film da sukeyi, tana Nan zaune taji karar door bell ta tashi ta nufi kofar ta bude yara ne kamar 'yan sheka sha uku haka suna rike da manyan ledoji kowa guys biyu a hannunsa.
Cikin girmamawa suka gaishe da Zahra tare da fadin "gashi inji Baba Malam yace a kawo Miki Kuma Yana gaishe ki".
Suka fada a tare, hanya ta Basu suka shigo da kayan ciki sai raba Ido suke suna kalle-kalle.
"Sannunku ku aje ku zauna, na gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi, a me kukazo ne?". Dayan da yafi magana yace "Yaya Habibu ne ya kawo mu Yana kofa gurin wancen mutumin" ya fada Mata.
"Masha Allah". Ta fada tana Kiran zilai, da sauri ta fito tana fadin. Gani uwar dakina".
"Kaya ne Baba Malam ya Aiko aka kawo min".
Gurin da kayan suke ta karasa tana fadin "Masha Allah 'yar gatan Baba malam, an gode madallah sai a Basu tukwaici". Zilan ta fada tana kokarin bude ledar dake kusa da it's.
"To Bari na dauko musu ki shiga da kayan ciki sai ki zuba musu abinci a robobin nan na take away Wanda aka kawo saboda zuba kayan gara Dan kada su zauna yau Ranar wanki da 'yan aikace aikacensu ne," ta fada tana yin gaba.
Bedroom dinta ta shiga ta duba Sam ba kudi a gurinta, Dan Jim tayi sai Kuma ta bude bedside locker ta dauko keys din dakin Mahmud daya Bata.
Kamar' Mai tsoron wani Abu kada ya kamata ta bude dakin, komai tsab hatta kamshinsa Yana dakin kamar yanzu ya fesa yabar dakin,limshe ido tayi tana shakar kamshi, komai na dangin electronic a kashe yake a dakin a hankali ta ratsa ta nufi inda ya nuna Mata yace idan bukatar wani Abu ya tashi ta dauka, locker din ta janyo 'yan dari biyar ne da dubu dubu ko wanne rapper uku uku 5k kawai ta Ciro daga cikin 'yan 1k din ta mayar ta rufe tana tunanin Kiran magaji yazo ya Ciro Mata kudin saboda irin haka Bata bukatar komai tunda ba abinda ba'a aje Mata ba wani abun ma Sai a shekara Bata nema ba.
Bayan ta kawo musu sukayi gdy suka fita, gurin Aunty zilan Zahra ta shige.
***********
Karfe biyar na yamma jirginsu Ammi ya sauka a sokoto, lokacin data fito Harabar da masu jiran saukar 'yan uwansu suke,Habu direban Hajiya Inna ne ya nufo Ammi da sauri Yana fadar "barka da sauka Hajiya, nine Hajiya Inna ta turo nazo na tare ki".
Ya fada Yana karbar karamar luggage din dake hannunta .
"To sannu da kokari nagode kwarai".
Direct gidan Hajiy innar ya nufa da ita da yake unguwar mabera, duk yanda Abban su Mahmud yaso ta zauna part dinta daya Gina Mata Amman ta nuna tafi son daga nesa dai.
Har kofar falon Hajiya Malam Habun ya kawo ta bisa umarnin Hajiya, lokacin da ze tafi dauko ta fada masa ya kawo Mata ita har kofar parlour.
Kafin ta fito Yara qananu guda biyu suka fito da gudu daga parlour wanda yayi dai dai da fitowar Ammi daga mota da gudu suka karaso, suna fadin ga Ammi! Ga Ammi" suka fada jikinta a tare suna fadin "Ina kikaje Ammi Baki tafi damu ba mukayi ta kuka".
Kansu ta shafa tana fadin "sorry My babies ba gashi na dawo ba, ai kuka Kuma ya Kare"
Hannunsu ta rike ta nufi kofar da suka fito, sun riketa ram kamar zata gara guduwa ta barsu.
A zaune Ammi ta samu Hajiya inna tana lazumi, gurinta ta nufa cikin takunta na nutsuwa tana fadin "Hajiya barkanmu da yamma".
.
Ajiye tasbahar dake hannunta tayi tana kallon Ammi wadda tayi wani tas da ita, bazaka taba cewa ta aje kamar' Mahmud ba, idan aka jera su mafi yawan mutane zasu ce yayarsa ce. Gefen Hajiyar ta zauna daga kasa wannan d'abi'ar ta ce Bata taba Zama a kujera matukar Hajiya na Kan kujera, cikin ladabi irin na D'a da uwa Ammi ta gaishe da Hajiyar Tana fadin "Masha Allah zainabu kin cika Alkawarin da Kikayi min Koda kuwa ba a lokacin bane nagode kwarai da gaske Allah ya Albarkaci zuciyar ki ya Baki rinjaye akan duk masu son su tagayyara Miki zuri'a, ki Kara hakuri akan Wanda kike yi lallai duk Wanda akace yayi hakuri an Bata masa ne, Allah yayi Albarka yanda kike min biyayya kema Allah ya Bak