NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 136

you shawara suka shiga dakin Auntyn saboda Nan ne baza'a shigo ba. Bakin gadon ta zaunar da Zahra ita Kuma ta janyo stool ta zauna har lokacin Bata saki hannunta ba,tana Jin yanda ilahirin jikinta yake rawa. Hannun ta Kara jimkewa cikin nata tana fadar. "Cool down Mana bestie haba take it easy, kada ki tada hankalinki Taya Zaki kama maganar faruq kinsan dai ba wani hankali ya Gama Masa jiki ba". Kai ta shiga girgizawa cikin muryar Kuka tace. "Wallahi Saji akwai matsala kema Kuma kin sani sai dai kik'i fad'a idan ba matsala Ina su Maryam da mukayi dasu zasu zo tun kwana ukunda suka wuce Ina shi kanshi uban gayyar ina su Deeni dasu Aliyu, kowa ka Kira sai dai kaji switch off baka haka ba". Ta fad'a tana fashewa da wani irin Kika.mai taba zuciya. "Kiyi shiru Dan Allah kada ki janyo hankalin mutane Mana kinga ga Amatu can zataji dasu ki nutsu har muji meye gaskiyar maganar Mana". "Ki barni nayi kuka wallahi na gaji nikenan kullum matsala daga wannan sai waccan na rasa a Ina matsalar take ni wallahi bana son kowa ma a kyakeni haka Nan bana son auren, bana so wallahi ni nagaji Allah Jordan zan tafi bazan zauna ba, bazan Kara Zama a kasar nan ba". Ta fusge hannunta daga na Sajida ta yunkura ta tashi ita dai Sajida Bata San ta Yaya akayi ba sai ganin Zahra tayi ta kifa kan gadon tana wata irin fuzga da gudu ta karasa kusa da ita tana jijjigata tana fashewa da kuka tana fadin "ki tashi Dan Allah wayyo Allah na". Baba Tabawa ce ta bude kofar ta shigo, Dan tunda tana kusa dasu Faruq ya shigo da wannan maganar duk da tasani Dan Aunty Hasana Bata rufe Mata komai ba ta fad'a Mata tun jiya, shi yasa data ga sun nufo dakin hankalinta ya kasa kwanciya ta biyo su tasan koya Sajida zatayi Mata kalamai ba kamar ita ba tunda abinda babba ya hango yaro koya hau iccen rimi bazai gano ba. Turus tayi tana kallon Sajida dake Kuka bil hakki tan jijjiga Zahrar. Da sauri ta karaso tana fadar "ke 'yan Nan menene haka?". Hawaye jage-jage Sajida ta dago tana fadar "wlh Baba Tabawa kawai tana kuka tana maganganu tana tashi kawai sai Naga ta yanke jiki ta Fadi?. Wani ruwa Baba Tabawar ta dauko a kan bedside fregde din Nan ta zubawa Zahrar a fuska Amma shiru ta Kara watsa Mata Nan ma shiru cikin tashin hankali ta lalubo Yar wayarta rakani toilet ta mikawa Sajida "ungo maza Kira min Aunty zakiga an saka Maman Ali yi sauri". Bugu biyu Auntyn ta dauka tare da sallama, gani Sajida ta rasa me zatace ne yasa ta mikawa Baba Tabawa wayar. Can Kuma tana ta faman" hello Baba" Abinda taji kenan lokacin data Kara wayar a kunne cikin sauri Baba tace "yi sauri ki turo a Kai Zahara'u asibiti wallahi gata Nan a suma min yayyafa ruwa a banza". Bata jira taji me za'a fad'a ba ta kashe wayar. Abdul Hakeem Aunty Hasana ta lalubo a waya lokacin suna tsaye shi da Mahmud suna magana wayar Abdul Hakeem dince ta Fara ringing Sunan Aunty Hasana ya gani ya daga har zai Fara Mata abunda ya saba ta tsayar dashi tana fadin "Dan Allah maza kaje gidana ka dauko Zahra ku wuce asibiti mu hadu a can wai Suma tayi" Kit ta kashe wayar. "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yake ta Nanatawa da sauri Mahmud ya tambaye shi "lafiya meya faru". "Bari kawai ba komai Ina zuwa yayi gaba da sauri jikinsa har rawa yake Yana tafe Yana laluben key din motarsa. Da sauri Mahmud ya biyo bayansa' Sam baiji key din ba sai daga baya ya tuna tana hannun mustapha yaje gari ya dawo. Tsaki yayi daidai lokaci da Mahmud din ya karaso Yana fadar"Dan Allah Wai menene Naga duk a rude". "Bari kawai Wai Zahra ce ba lfy zan kaita ASIBITI". Kallon yayiwa Abdul Hakeem din kafin yace "shine Kuma zakaqi fad'a min". Hannu yasa ya yafito Sameer, cikin bada umarni yace "Dauko motar can kuje da Abdul zaku Kai madam asibiti". Ya juya ya koma gurin su Habib. Har sukaje gidan Auntyn Abdul Hakeem Bai daina mamakin Mahmud ba, yanayin yanda yayi maganar kawai kasan da abinda ya taka umarni fa ya bada, su dai a zahiri ai Sameer ne uban gidan Mahmud tunda kowa yasan aikin NGO's ya kawo shi garin har suka hadu da Mahmud din suka dauke shi yake musu aiki a sauran makarantun tsangayun na cikin gari Dana kauye. Da sauri Abdul Hakeem din shiga gidan Auntyn ta kofar baya gurin kitchen ya shiga koridon dakunan barcinta. A tsaye cirko cirko ya samu su Baba Tabawar har lokacin numfashinta Bai dawo ba. Da sauri ya karasa gaban gadon yasa hannu ya dauketa kamar wata Baby yayi waje da ita. Sajida da Baba Suka rufa Masa baya. Da sauri Sameer ya bude Masa seat din baya ya sakata Sajida ta shiga ita da Baba shima Abdul Hakeem ya shiga gaba da gudu Sameer ya fizgi motar. Saida ya daidaita a titin sannan ya kalli Abdul Hakeem din "ina muka nufa?". "F.M.C zamuje tunda yafi kusa". Nan da Nan aba karbeta likitoci suka rufu a kanta, suna Nan tsaye Aunty Hasana tazo ita da Inna maimuna sai Hajiya kaltume. Suma tsayawa sukayi a gurin Baba Tabawa tana maida musu yanda akayi ita dai Sajida ba baka sai sharar hawaye take. Su Abdul Hakeem suna suna gefe daga zuwansu Mahmud ya Kira akai sau biyar idan y
🏠