NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 105

Sakina Yazid (Innar su Amal) Yayi ‘yar dariya ‘Babu matasala fa, akwai dai maganar da nake so muyi. Zan iya zuwa, minti talatin kawai ya isa.’ ‘Ok, ina jiranka duk da dai na kusa tashi.’ Ya ajiye wayar ya mike ya dauki mukullan motarsa ya kama hanya. ……. Yana sane yaki ya kirawota da ya sa don so yake ya shiga ya sameta a office din nata, don haka bayan ya ajiye motarsa sai ya fito ya shiga gidan talabijin ya tambaya. Ba tare da bata lokaci ba aka nuna masa office din nata. A hankali ya kwankwasa kofar, daga ciki muryarta ta bashi amsa ‘Shigo a bude kofar take.’ Ya tura kofar ya shiga da sallama. Tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya wadda take gefe guda, da jakarta a gefenta tana ta danna waya; da alama ta gama shirin tafiya gida. Bayan ta amsa sallamarsa ya mayar da kofar ya rufe sannan ya karasa yayi kansa mazauni a kujerar da take kusa da wadda take zaune a kai. Bai san dalilin da yasa ganinta ya saka shi jin dadi ba amma dai ya san ya ji dadin ganinta. Cikin girmamawa ta gaisheshi kamar babu wata damuwa a tsakaninsu. Bayan ya amsa tace ‘Allah ya sa dai ba wata matsala don tunda kace zaka zo nake ta tunani.’ Yayi murmushi yace ‘Babu wata matsala, kawai dai ina son ganinki ne.’ Ta dan yi gajeren murmushi tace ‘Uhm, to gani.’ Yayi dariya yace ‘Kamar dai kina korata.’ ‘Ba korarka nake ba, kawai dai ina son na tafi gida don wallahi na gaji.’ Ya gyara zama; yarasa ma ta inda zai fara domin ganinta ya goge masa duk zantukan da ya tsaro zai zo ya gaya mata. ‘Yara suna kewarki.’ Ya fada bayan ya gama nazarin ta inda zai fara. Nan da nan murmushinta ya kara fadi, tace ‘Allah sarki ni da Hammad ma muna kewarsu. Don ma Yaya Habib yana zuwa gidan Mommy yana gaishemu.’ Ya girgiza kai domin Habib bai taba gaya masa yana zuwa wajen Khadeeja ba, bai ma taba yi masa maganar Khadeejan ba tun bayan da suka rabu. ‘Ya Hammad? Baya kukan makaranta?’ Ya tambaya. ‘Baya yi, ka san ya hada wayon yayyinsa gaba daya.’ Ta fada tana dariya. Suka yi shiru na dan lokaci; ita duk ta kosa domin so take ta tafi gida yayinda shi kuma ya gyara zama yana kwaso hira. PAGE 236 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Khadeeja.’ ‘Na’am.’ Ta amsa tana kallonshi. ‘Wai me yasa kika ce na sakeki?’ ya tambaya yana tsareta da ido. Ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake yi masa wannan murmushin nata wanda yake dauke da ma’anoni daban daban tace ‘Right question at the wrong time; amma dai zan baka amsa.’ Ta sunkuyar da kai a daidai lokacin da murmushin fuskarta ya gushe, ta dago suka sake hada ido sannan ta gyara zama tace ‘Gajiya nayi Musatapha. Ka san idan mutum wanda bai iya swimming ba ya fada ruwa to zai yi ta kokarin ganin ya fita da rai ko, amma duk dadewa zai gaji. To haka ce ta faru da ni. Soyayya ce ta saka na aureka, amma idan dai ba na manta lissafin ba tun a shekarar farko na rasa soyayyarka. Haka na dinga kokawar janyo attention dinka ko zaka fahimceni amma baka ko kalli inda nake; kai dai abinda kake so kawai shi kake so. Na hakura ina zama da kai a haka saboda I was ok with just sleeping behind you every night; sai kuma ka dauko aure. Duk wani abu da nake so daga wajenka a lokacin ka dauka ka bata ina kallo. Haka na cigaba da kokawar samun attentin dinka, ina kokarin ganin kayi mana adalci amma hakan bai samu ba. Na tuna tun ina ni kadai ma ka fara kasa yi min adalci to balle yanzu mun zama mu biyu; ni da rabin ranka. So I gave up, ba zan iya ba, na gaji da fadan da bashi da ranar karewa don na gane bana ma gabanka. Shi yasa na nemi saki kuma Allah ya taimakeni ka bani kuma ka barni har na gama idda.’ Idanuwansa suna kan fuskarta har ta gama tayi shiru, ya cije lebe yace ‘Kuma baki gaya min ba Khadeeja? How did I not see all this?’ Tayi dariya tace ‘Da wanne yaren zan gaya maka?’ Suka sake yin shiru na dan lokaci. ta danna wayarta ta kalli agogo sannan tace ‘Time yana tafiya, wallahi so nake na tafi gida don na gaji.’ ‘Oh, sorry’ PAGE 237 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal Suka sake yin shiru na dan lokaci sannan yace ‘Khadeeja yi hakuri mu mayar da aurenmu, in sha Allahu haka ba zata sake faruwa ba.’ Ta mike tsaye tana dariya tace ‘Kayi hakuri Mustapha amma aure ba zan sake yi da kai ba, babu wannan zance don Allah kada ka sake yinsa. Shekarun da muka yi Allah ya amfana su kuma Allah ya sa kaffara ne amma kada Allah ya maimaita mana.’ Ya dafe kansa da hannuwansa biyu na dan lokaci sannan ya sauke hannuwan ya mike tsaye. Ta bude kofar ya fice sannan ta biyo bayansa suka fito daga office din. Suka jero suka fito harabar office din. Nan suka tsaya yana ta faman lallabata ta bari ya kaita gida amma ta ki; yana ji yana gani ta tare taxi ta hau. Sai da ya tabbatar ta zauna a bayan motar sannan ya zagaya ya
🏠