a fice.
Yana zaune a tsakar gida wajen Baba maigadi Shukra taje ta kirawoshi. Yana shigowa ya ci karo da wankin a zube a bakin kofa; tabbas wankin sun fi kala biyar. Yana shiga cikin parlor din kafin yayi magana Naja da take tsaye tace ‘Gasu nan kaje ka wanke, kuma wallahi idan basu fita ba sakewa zaka yi har sai sun fita.’
Ta juya ta haye sama ta barsu a nan shi da kannensa.
Ya juya ya dawo ya tsaya a kan wankin yana kare musu kallo yana tunani; tabbas ba zai yi wankin nan ba, ko da kuwa kala dayan ta bayar kamar yanda tace. Kuma yanda yaga a gaban Abban tace kala daya ne kuma ta dauko kaya da yawa haka ta bashi ya san ta shirya wata makarkashiyar.
PAGE 226
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya san ba lallai Abbanshi ya saurareshi ba saboda tana gabansa tana tsara masa zance, kuma ya san idan har yayi wannan wankin to ta sami damar da zata mayar da shi dan aikin gida kuma ba zai yi ba. Haka ya kewaye ya fice ya bar wankin a nan inda ta ajiye su.
………
Suna sama ita da maigidan suna ta hirarsu cikin kwanciyar hankali, sai waje karfe tara sannan Anti Wiyya ta fito daga dakin baki ta ga wankin. Tayi matukar mamaki musamman da ta tambayi Afaf ta tabbatar mata Habib din ya fice bai dauki wankin ba. Nan ta koma daki ta kirawo Naja a waya wadda ta sauko, ta nuna mata wankin sannan tayi mata bayanin cewa a nan ya fice ya barsu.
Yaran suna kallo ta tsuguna ta tsince kayan ta bar kala daya da hijab guda daya sannan Anti Wiyyan ta koma daki ita kuma ta haye sama.
Jimawa kadan Mustapha ya sako yana tambayar Afaf ina kaninta.
‘Abba ban ganshi ba, ficewa kawai yayi ba tare da yace komai ba.’ Ta bashi amsa.
A fusace ya murda kofar dakin Habib din ya shiga yana kiransa, sai dai ga mamakinsa Habib din baya cikin dakin. Ya fice wajen Baba Maigadi inda ya tabbatar masa bai san inda Habib yake ba, ya kara da cewa ‘Bana jin ma fita yayi, don tun da aka ce ya zo kana kiransa ban sake ganin gilmawarsa ba. Sai dai ko da ina sallah ne ya fice ban sani ba.’
Ya koma cikin gidan ba tare da yace komai ba.
Yana shiga parlor din ya dubi kayan yace ‘Nasreen zo ki kwashi kayan nan ki mayar mata, yayan naki zai zo ya same ni.’
Ya haye saman inda ya tara da Naja a zaune a parlor ita da Rukayya, ya sami waje ya zauna sannan ya dauki wayarsa ya dannawa Habib kira. Ba karamin mamaki yayi ba da yaji wayar Habib din a kashe, sai dai yayi tunanin kashe wayar Habib din yayi don ya san bashi da gaskiya. Don haka sai kawai ya sauko ya sanar da Baba Maigadi cewa idan Habib ya shigo gidan yayi masa waya.
……..
Tun yana sa ran shigowar Habib har abun ya fara bashi tsoro; yaran duk sun tafi sun kwanta har sha biyun dare ta yi amma Habib bai shigo gidan ba, gashi sai kiran wayarsa ake yi a kashe. Yana son ya kirawo Hajia ko Habib din yaje can amma kuma baya son ya daga musu hankali.
PAGE 227
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid
A karo na babu iyaka motsin shigarsa dakin ne ya farakar da ita daga bacci, ta gyarawa Baby Maryam kwanciyarta sannan ta dubeshi tace ‘Wai bai dawo ba.’
A jigace yace ‘Eh, wallahi har abun ya fara bani tsoro. To ina Habib zai tafi? Ina ma ya sani a garin nan shi da ba wani yawo yake ba?’
Tace ‘Ya zaka ce ina ya sani yaron da yake level 1, kuma yake tafiya makaranta da kansa. Ai yanzu ba kamar da bane, tsaf ya san ko ina.’
‘To ina zai tafi a wannan daren? Gashi Baba Maigadi ma yace ko fitarsa bai gani ba kuma gidan nan babu inda bamu duba ba baya nan.’
Tace ‘To ka dai yi hakur ka zo ka kwanta tunda ka ga yanzu dayan dare ta kusa, zuwa wayewar gari sai a nemoshi a bashi hakuri a gaya masa ya barwankin.’
‘Mtseww! Wai kin san me kike fada kuwa? Na zo na kwanta saboda ke kin kwanta ko?’ ya sake jan tsaki sannan ya fice daga dakin ya rufe mata kofar da karfi, rufe kofar da sai da ya farkar mata da Baby daga barci.
Ta juya a fusace tana gunguni ta dauki yarinyarta ta saka mata nono.
Yanda yaga rana haka yaga dare, yana zaune a parlor shi kadai. Sai dai idan bacci ya daukeshi yayi firgigit ya farka, ya sake buga lambar Habib amma a kashe. Yana fara jin kiran sallar asuba ya kirawo Alhaji ya sanar da shi ba a ga Habib ba.
A shirye ya fice masallaci, bayan an idar da sallar asuba ya sanar da su bacewar habib. Yana dawowa gidan ya dauki mukullin motarsa ya fice ya nufi gidan Hajia.
Suma a tsaye ya samesu cikin tashin hankali, nan suka zauna suna jira gari ya kara wayewa suje police station su sanar.
Suna zaune a parlor din Alhaji cikin tashin hankali Hajia ta dubi Mustapha tace ‘Kuma ka tuntubi kakanninsa, can gidan su Ma’u da ma ita Khadeejan ko wajensu ya tafi?’
Ya gyara zama yana cewa ‘Khadeeja dai na tambayeta itama bata ganshi ba, amma gidan mama ma ni na manta da su. Bari na kirawosu na ji.’
Kafin ya gama laluben lambar suka jiyo bugun kofa, gaba dayansu suka nufi kofar saboda Alhaji ya bada sanarwa a masallaci yayi zaton ko an sami wani labari ne.
PAGE 228