sallamarsa tace ‘Um kayi mantuwa ne?’
Kamar wanda aka farkar daga barci yace ‘No. Umm! Hammad fa? Ya kamata ya dawo cikin ‘yan uwanasa ai ko?’
A nutse tace ‘Eh haka ne, amma ka ga bai karasa shekaru hudu ba ma. Ina ganin nan da zuwa ya gama primary in sha Allahu sai ya dawo cikin ‘yan uwansa tunda tabbasa ni na san kula da yaro akwai wahala, musamman da yake ka ga Antinsu ba zama take ba tana aikinta. Ina ganin ka bar min shi duk wani abu da yake bukata in sha Allahu zan sanar maka, idan ya iya kula da kansa sai ya dawo gida.’
So yake ya ce mata hakan ba zai yiwu ba ko don ma ya bata mata rai, amma ya kasa. Tabbas yana son ganin yaronsa a kusa da shi cikin ‘yanuwansa amma kuma idan ya karbeshi baya jin Naja zata iya hadawa da shi ta rike, don yanzun ma kullum cikin korafi take a kan yara suna gajiyar da ita. Gara ma ya bari ta rike shi in Allah yayi da ragowar zaman sa koma tare. ‘Um hakane, to babu damuwa. Sai goben kenan.’
‘Ok, Allah ya kai mu goben.’
……....
Bata taba tsammanin Mustapha zai bar mata Hammad da sauki ba, don haka ma da yayi saurin amincewa da maganarta sai ta ji wani dadi marar misaltuwa; domin ta hango wahalar da zai sha idan ya koma gidan; zama zai yi kamar maraya. Tunda su Shukra su hudu ne, Rukayya kuma uwarta tana gidan sai shi kadai wanda ba shi da uwa bashi da dan uwa a gidan.
A hankali ta mayar da wayar tata ta ajiye a kan teburinta. Ta sunkuyar da kanta ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta sannan ta zuba fuskarta a tafukan hannunta; ta tuno lokacin da suna soyayya da Mustapha kafin suyi aure. Wai ina soyayyar nan ta tafi ne? ya barta ita kadai tana ta dakon soyayyarsa har tsawon shekaru takwas?
PAGE 221
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tabbas ta sha wahala a gidan Mustapha; ba wai wahalar jiki ba don wahalar jiki ta san abinda ta yi bai wuce abinda matar aure zata yi ba. Sai dai wahalar zuciya da ta sha; kulawa da tausaya tare da kauna da zuciyarta take bukata daga wajen Mustapha sune bata samu ba. Ko su din ma ta hakura da su tana zama haka tunda ko babu komai tana kallonsa a matsayin mijinta kuma suna kwana tare. Amma daga lokacin da ya auro wata kuma ya ke bata kulawa da kauna wanda ita ya kasa bata daga lokacin ta yanke kauna daga zaman gidan Mustapha.
Ba zata ce bata jin zafin rabuwa da shi ba domin tabbas ta san ko babu kauna akwai sabo, amma tabbas ba zata sake komawa gidan Mustapha ba. Domin tayi sujjada ta roki Allah kada ya sake hadata zaman aure da Mustapha. Da farko ta fara jin haushnsa amma daga baya sai taga jin haushin babu wani amfani; ko babu komai dole ta yiwa Hammad kara ta girmama mahaifinsa.
Ta sake share kwallar da ta taru a kwarmin idonta, ta kalli ruwan hawayen da ta lakata a hannun nata; to kukan me take a halin yanzu? Ta zata ta gama kuka a kan Mustapha. Tayi murmushi ta sake goge kwallarta; ta san ba zata iya goge Mustapha daga cikin tarihin rayuwarta ba amma tabbas bata fatan sake rayuwa irin wadda tayi a gidansa. Ta goge fuskarta ta fice ta nufi cikin studio inda zata gabatar da labarai.
......
Ba a fi sati daya da kwashe kayan Khadeeja ba Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya sake fentin saman aka gyara ta kwashe kayanta ta koma. Yaran kuma gaba daya ta tattarosu ta dawo da su kasa tare da masu aikinta guda biyu. Dakinta da parlor dinta nan ta mayar dakinsu Afaf, suna ji suna gani babu yanda suka iya. Shi kanshi Mustapha abun bai yi masa dadi ba amma ya kasa magana; yana matukar mamakin abinda ya sa baya iya hana Naja abinda take so a ‘ya kwanakin nan.
Cikinta yana cika wata tara ta sake haifar ‘yarta mace, haka ta dage ta shirya taron suna fiye ma da wanda ta shirya a haihuwar Rukayya. Aka sakawa yarinyar suna Maryam.
PAGE 222
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Washegarin suna su Anti Wiyya da sauran dangi suka soye naman suna suka gyara koma, sannan suka tafi suka bar Anti Wiyya ita kadai wadda zata kara kwana biyu saboda tayata jego.
Tana zaune a parlor din sama Anti Wiyya ta shigo da sallama, bayan ta amsa ta karasa ta zauna a kusa da ita sannan tace ‘Wannan mai wankin naki gaskiya ya iya wulakanci, sai da ya fuskanci ana taro sannan ya gudu. Ni dai wallahi ko kayan sakawa gobe bani da su duk sun yi datti, ga shi duk jikina ciwo yake balle na zage na wanke kuma ‘yar aikinki ma dai ta fini gajiya.’
‘Ai mai wankin nan yayi wa kansa, in sha Allahu gobe Abban Rukayya zai samo mana wani mai wankin kowa ya huta.’ Ta fada tana gyara zama.
Anti Wiyya tace ‘Don ma dai ‘yayanki basa moruwa ne in banda haka ga Habib can a kasa yana wanki ai da ko kala daya ne ya wanke min.’
Ta gyara zama ‘Au ai ban san ma yana gidan ba kwaso kayan duka bari na kirawoshi zai wanke miki yanzu.’
Ba tare da bata lokaci ba ta juya ta koma kasa inda ta kwaso kayan nata yayinda ita kuma Naja ta kwalawa Afaf kira ta sakata ta turo Habib.
Kusan a lokaci guda suka isa parlor din, shi ya tsaya daga bkin kof