NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 91 of 105

suka yita hira a wajen Hajia. Duk da ya gaya musu ba yau zai tafi da su ba amma Shukra ta kafa a kan ita a ranar take son ta bisu, don haka yace su shirya tare da su zai tafi. Sai bayan sallar magriba sannan Alhaji ya dawo, bayan sun gaisa suka cigaba da hirarrakinsu. Alhaji yace ‘Yauwa, ya wajen Khadeeja kuwa? Kun yi magana ne?’ Yace ‘A’a ni ban nemeta ba kuma ba zan nemeta ba Allhaji, itace fa tace na saketa kuma na saketan, taje ta dana zaman gidan.’ Alhaji ya dan bata rai yace ‘Kai! Ba a yiwa mata haka, idan jira kake ta nemeka to ba lallai ta nemeka ba gara ma kaje idan da wani abu ka yiwa iyayenta bayani su yi mata fada ka mayar da aurenta.’ Ya jijjiga kai ‘Alhaji ni ba inda zan je, idan tana son auren nata zata nemeni tunda ai da kanta ta nemi sakin.’ Haka Alhaji ya saka shi a gaba yayi ta yi masa nasiha, daga baya yayi musu sallama ya kwashi yaransa suka wuce. ……….. Ba shi kadai ba hatta yaran ma saida suka gane bata ji dadin dawowarsu a ranar ba, haka dai suka gaggaisa suka yi mata sannu zuwa kowa ya shiga harkarsa. Inda Allah ya taimaketa ma shine ya siyo musu abincin dare. Ta rigashi kwanciya saboda gaba daya bata ma jin dadin jikinta, sai da suka gama hira shi da yaransa sanan ya rufe gidan kowa ya tafi ya kwanta. PAGE 216 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Motsin shigarsa daki shi ya tasheta daga bacci, sai da ta bari ya gama shirins ya kwanta sannan ta gyara kwanciya tace ‘Kai da muka yi da kai ka bar yara sai mun huta shine ka taho da su?’ Ya gyara kwanciyarsa yace ‘To sun ce zasu taho, suma fa ba dadin zaman suke ji ba a wani wajen kin san kowanne yaro ya fi son gidansu.’ Ta kula idan dai a kan yaransa ne ba zai saurareta ba don haka ba tare da ta ce komai ba ta juya masa baya ta cigaba da baccinta; amma dai ta san tabbas dole ta dauki mataki don babu yanda za ayi ta bari ya kori kishiyarta kuma ya mayar da yaransa kishiyarta. dole ta dauki mataki. Sai da tayi sati da dawowa sanna taje gidansu ta taho da Rukayya, don ko ‘yan gidan nasu ma da zasu zo musu sannu da zuwa cewa tayi kada a zo da ita don idan ta zo ba zata yadda ta koma ba. Bayan ta gama hirarta a gidan ta wuce gidan Anti Wiyya; nan suka zauna tayi mata bayanin ayyukan da ka yi mata, sannan ta bata wasu layu guda biyu tace ‘Gasu nan hatimi ne aka rubuta da ayoyin Allah, ki sami waje ki konesu kurmus sai ki zuba masa tokar a miya. In dai ya sha miyar nan to ba zai sake yi miki musu ba. Wannan aikin bana haufisa kamar yankan wukane sai dai idan baki aikata ba.’ Ta karba ta mayar cikin ledarsu ta kulle ta jefa a jaka tana cewa ‘Ai dai kin ce ayoyi ne ko?’ Tace ‘Wallahi ayoyi ne, ke malamin fa har almajirai gareshi suna karatun allo. Ai idan kin haihu zamu je ki gani da kanki idan har kina da wata matsala.’ ‘Hmm! Ai dole ma nayi Anti Wiyya, daga dawowarmu ya fara neman ya nuna min iyakata a kan yaransa, gashi su baka isa ka saka su aikin komai ba sai dai kai ka kare a hidimarsu. Ai yau din nan zan aikata wannan layun kowa ya shiga hankalinsa. Ko nan ma fa da zan taho shi so yayi na taho da su wai saboda kada na barsu su kadai, ki ji don Allah sai kace wasu jarirai.’ ‘Ya zata kema Khadeejan ce.’ Suka yi dariya gaba daya. Sai gefin magriba sannan ta dauko Rukayya suka dawo gidan. Tana zuwa tadora abincin dare imda ta dafa tuwo miyar kuka. PAGE 217 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tsaf ta hade tokar layun nan ta juye masa a miya ta juya komai ya shige, tayi sa’a kuma ya sami tuwon nan yayi masa cin koshi. A hankali ta fara ganin kyawun aikin da Anti Wiyya ta yi mata. Cikin wata daya da dawowarsu ta tattare kayanta ta koma sama part dinshi, bata son tayi maganar part din Khadeeja sai ta bari wata uku ya cika saboda kada ma ta tuna masa yaje ya dawo da ita. Yanzu ta samu idan suna sama shi da ita ta hana yaran hawa kuma ya kasa yi mata magana. Ta san bai ji dadi ba don yana nuna mata a fuska amma wannan ba damuwarta bace, kuma idan shi ya zauna a kasan da zarar ta kirawoshi haka zai tashi ya bi bayanta su koma saman da shi da ita da Rukayya, sauran yaran suna kasa. Sai dare yayi idan zasu kwanta ne suke hawa saman da yake dakinsu yana can. Suna hawa sai ta kadasu su wuce daki su kwanta. ……….. Tun ranar da ta koma gida take lissafi, duk da dai tana jini a lokacin amma dai sai da ta lissafa jini uku, kuma jiya ne ranar da ta fita daga jini na uku bayan rabuwarsu da Mustafa. Tana zaune a gefen karamin gadonta wanda shine dai gadonta tun kafin ta auri Mustapha, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana tunanin yanda rayuwarta zata cigaba; tabbas ta ji dadin rabuwa da Mustapha, bata yi nadama ba kuma ba zata koma ba. Domin ko babu komai yanzu ne ta tabbatar tana cikin nutsuwa. Duk wani abu na kulawa da Hammad yake bukata zata iya yi masa don haka ba zama ta nemi Mustaphan da maganar Hammad din ba saboda ma kada yace ta bashi yaronsa. Fatan ta daya Allah ya
🏠