lo. Ya dubi khadeejan ya sake cewa ‘Deeje me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
Ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake sunkuyar da kai tace ‘Baffa na gaji, wallahi Baffa baka ga zaman da muke yi a gidan nan ba. Tun kafin ya auri matarsa Baffa dama hakuri nake, matsayina a gidan da kadan ya wuce matsayin ‘yar aiki. Kuma bayan ya aurota ma ya kara tabbatar min da hakan; duk wani abu na walwala da jin dadi da ita ake yi amma wallahi idan aiki ne da wahala Baffa ni zai kawowa kuma dole na yi. Ita kanta matar tasa haka yake saka ni nayi mata aiki babu sannu bare na gode. Shi yasa kwanaki da nace ba zan yi ba ya zo ya kawo maka karata. Wallahi Baffa a lokacin sai da nayi wata takwas ina mata aikin gida da girki da kaomia kuma kullum shi a wajenta yake kwana.’
Ta sake sunkuyar da kai ‘Na gaji Baffa, baya sona, wulakancin da yake min suna da yawa, gara na hakura kawai shi yasa nace ya sakeni.’
Ya kama hannunta wanda take wasa da shi a kan cinyarta ya kalleta suka hada ido yace ‘To ya isa, kuka ya isa haka. Ki je ki kai kayanki daki ki huta mayi magana wani lokacin.’
Ta gyada kai ta mike ta fice daga dakin.
A fusace Mommy ta bi bayanta, cikin sauri Baffa yace ‘Zo mana.’
Ta juyo a daidai lokacin da Khadeejan ta rufe kofa, ya nuna mata inda Khadeejan ta tashi ta zauna. Sai da ya dauki lokaci yana kallonta sannan yace ‘Ki bita a hankali tunda dai kin ji bayaninta. Ni da na bashi aurenta ai ba ‘yar aiki na bashi ba ko? In ya dawo ya zo yayi bayani in ya so sai a san matakin da za adauka. Shi a zaman aure ma wani lokacin hutu kawai mutum yake bukata; kada ki je ki daga mata hankali. Ki barta ta huta karshenta in ya dawo sai dai kiji da kanta tana gaya miki ya mayar da ita zata koma. Da-Allah kada ki daga mata hankali tunda dai ita ta kawo mutumun nan tace tana so ai ba laifi bane idan ta dawo tace bata son shi. Ki bata lokaci ta sami nutsuwa tukunna.’
PAGE 214
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta sauke numfashi sannan tace ‘To.’
Ta tashi ta fice ta barshi a dakin.
………
A nan gidan Hajia ya ajiye motarsa ya samar musu taxi wadda zata kaisu airport, ya shiga gaban mota ita kuma ta shiga baya. Suna kama hanya ta zaro wayarta ta lalubo lambar Anti Wiyya ta tura mata sako ta wahtsapp tana sanar da ita an saki Khadeeja. Bayan sun gama hirarrakinsu na murna da nuna jin dadi Anti Wiyya ta turo mata sako kamar haka “Kije kiyi ta addu’a Allah ya sa kada kuna dawowa ya dawo da ita. Nan ma in sha Allah akwai wani malami da zan kaiwa abin sadaka yayi miki aikin da ba zata taba dawowa gidan ba, kin ga ki ci gida se yanda kika yi.”
Ta turo mata emoji na dariya ta rufe wayar, ta mayar da hankalinta kan hanya zuciyarta fes cike da fatan Allah ya sa kada ya dawo da Khadeeja tunda ya ce saki daya ne; in ya so sai ta ji da yaran kawai.
………
A hankali Khadeeja ta baje kayanta a gida; ta sanar da Baffa ko da ya dawo ma ba zata koma ba domin ko ya mayar da aurenta to kotu zata kaishi ya saketa. A haka dai aka bar maganar domin shi Baffa gani yake kamar idan aka bata lokaci ta huce zasu yiwa kansu sulhu ita da shi.
Tun Baffa yana sa rai zai ji kira daga wajen iyayen Mustapha sun biyo sawu har ya fitar da rai. Saura kwana biyu babbar sallah suna zaune a parlor shi da Mommy suna hira yace ‘Mutanen nan dai shiru, babu wanda ya biyo sawun Dije. Na san dai babu yanda za ayi suce basu san ya saketa ba tunda ai zasu ga ba ita ya barwa yaransa ko?’
‘Uhm, ni abun har ya isheni ma wallahi. To amma ko tuntubarsu zaka yi ka ji, tunda ai ba zamu taru mu zama daya ba ko?’ Mommy ta bashi amsa.
Yayi ‘yar dariya yace ‘Babu wanda zan tuntuba tunda ai da zan basu aurenta ba ni na tuntubesu ba su suka zo har gida suka tuntubeni. Idan na tuntubesu hakuri zan basu ko me? Ni aka yiwa wulakanci aka saki ‘yata ko ma don wanne dalili ne amma kuma ni ake jira nayin magana? To su cigaba da zamansu kada ma su zo inda nake.’
A haka suka bar zance domin Mommy ta san in dai Baffa ne yanda ya kafe ba zai yi magana ba to tabbas ba zai yin ba.
PAGE 215
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suma daga can gidansu Mustapha a tunaninsu Baffan Khadeeja ne ya kamata ya nemesu don ya kamata idan ta je gida a bincika a ji, sai dai har aka shiga hidimar bikin sallah babu wanda ya neme su. Sai suka bar maganar kawai suna jiran Mustaphan ya dawo su ji ko shi yayi magana da iyayen nata.
...........
Suna daga cikin na farko-farkon dawowa a alhazai. Tun kafin su baro masaukinsu ta gama magana da shi a kan ba za adauko yara ba sai tayi kwana biyar tana hutawa, don Rukayya ma tace kada a dawo da ita sai bayan sati biyu. Abokinsa ne ya daukosu daga airport ya kaisu har gida, da yake ya saka Habib ya bude gidan an gyara tsaf suka sami ko ina.
Da safe suka sauka don haka kafin su shiga gidan sai da suka yi order din abincin rana. Sai can da yamma bayan sun gama hutawa sannan ya shirya ya wuce gidan Hajia. Nan ya zauna