end zan soya musu in sha Allah.’
‘To ai da kin bari sai weekend din ma ci gaba daya, yanzu idan sun dawo ai zasu ga bawon ba dadi ai kuma ma Shukra zata gaya musu tunda ita taci. Mai aikin ma kuma za a dauka.’
'Uhm.'
Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba.
Gaba daya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba zata bawa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta.
Ya gama cin abincin ya fice ya barsu ita da Shukra.
Sai wajen 10am ya kirawota a waya, bayan ta dauka yace ‘Mantawa nayi ban gaya miki ba idan 1pm tayi sai ki je ki dauko yara daga school.’
Ta dan yi shiru don ta zata shi zai daukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a kasa?’
'No, kin san school din ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’
'Ok.'
Suna gama wayar ta mike ta dora abincin rana don ta gama da wuri. Lokaci yana yi ta dauki Shukra suka tafi suka dauko yan makarantar. Suna dawowa bayan sun huta ta shiryasu suka tafi islamiyya.
Dab da magriba ya dawo. Bayan ya huta yana zaune a parlor shi da yaran tana jiyoshi yana tambayar Afaf abinda aka yi da baya nan, an dauko su da wuri daga school? Sun ci abincin rana? Me suka ci? Sun makara a islamiyya? Haka dai ya cigaba da tambayoyinsa tana kitchen tana jiyosu, kamar ta fito tayi magana sai kuma ta share ta cigaba da abinda takeyi.
PAGE 20
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
A haka suka karasa satin nan tana bakin kokarinta wajen kula da yaran nan gaba dayansu.
Ranar Juma'a suna gida da yake yara babu islamiyya; ranar ne kuma suke gyara gashin yaran mai kitso zata zo. Tun da wuri Afafa ta tsefe nata kan, ita kuma Shukra da yake tun suna makaranta Khadeejan ta tsefe mata babu wanda ya ji kansu. Tun da suka gama cin abincin rana take faman lallaba Nasreen ta bari a tsefe mata amma har aka kusa kiran la'asar guda biyu suka tsefe. Bata son a taba gashinta kwata-kwata don haka taki ma zama a tsefe.
Khadeeja ta kamo hannunta tace ‘Zo kin ji Nas, kin ga fa Shukra zata fi ki kwalliya tunda ta tsaya an gyara mata nata.’
Ta zauna, har an fara tsifar ta zame kanta ta matsa tana zumbura baki. Afaf tace ‘Anti wallahi idan baki zare mata ido ba haka za kiyi ta fama da ita, sai ayi sati ana tsefe kanta a gidan Mama.'
Ta cigaba da lallabata amma sam ta ki tsayawa; don haka ta kama hannunta ta zaunar da ita tana cewa ‘Idan kika sake tashi sai na zaneki Nasreen, ko na sa almakashi na aske gashin kan ya koma kamar na Yaya Habib.' Ta dubi Afaf tace ‘Yaya Afaf dauko min slippers mai zafi idan bata tsaya an tsefe ba zaneta zan yi.’
Da sauri Afaf ta dauki slippers ta zo ta ajiye a gaba Nasreeen wadda ta fara shesshekar kuka tana fizge-fizge. Khadeeja ta dan rike gashin tace zan dake ki fa Nasreen, ki rufe min baki bana son jin kukanki.’
Nan da nan ta hadiye kukanta tana shessheka aka cigaba da tsifa Shukra tana mata dariya.
……….
Daga masallacin Juma'a ya wuce gida don ya gaida Hajia, da ya gaisheta sai ya wuce gida don Khadeeja tace idan ya dawo zai kaisu saloon ita da yara a wanke musu kai da yamma kuma akwai mai kitso a makota dama ita take musu.
Yana shiga gidan ya sami Yaya Jidda da yaranta biyu ‘yan mata Naja da Farida, bayan sun gaisa gaba daya Yaya Jidda ta dubeshi tace ‘Gidanka fa zamu tafi yanzu ni da yara, Hajia tace muje mu dubo su Afaf.'
Yace ‘To ai sai ku tsaya mu tafi, don nima gaisawa kawai zamu yi na wuce.’
Kafin minti goma sun gama, suka shiga mota ya ja su suka kama hanya, suna tafe suna hira.
'To ya yaran? Ana kula da su dai ko?’
PAGE 21
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta tambayeshi.
'Ah Alhamdulillah, gaskiya tana kokari.’ Ya fada cike da fara'a.
'To ai haka ake so, Allah ya sa ta dore.’
Tun a bakin gate yayi honk, gaba daya yaran suka fito banda Nasreen. Habib ya tayashi bude gate, bayan ya shigo da motar gaba dayansu suka yi masa sannu da zuwa.
A nan suka fara gaida Yaya Jidda, bayan ta amsa tace ‘Ina Nasreena?’
Afaf tace ‘Tana ciki tsifa Anti Khadeeja take mata.’
Suka wuce gaba daya suka shiga gidan; kafin Khadeeja ta amsa sallamarsu Nasreen ta fizge kanta wanda saura daya a gama tsefeshi ta tashi tana share hawaye tace ‘Abbaaa.’ ta fada tana zumbura baki.
Da sauri ya rungumeta ‘Ya haka na ganki wujiga-wujiga? Wa ya taba ki?’
Shukra ta tintsire ta dariya ta daga slippers din da aka ajiye tace ‘Kukan tsifa take Abba shine Anti zata zaneta da slippers, kaga nawa Anti yalash din ko kuka ban yi ba har aka tsefe yanzu za mu je saloon smma banda ita. Anti tace tunda bata so a taba kanta askeshi zata yi kamar na Yaya Habib.'
'Sannu da zuwa Yaya.’ Khadija ta fada tana karkade jikinta.
'Yauwa.' ta amsa ba yabo babu fallasa.
Ta kare musu kallo tana kokarin zama tana cewa ‘To yanzu Kuma tsifar ce sai an yi zaniya ni ‘ya su?’
Kafin Khadeeja tace wani abu Afaf tac