, sai na ajiyeku gidan Hajia. In ya so ko gobe sai ku dawo da Yaya Jidda ku debi kaya. Antin ta tafi.’
Ya fice batare da ya sauraresu ba Naja ta rufa masa baya.
Nasreen ta kalli Habibi ta kare gefeb bakinta kamar me rada tace ‘Ya saketa.’
Ya zaro ido zai yi magana suka jiyo muryar babansu daga kafar bene yana cewa ‘Maza fa ku sauko.’
Suka mike gaba daya suka shirya suka fice.
PAGE 211
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ba karamin mamaki Hajia da Alhaji suka yi ba da Mustapha ya gaya musu ya saki Khadeeja.
Shi kadai ya shiga da yaran don ita Naja ma cewa yayi ta zauna a mota saboda kada ta bata musu lokaci. Suna shiga yaran suka wuce cikin gida shi da Hajia da Alhaji suka tsaya a parlor yana musu bayanin abinda ya faru.
Alhaji yace ‘To kai wane irin rashin hankali ne wannan? Ai don mace tace a saketa ba a sakin nata. Zuciya ce ta kwasheta kuma sai daga baya zata zo tana nadama. Da ka sani ka barta da aurenta idan ma tafiyar zata yi ta tafi idan ka dawo kalau zaka ga ta dawo.’
A fusace yace ‘Alhaji yarinyar ce ta kureni, ita kullum sai dai ay mata yanda take so amma ita ba zata yi yanda ake so ba? Taje idan mutuwar aure dadi ne ai ta samu sai ta dana ta fi shiga hankalinta.’
Hajiya tace ‘Ai shikenan tunda haka ta zaba. To yanzu in Hammad din da Rukayya? Ban gansu tare da ‘yan uwansu ba.’
‘Shi Hammad dama yana gidansu, ita kuma Rukayya gidansu ta kaita.’
‘Ai shikenan, Allah ya sauwake. Idan ka dawo a san yanda za ayi domin dai aure bai kamata ya mutu saboda kujerar hajji ba.’ Alhaji ya fada cike da nadama.
Mustapha ya dubi Hajia yace ‘Mukullin gida yana hannun Habib in an jima Baba Sani abokina zai zo ya kaisu shi da Afaf su debo kayansu su rufo gidan. Idan sun dawo sai ya bawa Alhaji mukullin gidan ya ajiye min. akwai ATM card din a hannun Afaf idan ana bukatar wani abu na kudi sai taje ta ciro ta bayar.’
Yayi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da damuwa.
……….
Zuciyarta fayau ta fito daga gidan tana addu’ar Allah ya sa iyakar zamanta kenan da Mustapha tunda ta san saki daya yayi mata. Sun tsaye a bakin titi ita da Hafsa suna jiran mota ya zo ya wucesu a guje a tashi motar. Ta bi bayan motar da kallo tana murmushi; ta tuna lokutan da yake zuwa ya wuceta a titi zata tafi makaranta amma ba zai iya rage mata hanya ba. Tayi murmushi ta kawar da kai. Jimawa kadan da wucewarsu ta sami mota, suka hau suka nufi gidan Mommy.
Tana tura gate din gidan Baffa ne a tsaye yake rufe motarsa, da alama dawowarsa kenan.
PAGE 212
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suna hada ido dashi hawayen da ta kasa fitarwa ya kwace, ta saki akwatin da take ja. Ahmad wanda yake tsaye a kusa da shi ya karasa ya rike akwatin yayinda ita kuma ta karasa ta fada jikin Baffa wanda yake binta da kallon mamaki. Ya rungumeta sannan ya dafa kanta wanda ta kwantar a kirjinsa yana cewa ‘Subhanallahi! Me ya faru da ku Khadeeja?’
Ta kasa magana sai kuka kawai take har da shessheka.
Baffa ya fara shafa bayanta yana cewa ‘Ya isa haka, ya isa, ki gaya min me ya faru?’
‘Ya sakeni.’ Ta fada a cikin shesshekar kuka kamar mai rada.
Take fuskar Baffa ta canza, ranshi yayi matukar baci. Yace ‘Mustaphan ya sake ki?’
Ta daga masa kai.
Ya sake shafa kanta cikin yanayi na lallashi yana cewa ‘To shikenan, ya isa haka.’
Ya ja hannunta suka shige gidan; da yake Mommy tana dakinsa kai tsaye can ya wuce da Khadeeja. Mommy tana kokarin yi masa sannu da zuwa ta kula da Khadeeja, tace ‘A’a, Baffa a ina ka samo wannan?’
Ya zaunar da ita a gefen gadonsa yace ‘Mustapha ya saketa.’
‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Saki kuma? A yau din? Na dauka ce min kika yi yau jirginsu zai tashi?’
Ta share ragowar hawayenta ta ajiye jakar hannunta sannan tace ‘Eh, kafin su tafi airport din ne ya sakeni saki daya.’
‘Lallai Mustapha, to me kika yi masa ya sake ki? Ko kuwa dai tsabar wulakanci ne yaga gara ya sakeki kafin ya wuce yayi ibada?’ Mommy ta tambaya tana daga tsaye.
Bata yi tunanin wata amsa da zata bayar idan an yi mata wannan tambayar ba, amma dai tana jin gara ta fadi gaskiya don ma kada ya zo shi ya bada amsa da ta bambanta da tata. Ta daga fuskarta suka hada ido da Mommy sannan ta sunkuyar da kai. Mury kasa-kasa tace ‘Ni nace ya sakeni.’
Saura kadan wayar da take hannun Mommy ta kufce ta fadi, ta rike wayar sannan tace ‘Kika ce ya sake ki Khadeeja? Saboda rashin hankali ko saboda me?’
Baffa da yake tsaye a gaban wardrobe dinsa yana rataye babbar rigarsa ya zagayo ya zauna a kusa da ita yana kallonta yace ‘Dije me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
PAGE 213
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kafin ta yi magana Mommy tace ‘Saboda wulakanci mana, ko kuma saboda yace ba zai je da ita aikin Hajji ba sai ya je da amaryarsa.’
Kallonta kawai Baffa yayi ta yi shiru, ta gyara tsayuwarta tana binsu da kal