NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 88 of 105

daga ita ba zan sake ba. Gidanmu zan tafi Mustapha saboda na gaji da aurenka, kuma na gama aurenka daga yau. Zaka iya sakina yanzu ko kuma duk lokacin da ka sami natsuwa ka rubuta min takardar sakin ka aiko gida; amma ba zan sake zama a matsayin matarka ba.’ Gaba daya yawun bakinsa kafewa yayi saboda bai taba zaton Khadeeja zata iya fada masa haka ba, ya saketa! Kuma a wannan lokacin; ya kalleta ya sunkuyar da kai, jimawa kadan ya sake kallonta sannan yace ‘Saboda kujerar Makka kike so ki kashe aurenki Khadeeja? Kujerar da na gaya miki next year dake za a tafi. Tukunna ma kin san hukuncin matar da ta nemi saki a wajen maigidanta ba tare da wani dalili ba?’ Ta jijjiga kai tana murmushi a daidai lokacin da kwalla ta fado daga idonta, ta share kwallar sannan tace ‘Ko daya, kujerarka ba ta kai ta daga min hankali ba tunda dai kasar Makka ta Alla ce ba taka ba. Alhamdulillahi ma kace wadda ta nemi saki ba tare da dalili ba; don ni ina da dalili kuma Allan da ya halicceni ya fi ni sanin dalilin. Amma tabbas yau zan bar gidanka da aurenka Mustapha.’ Ya ja baya ya sake kare mata kallo, yace ‘Kin san me kike fada kuwa Khadeeja? Please idan wasa kike ki bari kada ki saka muyi missing flight.’ PAGE 209 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tayi yar dariya yayinda ta ware hijabinta ta saka tana cewa ‘Ba wasa nake ba, amma dai kana da zabi. Ka sakeni yanzu ko kuma ka tafi idan ka dawo ka rubuta min takardar ka aiko min gida.’ Ta kwayeshi ta bude dauko jakarta daga kan gadon ta nufi gaban mudubi. Yana tsaye mamaki ya hanashi magana. Yana daga kai idonsa ya sauka a kan agogon bangon yake kafe a saman dakin; 12:52pm agogon ya nuna; shi da aka cewa su zama suna cikin airport kafin azahar. ‘Mteww!’ ya ja dan gajeran tsaki sannan ya fesar da iska daga bakinsa. ‘Khadeeja yanzu ya kike so nayi da yaran bayan mun gama magana dake? Kuma me nayi miki da har zaki rike a matsayin hujjar da ta saka zaki ce na sake ki?’ ‘Yara kam ai yanzu ba matsalata bane, duk yanda kayi da su daidai ne. Ni dai zan tafi, yanzu in sah Allah.’ Ta sauke akwatinta ta fara ja tana nufin koafr dakin. Ya bi bayanta da kallo; to me yayi mata da har zata ce ya saketa a wannan lokacin? Anya kuwa ta san menene zawarci? Kawai saboda bakin cikin ba da ita zai fara tafiya aikin Hajji ba? Ko ma me take nufi ya kamata ya cika mata burinta, watakila kafin ya dawo ta dawo hayyacinta kuma ta gane mahimmancin aure a rayuwarta. In ya so idan ya dawo da ita sai ta hakura ta zauna tunda dai shi bai ga wani abu da yayi mata ba. Tana daf da karasawa bakin kofar yace ‘Khadeeja.’ Ta juyo ta dan tsaya ‘Ki je na sakeki saki daya.’ Ta yi sauri ta juya fuskarta saboda kaucewa hada ido da shi; duk da ita nema kuma da yakinin zai aikata haka amma sai da fitar kalmar tayi mata ciwo. Ta sake juyowa cikin murya kasa-kasa tace ‘Nagode.’ ‘Zaki yi nadamar rabuwa da ni Khadeeja.’ Ya fada a gajarce. Ta kalleshi tayi murmushi sannan ta kawar da kanta ta faki idonsa ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta. Bugun kofa ne ya klatsesu da Shukra tana cewa ‘Abba Anti tace zaku makara fa.’ ‘Um, gani nan zuwa.’ Ya amsa daga cikin dakin. Ya wuce Khadeejan ya bude kofar ya fice. Ta bi bayansa janye da akwatinta. Shukra ta tsaya a gefenta tace ‘Anti kema harda ke za a tafi?’ Ta kama hannunta tace ‘A’a ni gidanmu zan tafi ba da ni za a tafi ba.’ PAGE 210 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Gidan Mommy? To damu zaki tafi?’ ta tambaya da mamaki. ‘Eh, gidan Mommy zan tafi amma ba daku zan tafi ba. Abbanku zai gaya muku wadda zata zauna da ku.’ Gaba daya yaran suka zuba mata ido suna kokarin gani me take fada. Ta kwalawa Hafsa kira ta bata umarni ta hada kayanta su tafi gida. Ba tare da bata lokaci ba ta juya. Ta dubi Naja wadda take zaune tana binsu da kallon mamaki tace ‘Maman Rukayya sai kun dawo, Alah ya amsa ibada Alah ya maimaita mana.’ ‘Amin.’ Ta amsa a gajarce sannan ta dubi Mustapha tace ‘Ban fa gane ba, me yake faruwa ne?’ Kafin ya bata amsa tuni Khadeeja ta ja akwatinta ta fice daga parlor din. Shukra wadda ta karasa ta fada jikin Abbanta ta rushe da kuka; saboda ta kasa fahimtar me yake faruwa su da aka ce za ayi tafiya har Abbansu a barsu da Anti kuma Antin ta fara tafiya. Ya dubi naja yace ‘Cewa tayi na saketa kuma na saketa, tunda ita ta nema.’ Ta dan firgita ta dafe kirji, bata san lokacin da yawun da yake bakinta ya wuce ba tace ‘Saboda me? Kai kuma ka biye mata?’ ‘Saboda bakin cikin zan tafi dake Hajji ban tafi da ita ba.’ Ya fada cike da adcin rai. Ya karasa ya zauna a kan kujera a jigace kamar wanda aka tura. Sukayi cirko cirko suna kallonshi. Habib ya shigo a guje ko sallama bai yi ba, yana cewa ‘Abba na ga Anti tafi. Me yake faruwa ne? waye zai zauna damu?’ Ya mike a jigace yana cewa ‘Maza kowa ya debo kaya ko kala daya ne mu wuce
🏠