igaba.
--------
Tun kafin ta yaye Hammad al’adarta ta dawo, don haka kai tsaye ta tafi asibiti ta karbo kwayoyin family planning; ko Mustaphan ma bata gayawa ba sai da ta karbo. Ba wai haihuwar ce bata so ba, kwai dai bata da tabbas din zaman auren. Kullum Mustapha nuna mata yake itace jakar gida yayinda Naja itace matar gida; don haka duk da yana kula da yaransa sosai kuma yana son su amma bata jin zata iya tara masa wasu yaran balle ma azo inda zata yi magana a ce tayi hakuri ta zauna don yaranta.
Tunda ta karbi kwayar nan bata taba yin fashi ba kamar yanda likita ya sanar da ita, ko da kuwa ba itace da kwana ba haka take shan kwayarta. Amma a ‘yan kwanakin nan gaba daya ta rasa gane kan jikinnata; wasu abubuwa take ji kamar na mai laulayi.
A hanyarta ta dawowa daga office ta tsaya a chemist ta siyo pregnacy test strip, har ta zo gida tana fargaba saboda duk wasu alamu na ciki sun gama bayyana a tare da ita. Sai da ta bari tayi baccin dare sannan ta dauki fitsarinta na sassafe ta gwada da shi; kafin sakamakon ya bayyana a jikin ‘yar takardar gaba daya ta gama rudewa. Ko da taga layukan guda biyu sun bayyana batare da wata matsala ba sai da zuciyarta ta kusan bugawa, ta muttsike ido ta sake kalla amma har yanzu layukan suna nan guda biyu. Haka ta hakura ta mike ta dauro alwala sannan ta fito daga bandakin ta tayar da sallar asuba.
Bayan ta idar da sallar ta zauna a kan daddumar ta yi shiru; ta daga hannu zata yi addu’a amma ta rasa ta inda zata soma. Gaba daya ma bata san me take ji ba. ‘Alhamdulillah.’ Ta fada a fili kamar me yin rada.
PAGE 197
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka ta karasa azkar dinta sannan ta mike ta shiga hidimarta.
Dole ta hakura ta daina shan kwayar family planning din da take sha saboda kada taje ta cutar da abinda yake cikinta.
Sai bayan kwana biyu ta dan sami natsuwa sannan taje asibiti aka sake yi mata gwajin, aka tabbatar mata tana dauke da ciki na sati shida. Bayan ta dawo daga asibitin sannan ta sanar da Mustaphan.
Wannan gwajin da ta yi kuma sai ya zama kamar ta kunno laulayin gaba daya. Babu inda yake mata ciwo amma tana fama da kasala sosai sannan kuma ga rashin son cin abinci. Haka dai ta cigaba da lallabawa.
…………
Ranar kwananta ne don haka Mustapha a dakinta zai kwana. Yaran duk sun kwanta a dakinsu yayinda Hammad da Shukra suke kwance a dakin bakinta wajen Hafsa.
Yana zaune a gaban mudubinta yana aiki a computer dinsa yayinda ita kuma take kwance a kan gado tana game a waya. Ya bar aikin ya juyo yana kallonta ya kirawo sunanta, ta bar gane din ta mayar da hankalinta kanshi sannan ta amsa.
Yace ‘Umm! Ina so dama na sanar dake bana zamu je aikin Hajji da Naja. Da dake zamu je amma kin ga ke laulayi ya saka ki a gaba don haka na cire sunanki na saka nata sunan.’
Ta dan yi shiru saboda yanda maganar ta zo mata a ba-zata; idan dai ba wai bata ga dai-dai ba ma kamar dai ganin da ta yiwa Najan shekaran jiya ta ga kamar itama tana dauke da yaron ciki; ko da bai fito ba dai amma ita Khadeejan taga wasu alamu. Domin a lokacin har ta ji kunya tana fatan Allah ya sa ba ganewa Najan tayi ita tana dauke da ciki ba taje itama tayi. Kallon da ya kafeta da shi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta tana cewa ‘Ma sha Allahu, Allah ya nuna mana. Amma ai ana zuwa da masu ciki kuma zan iya; in dai an yi niyyar kaini to a bani kujerata zan je.’
Yayi dariya ‘Haba aikin hajin fa ba wasa bane kuma ba akwabce ake yi ba, ko so kike muje wahala ta sa ki sami miscarriage? Kuma ya za ayi na daukeku mu tafi saudiyya gaba dayanmu? Mu bar yaran a wajen wa? Kin san Hajia yanzu ba lafiya ce da ita ba.’
‘Hakane, to ai sai Najan ta zauna ni naje tunda ni ka fara yin niyyar biyawa.’
PAGE 198
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘To ai na gaya miki ke ga ciki, da ace baki sami ciki yanzun ba dake zamu je amma ki yi hakuri sai shekara mai zuwa in Allah ya nuna mana.’
Ta tashi zauna ta kara marairaicewa tace ‘Idan na mutu a haihuwa fa?’
Ya harareta yace ‘Ka fadi alkhairi ko kayi shuru.’
Ta sunkuyar da kai tana murmushin yake; yayinda ya juya ya cigaba da aikinsa.
Ta zame ta koma ta kwanta; tabbas ba kuskure tayi ba ciki ne da Naja, ko da kuwa bai kai sati shida ba. Kuma tabbas ta san ba ita Mustapha yayi niyyar biyawa Hajji ba, Najan ya so biyawa. Kawai dai cikin ya zo masa ne a matsayin uzuri da kariya. Ya wanke kansa daga zargi. A hankali ta zame ta gyara kwanciyarta ta janyo abun rufa ta rufe jikinta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci; haka ta kwana zuciyarta tana kuna.
Me Mustapha ya mayar da ita ne; shikenan idan dai abun karuwa ne ba zai iya sakata a ciki ba sai bayan ya saka Naja amma idan dai wahala ce itace a kan gaba? Yanzu yana nufin yace da matarsa zai tafi aikin Hajji; wadda itama cikin ne da ita sannan ita kuma ya barta ta kular masa da yara da gida duk da itama cikin ne da ita. Zata iya wahalar kula da gida amma ba zata i